Skip to content
Part 10 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Kuka ba zai zama maganin komai ba,ina roqonki kar kiyi kuka,hakan idan ki kayi zanji da’di sa’banin hakan kuma zanji babu da’di saboda Sumayyah  tunanina gida zaki je kowa naki ne a gidanmu,idan wani akasi ya faru ba yadda muka so ba kina dani,zanyi miki abunda ko wanne Yaya yake yiwa kanwarsa Sumayyah  dan Allah kar kiyi kuka saboda hakan zai ‘batamin rai zanji ya sagarmin da gwiwa”Maganar Yaya Samir ita ta ratsamin zuciya na ‘dago na kallesa bayan yakai qarshen maganarsa.

“Yaya Samir ba kuka nake ba”nayi Maganar ina maida kaina qasa.

“Kina jin babu da’di ko,rabuwa da iyaye Sumayyah saidai bisa dole kema ki ‘dauki hakan tamkar dole,kuma ina fatan ki ‘dauki nawa iyayen kamar naki,banaso kiyi maraici ta dalili na,nima zanyi addu’ar Allah yasa baza’a samu matsala tare da nawa iyayenba, Sumayyah inasan zumunci,kuma inason yinshi da qarfina da ku’di na,kimin addu’a Allah yasa kar nida iyayena muci amanar zumuncinmu.”

Murmushi kawai nayi Jin Maganar da Yaya Samir yakeyi,da maganarsa tasa hankalina ya kwanta sosai harna daina jin zullumi sosai haka dai na daure na ce.

“Amma Yaya Samir zan kai yaushe kafin na dawo gida.”

Murmushi yayi da na gani kan fuskarsa ya ce

“Sai munyi aure tukunna zaki zo ki ga gida”ya qarasa zancen yana hararata

Duk da nasan wasa yakeyi sai da gabana ya yanke ya fa’di jin batun aure danni a qaddarata bana fatan Allah ya qaddaramin auren zumunci musamman yadda zumuncin ya ta ‘bar’bare,Maganar Yaya Samir ta katsemin tunanina.

“Ya kikayi shiru Qanwata wasa nake miki,ba zaki da’de ba zaki dawo,amma saikin saba da mu ‘yan uwanki,dan tun farkon zuwana na fahimci kamar tsoronmu kike ji,wanda baikamata ‘dan uwa ya ji tsoron ‘dan uwansaba,shiyasa nayi alqawarin zan ‘daukoki ki zauna tare damu,ken samu har sai zaki yi aure ki dawo,idan ma a katsinan ne da nafi kowa jin da’di” nidai shiru nayi dan gaba ‘daya bana fahimtar inda zancen Yaya Samir ya dosa barci ma naji inaji hakan yasa nayi shiru na fara gyangyadi,tsayawar motar yasani bu’de idona parking Yaya Samir yayi gefen titi dai dai Rufaida fura and yoghurt na rijiyar zaki fita yayi a motar ba tare da yace min komai ba,dan nafi tunanin yaji haushina ne,yayi magana ban basa amsa ba,bai jima da fita ba ya dawo ya miqomin ledar Rufaida yana cewa”ga wannan dan tafiya Katsina ba dai nisa ba nasan zakiji yunwa kafin mukai”
Godiya nayi masa, shima na shi da ya siyo ya sa bayan mota muka cigaba da tafiya da muke tafiyar ina tunanin makomata anan gaba ka’dan,kaina na mayar qasa ina tuno komai na rayuwata yau nice wai zanje inda ba muda wata daraja a idanunsu,gidan mutumin da saboda Mamanmu ya hana Abbanmu aiki a haka har zanyi tunanin akwai wata soyayyar da zan tarar a gidan wan mahaifina,zan jure komai nayi alqawari ba wai dan kowa ba sai dai Yaya Samir da a baya na ‘dauka ni ‘din babu wani Wanda zai so rayuwa da mu,a cikin dangin Abba ,amma sai ga Yaya Samir yana so na rayu har abada a tare da su,da ace dangin Abba kamar Yaya Samir suke da nasan babu abinda xamu rasa a rayuwarmu,dukda ba wanda yake azurtawa sai Allah amma dai nasan da abubuwa da dama sun ragu

Sai wajen qarfe hu’du da mintina muka qarasa Katsina dan Yaya Samir ba wai gudu yake a mota ba,kuma gashi Katsinan ma akwai tafiya babu laifi Katsinan ta burgeni sosai dukda ba wai takai inda na baro ba amma dai tana da abun birgewa itama

