Skip to content
Part 47 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Hidima ta ban mamaki Ado ya yiwa Sa’adatu, a lokacin auren nata irin hidimar da ko auren su Umamatu ya tashi yi in yayi haka ya ci a yaba mishi.

Magana guda daya da ya gayawa Sa’adatu a ranar da za’a kaita gidan mijin nata kuma ita ce dai ta gamsar da ita tayi amfani da ita aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake nema bai taba kawo karanta wurin Adon ba balle maganar ta wuce ta kai ga Gambormnu.

Maganar kuwa ita ce hukunci na zartar miki Sa’a, irin wanda uba ne kadai ke da ikon yiwa ‘yarshi hakan in har anyi mata tarbiyar da ta dace da ita duk kuwa da ni din ba mahaifinki ba ne, na kuma san hakan sai dai nasan ke din yarinya ce da aka yi wa tarbiyar sanin darajar na gaba. Na kuwa san ina da girma da mutunci a wurinki sai nake ganin kamar ba zan yi iko dake kiyi sanadin da zan tozarta wurin mutumin da nake da kima a wurinshi ba, don haka in kin ji ku zauna lafiya.

Shekaru biyu kenan da yin auren Sa’a ta haifi danta Adam, har sun yi aikin Haji ita da Gambo tare ya biya musu suka tafi babu wanda ya taba jin wata magana surukuta mai dadi suke yi shi da Ado.

Ire-iren irin wadannan al’amuran sune suke kara sanya ni hakuri da kokarin danne zuciyata a kan al amura masu yawa ina kawar da ido akansu.

Amma duk da haka wani abin kure hakuri ake yi, saboda a hali irin nawa halin da kullum Gambo ke yi min kirarin rashin hakuri a kan shi sai in rinka ganin bai dace in yi hakuri da dole in kuma yi da abinda bai zame min dole ba.

Dawowan Mama gidan Ado yayi dalilin da itama Suwaiba ta dawo gidan da zama don ta ce ba za ta iya zaman gidan ubanmu ba, in kuma da mutumin da ke taimakon Mama kina a zahiri to Suwaiba ce.

Kan ya’ yana a hade yake, don ko da sun yi wayon sanin iyayensu tun kan mu taso to a zaman da ake yi dai kansu a hade yake, don ba a bambanta su da komai ba, komai tare ake musu, suma duk abin da zasu yi tare suke yi ba su da wata matsala ko wata damuwa.

Amma zuwan Suwaiba sai ta tasa min su a gaba da iya shege iri-iri, dan kankanin abu ne na yara zasu yi sai ta ce uhun, wai su masu gida ko? Saboda ita gidan ubanta ne yasa take yi muku haka, ta bugi Umamatu ko Mama ta buge ta bai taba damuna ba, don nasan duk tsiyarsu ba za su gana mata %50 din abin da suka gana min ba.

Don haka ko a jikina saboda na riga nayi ilimin sanin cewar zaluntar yaro bai cutar dashi da komai sai dai ma ya zamo mishi wani alheri a rayuwarshi ta gaba.

To amma neman da take yi na ta rinka ‘shiga tsakanin Umamatu da dan uwanta tana batawa shi ne abin da naji ba zan lamunta ba, tunda abin da ke faruwa a tsakaninsu din hali ne kawai na kuruciya.

Suna mata tana musu kamar yadda take yi tsakaninta da kannenta da ni ce na haife su, gara wadancan ma duk sun fi karfinta in dambe za’ayi dukanta zasu yi.

A duk lokacin da maganarsu tazo gabana kuma na kan yi hukunci ne bisa cewar ta basu hakuri don ita ce karama duk da mafi girman da aka yi mata na kwana bakwai ne.

Ba kuma don komai nake yi hakan ba sai don in hada kansu su zama abu daya, su sani su kuma yarda da cewar yancin da ita take dashi a gidan bai wuce wanda suke da shi ba.

