Cikin ikon Allah kafin kace kwabo Tafi da yaranta sun miƙe. Sana'a ba kama hannun yaro. Kuma sai komawarsu unguwar ya zo musu da tulin alheri. Mutane suka yi ta aiko da daka da surfe. Tun da suka fara alewar yara sai ya zamana gidan ba a raba shi da sallamar yara.
"Akwai mandula?"
"Akwai tsami gaye ko carbin malam?"
Muryoyin da za kai ta ji kenan. Ba a rufa wata ɗaya ba yaran suka koma makaranta, don ita
Aminatu ma sai aka saka ta a wata makarantar sakandire ta jeka-ka-dawo. Da Ibrahim da Usman su. . .