A Kofar gate ‘din wani gida upstairs Yaya Samir ya fara horn ‘din motarsa wanda ko ba’a fa’damin ba gidan Abban Katsina ne,cikin mintina qalilan aka hangame gate din gidan,ya kunna hancin motarsa cikin gidan maigadi yana ‘daga masa hannu da ce masa “sannu da zuwa”Gurin aje motoci ya qarasa ya parking ‘din motar ya fito,nima ba nida za’bi da ya wuce na fito gabana yana tsananta fa’duwa da addu’ar da na fara ta rage haka har na tsaya nabi gidan da kallo tabbas gidan yayi kyau sosai,dan zasuyi kyau ‘daya da gidan Aunty Asma’u daga fara kallonsa da nayi,a raina na cigaba da ayyana muna da masu ku’di haka duk a ‘yan uwan Abbanmu amma rayuwarmu take haka babu Wanda zai kalleni yace akwai dangina masu ku’di musamman idan kaga gidan dana fito Maganar Yaya Samir ta ktsemin tunanina
“Kizo mu karasa ciki,Malam Musa zai shigo da kayanki cikin gida”ya qarasa zancen yana fara tafiya nima ba nida za’bin da ya wuce bin bayansa da nayi Kofar falon muka qarasa knocking mukayi ta bu’de muka shiga da sallama babu kowa a falon sai qarar fanka da Ac kawai a falon tsayawa nayi kawai kaina a qasa dan banaso a lura da qauyancina shiyasa na maida kaina qasa
“Ki zauna mana bari na kira Ummi nasani tana ciki”Maganar da Yaya Samir yayi ya sani ‘dago kaina da kafin na zauna Yaya Samir har ya fara tafiya hakan ya sani zama a kujera mai ‘daya  ina ware idanuna akan komai dake cikin falon komai yayi dai dai da tsarin falon komai na falon brown ne harda labulaye,Maganar dana fara ji ya sani maida kallona ga inda nakejin maganar Yaya Samir ne sai Mamarsu da kallo ‘daya nayi mata na ganeta inda nake suka qaraso
“Maraba da Kanawa,ansha hanya”
Naji Maganar mamarsu Yaya Samir kamar daga sama da ban tsammaci hakan daga gare taba, murmushi nayi da a lokacin take qoqarin zama kujerar dake kusa da tawa da shima Yaya Samir ya zauna kusa da mamarsu.

“Ummi in yini”nayi maganar da alamun rashin sabo

“Lafiya qalau Sumayyah,ya kuka baro su mamarku”

Na ce”Alhamdulillah”

Daganan Ummin ta fara qoqarin kunna Tv tana cewa

“Bari a kawo miki abinci ko ciki zaki shiga,ki huta,kiyi sallah”

Kafin nayi magana Yaya Samir ya rigani

“A’a Ummi gwara ta shiga ciki ta gaji sosai koni buqatar hutun nake”

Ummin ta ce

“Shikenan taje ‘dakin,Fatima ka nuna mata tunda saika wuce bangaranku”ni dai kallon Ummin kawai nake dan har yau na kasa fahimtar farin ciki take da zuwa na ko akasin hakan,Yaya Samir ne ya miqe tare da cewa”taso na raka ki”

Ban musa ba na miqe nabi bayansa jikina duk a sanyaye da tunani da yawa a raina kodai zasu barwa Yaya Samir da yakawoni gidan ‘dawainiyatane,da wannan tunanin nawa  muka fara taka step har muka qarasa hayewa Yaya Samir kallona yayi bayan mun gama qarasa hawa

“Sumayyah kiya hakuri da yadda kika ga Ummi tayi Miki,ita ‘din haka take,sam bata fiye son mutane ba komai zance ne”
Murmushi nayi

“Yaya Samir to mene na fa’damin hakan”

Murmushin shima yayi ya ce

“Sumayyah  inaso Allah ya kawo sauyawarsu su so duk wanda zai ra’bemu Koda ba muda alaqar jini,dan su ‘din, bari dai kawai zaki tabbartawa kanki,yanzu ki shiga ki huta kiyi sallah ga ‘dakin Fatiman nan” ya qarasa zancen yana nunamin dakin da hannu da ganan yayi gaba ba tare da ya jira mai zance ba ba nida za’bi da wuce shigewa ‘dakin,komai na gidan masu ku’di yayi ‘dakin kansa kamar na tawa amarya yake Kuma ‘dakin budurwane kamar ni,dakin ya burgeni sosai,komai na dakin ya dace da muhallinsa,sallah nayi kawai kasancewarta qasaru ma,daganan na kwanta saman carpet ba yunwa nake ji ba,dan nasha yogurt ‘din da Yaya Samir ya siyamin a mota,ban jima ba barci ya ‘daukeni da tunanin makomata,a irin wannan gidan da Yaya Samir ya fara sanar dani,wanda dama na sani basu san talakawa,amma har yau nakasa fahimtar dalilin ‘daya qwaqqwara da ya Sanya Yaya Samir kawoni cikin rayuwar da bata dace dani ba”.

<< Na Cancanta 9Na Cancanta11 >>

1 thought on “Na Cancanta 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×