Don haka rannan da na sake jin Suwaiba tana shiga maganar su tana cewa ai tunda kuka zo zaman maula a gidan ubanta sai kuyi tayin hakuri da ita sai na gangara daga inda nake.

Naje na shiga wurin nasu Suwaiba tana ciki na tambayi yaran abin da ya faru suka mayar min na kalli, Suwaiba na ce mata a wannan bayanin ne ki ke, fadin wannan maganar wa wadaanan yan yaran ya’yan cikinki?

Sau nawa ki ka haifi wadannan? To bana so kar in sake ganin ki a wurinsu bana son ganin kina shiga min harkar yara, ta ce har da taki ma na daina, na ce to da yafi miki daidai.

Tun daga ranar ta daina gaishe ni, in na gaishe tan ma ta amsa a lalace, in za ta fita ko kallona bata yi, ba ta min sallama, ta dawo kuma a lokacin data ga dama.

Naga zata zubarwa mijina da mutuncin da ake ganinshi da shi tunda ba wani shiga na mutunci take yi ba shi kuma ba mazaunin gida bane balle yasan abinda take yi.

Don haka nayi mata magana kan ta daina yawan fita, ina take zuwa tunda ni da ita ai ba wasu dangi muke da su a Dabai ba, balle ta ce min wurin ‘yan’uwanmu take Zuwa.

Sai kawai ta fara min maganganun da na kalle su a matsayin rashin kunya, gudun bacin rai sai yasa Ado yazo gida daga Abuja, sai na ce mishi ga abinda ake ciki don ya sani.

Sai kawai ya ce min kai Humaira, kananan maganganu irin wadannam rinka hutar dani kawai ki daina gaya min su ko dai kiyi maganin abin kawai da kanki ko kuma hanya mafi sauki shi ne ki gayawa Mama.

Nasan zata tsawatar, na ce mishi to duk da ba dadin hakan naji ba.

Rannan sai wani abu ya sake hada ni da Suwaiba, naje na samu Mama ina gaya mata, sai kawai ga Suwaiba tana biye da ni tana magana har tana tafa hannu, ni fa sai dai in za ki mutu ki mutu in za ki yi rai kiyi rai.

Don duk tsiyarki ba zan bar gidan ba ba wurinki na zo ba, ba kuma don ke nake zaune ba, kin ce in daina kula ‘yarki na hada na ce har kema ba na kulaki, bana shiga harkarki, ba na shiga harkar  ‘ya’yanki dukkansu wurin Mama nazo gida kuma gidan Kawu na ne.

Na kalli Mama, wacce tayi shirù tana Kallon tsiwar da Suwaiba take yi min, na ce Mama kina jin ta? Sai kawai naji taja min tsaki ta ce min ke tafi can ni ki bani wuri da fitinarki ta tsiya, ke yanzu ai na riga na gane ki gaba daya burinki bai wuce kiyi min abin da hawän jinina zai tashi ba ya karasa ni in mutu, in yaso burin uwarki ya cika a kaina.

Na kalli Mama nayi murmushi na ce Innata ai bata da sauran buri akan ki Mama, tunda gidan da kike yi mata gadara a kanshi kina fadin naki ne ya zama nata, mijin da ki ka kwace mata gashi can kin baro mata shi saboda ya gagare ki. Nan kuma da aka dawo aka zauna nawa ne, tunda mai kishiyoyi da ‘ya’yan miji ma takan nishadi in ta samu wuri ta ce gida da mijin nata ne ita kadai balle ni da ni kadai din ce.

Mama ta kama kuka, Suwaiba kuma ta kama maganganu ba dai ita kadai ce a gidan ba wooo! Na ce ai ita bata dame ta ba, ba kin san gidan ba? Ai kin san bata kishi da ita.

Ai Gambo bata da sauran kishiya, dama Mama ce matsalarta, tun kuma daga ranar da tayi kuskuren kin jin kashedin da masoyanta suka rinka yi mata, ta dauki Ado ta danka min shi a hannuna da nufin zaluntar uwata, nayi wuf na kama shi na dunkule shi wuri daya na dankawa  Gambota shi bata sake zamowa matsalarta ba.

Na wuce su nayi tafiyata cikin zuciyata ina fadin Mama dai kam yau na zage ta duk abinda Ado zai yi kuma sai yayi kawai mu gani.

Ban dade da fitowa daga dakin nasu ba sai ga Suwaiban tazo ta wuce ni ta fita nayi waya na ce wa maigadi ya kulle gidan kar wanda ya sake shigowa kowane ne sai an gaya min, ya ce min to.

Sai da aka yi sallar magariba Suwaiba ta dawo Maigadi ya ki bude mata kofa tayi juyin duniya ya ki, Mama ta turo keken ta na guragu don bata riga tayi karfi ba tukuna, tazo ta same shi ka bude mata na ce.

Cikin tsawa take ba shi umarnin, ya ce Goggo ce ta ce kar a bude, tayi-tayi abin ya gagara sai ga ta a kofar dakina na ce kisa a bude wa Suwaiba gida ko?

Cikin tsawa tayi maganar na ce to, ba ta kuma zaci to din zance ba na kalli Hindu na ce mata jeki ki ce wa Solori ya bude mata kofar, tana gaya mishi ya bude, Suwaiban ta shigo.

Muna nan a haka Suwaiba bata sake fita ba don tasan taná fita zan sa a kulle har Ado ya dawo, shigowar dare yayi na kuma riga na shiryawa zuwan nashi, don sabuwar kaza ce a jikina.

Kwanaki uku kuma kenan tunda naci ta riga ta jika a kidime kwarai ranar ya kwana, Humaira, na ce mishi naam ya kara matsowa jikina ya kankame, kina da wani sirri a tare da ke Humairah da wani lokaci kike kidimar  da ni, ki rinka sanya ni ina jin tanfar dai ke din budurwa ce. Shiru nayi ban tanka mishi ba.

Washegari da safe sai da na shirya mishi abin karyawan shi ya gama komai ya yi wanka ya kintsa, aiken Mama biyu ta waya wai tana son ganinshi, amma bai samu fita daga dakin nawa ba sai gab da azahar.

Don haka sai da yaje yayi Sallah ya dawo sannan ya shiga wurin nata, ya dan dade kafin yayi waya wai in je.

A dakin na same su ranshi a bace kwarai da alamar ya ji maganganu iri-iri, amma duk da haka ya kalle ni saboda kwalliyar da nayin yasan táshi ce.

Me ke  faruwa ne Hurmaira? Cikin natsuwa na ce mishi kamar me? Ya ce ina nufin me ya hada ki da Mama? Nayi maza na ce babu komai.

Mama tayi maza ta ce ba ki zagen ba za ki ce mishi babu komai? Suwaiba ta ce wai ita ga mu… Ado ya yi maza ya katse ta in ki ka zage ta a gabana ranki zai baci, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi.

Ni babu abin da ya hada ni da Mama tunda ba abokiyar magana ta ba ce, uwata ce kai ne ka ce in wani abu ya faru tsakanina da Suwaiba in daina gaya maka, in kawo kara wurinta zata tsawatar mata.

Ya ce haka ne, na ce to karar na kawo sai Suwaiba tayi min rashin kunya a gabanta nayi mishi bayanin komai har kawo kan abin da ya faru duka, sai dai na ki yarda da cewar ni maganganu da Mama nake yi na ce da Suwaiba ne.

Ado yayi shiru na lokaci mai tsawo saboda ranshi ya baci kwarai, don kwa ko ban amsa da Mama nake yi ba ai shi ya ji abinda na fadan sai dai kuma nasan zai san ita Mama ita ta fara tsokanata.

Shiru yayi cikin matsanancin tunani, yayin da ni kuma nayi shiru cikin natsuwa ina sauraron abinda zai ce, sai Mama ta fara yi mishi bayani, ita Humairah bata gane ba ne ita so take duk wanda zai zauna a gidan nan sai ya yarda ta maida shi talolo kamar yadda ta maida wannan yaron.

Ado ya daga kai ya kalle ta ya ce wa Ibrahim? Tayi maza ta ce ebh, shi to ita kuma Suwaiba ba za ta yarda da hakan ba, don ita ba sakarya ba ce irin shi, ba wurinta tazo ba ba don ita tazo ba.

Tunda gidan nan ba nata ba ne ita da yan dakinsu da zata ce sai ita da su ne za su zauna a ciki, gida ai naka ne amma take bugun kirgin nata ne, ya yi maza ya katseta ba bugun kirjin bane nata ne kuma tunda suwaiba tace ba wurinta tazo ba.

Kema kin fada ba wurinta tazo ba, to ta bar mata gidanta kawai, azo a zauna a gida ace ba wurin matar gida aka zo ba wurina aka zo ni mazaunin gida ne?

Humairah ai bata adawa da ‘yan uwanta, Mama da ke take yi shi yasa da ta samu damar gaya miki magana ta gayaa miki, ba kuma zan kyale ta kan rashin kunyar da tayi miki ba.

Ai ta zauna da Ibrahim babu abinda bata yi mishi ba, ta kuma zauna da Kaltume da ya’yanta tsawon wata goma bata ji ko ganin wani abu mara dadi ba, saboda bata da matsala da ‘yan uwanta. Don haka Suwaiba suna da gidan uba ta koma can ta zauna.

Mama ta ce uhun, za ka kore mu dai kawai tunda kasan hakanne zai fi yi mata daidai, ai kaima kasan ba zan zauna a in da Suwaiba ba za ta zauna ba in dai ka ce ta tafi to tare zamu tafi.

Ya ce to shi kenan Mama, in kun ga hakan yafi miki sai ki bita ni dai nasan ban ce ke ba amma Suwaiba kam a gabana ta amsa ta ce ba wurin Humairah tazo ba, to in wurina ne ni bani da gida zaman nata ya isa haka ta tafi kawai.

A ranar Suwaiba ta tafi, ina jin Mama tana gaya mata inda zata, wai kar ta je gidanmu, ban san yan aka yi ba sai kuma gata ta gama bin dangi ta gaji ta koma gidan namu.

Ta bude dakin Maman ta shiga ta zauna ita kadai, Gambor tawa kuma ita ce dai mai daukar dawainiyartata.

Barin Suwaiba gida sai Ado ya dorawa diyar shi dawainiyar baiwa Mama magani da safe da yamma tunda da rana kam bata nan tana makaranta, sai ni in je in bata.

Tunda Ado ya dorawa Umamatu wannan dawainiyar ya hadata da aiki saboda kullum taje baiwa Mama magani tunda ba maganin ba ne kawai sai ta motsa mata jiki, to bata fitowa sai da kuka.

Tunda ba za ta gama ba sai ta jawo wata sanda da ta sunne a gefen gadon nata ta rafke ta dashi wai tayi mata mugunta.

Kullum tazo ta gaya min zan ce mata to kiyi hakuri Umamatu ai kin san bani na saki wannan aikin ba ko? Ta ce min eh.

Rannan ina dakin Ado da rana saboda yazo gida week end na kalli agogo na ce mishi bari in je in baiwa Mama magani lokaci ya yi, ya ce a’a babu inda za ki yanzu Umamatu taje ta bata na ce mishi to.

Sai ga Umamatu ta dawo tana kuka da iyakacin karfinta, sallama biyu tayi kafin Ado ya bani izinin amsawa da bata umarnin shiga inda muke din.

<< Mijin Ta Ce 46Mijin Ta Ce 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×