Skip to content
Part 14 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Mun da’de muna fira da Halima duk dai zancen na makaranta ne rabi da kwatarshi, Ina qoqarin kashe wayar na tuna banma Halima zancen Aliyu ba danako san zansha mita gurinta Halima ta Aliyu rabin zancenta na shi ne indai kunyi sabo da ita soyayyarsu tana burgeni Halima ‘din nima da nake mace tana sona a matsayin da yama wuce qawa sai dai ‘yar uwa bare Aliyu kuma na katse tunanin tare da yin hanzarin cewa

“Au Halima ya Aliyu?”

Kamar ba zata amsa ba naji ta a hankali tana

“lafiyarshi qalau na ‘dauka ba zaki tanbayeshi ba dan har zai fushi.”

Jinjina Kai nayi Kamar tana ganina “ah ni na isa Halima ai Kira dubu zance Aliyu sai yayi dubu zan miki.” na qarasa zancen ina dariya qasa qasa

Haliman ta fara”A’a Musa please stop sarkin qarya,na samu yanzu da kikayi ‘daya ma”

Nayi dariya na ce”toh Ina laifi ai zancenshi yana wajenki mu ji ne namu amma na cika zancenshiai kya tanbayi ba’asi ya Batul ?bari na katse na kirata”

“Uhmm uhmm fa kina da Hamid ‘dinki ga Yaya Samir ai na saurara miki dan kinyi zancenshi banace komai ba,ok Batul bana fa’da miki wani a family house nasu zata aura ba ai tayi shiru abunta ba yawo yaushe rabanta da gida,uhm mene ma sunanshi Yasir”

Nayi dariya”Kai Halima nasan kishinki na baki labari na ha’du da Malam Hamid ‘din ai ya ce ma zai zo wajena,oh su Batul ashe akwai labari,gaskiya bari nayi azamar kiranta zanyi ma,Mrs Yasir ma zan kirata da shi”

Halima ta sa dariya”ya dai kamata ni Mrs Aliyu da baki kirani da hakan ba kema ya kamata ki tsayar da gwaninki,mu sha bikinki kafin ma namu ni kinsan Ina sha’awar zuwa garinku ‘dinnan,ko yaushe gwarzo dai muje mu ga ni dai ya Gwarzon taku take dai”

Nidai dariya nayi
“Kai Halima,ai Yaya Samir ku kuke shagalinku ba saurayina bane,qila dai Hamid ne tom shikenan insha Allah zaku zo Gwarzo kuwa,amma fa qauye ne”

Halima ta kar’bi zancen
“Kai Sumayyah anya kuwa akwai fa lauje cikin na’di amma gaskiya Hamid ya rigashi,dan ni har na cire Malam a gefe,gashi saurayin qawata danko ko har yanzu yana school namu gaskiya dai ban iyawa Malam din nan,sai dai karfa ki qi shi ki kama yayanku please matsalar ina fa’da maku ke da Batul soyayyah da saurayi ‘daya tafi da’di ku bakwa gane karatun gashi nan Batul ta sha Yasir yayi ta maza,tom saura ke,Kai Sumayyah Banda qarya Gwarzon ku dagajin sunan garin ba qauye bace nasan tafi dai wannan anguwar taku anan cikin garin,Bari ma zan tanbayi Aliyu yana da friends ‘yan garinku may be ma familynku ‘daya za  mu yi maganar dai insha Allah”

Na bita da “tom shikenan “jin zancen bai qarewa zaro abunta take kawai gashi ko Umma ban kira ba bare Abbah,gani da zumu’din jin labari wajen Batul,har wani sauri nake bayan munyi sallama nasa layin Batul,dan Mama sai anjima Abbah ya dawo gida toh hirar ma dai kusan gaisuwa ce,sai Ahmad sarkin zance ya kar’be wayar ga Rumaisa,ga Khadija kuma

Bugu ‘daya biyu na ma Batul ta ‘daga ba wata tsayawa sallama nayi saurin Fara magana”Mrs Yasir,Sumayyah Abdallah ce dan ubanki”

Dariya ta kemin daga bangaren ta “Kai Sumayyah har da zagi kinje katsina fa ko kin kwaro zagi?,ai zamu zo mu tarkato ki da kayanki mu maidoki, nasan Halima ta miki zancen Yasir,a makaranta ma haka duk an kama Mrs Yasir,ai Halima ba’a sirri da ita,qilama yanzu ku ka gama wayar ko na kirata line busy,ashe ana nan ana zancenmu ni da bawan Allah,baki ga yadda yake ganin girman Halima ba nan baisan mutuncin ta ragagge bane”

Dariya nayi”na ce kunfi kusa da Haliman dai,tare ba barku,ba wani zance fa,kawai dai ce min tayi kinyi,saurayi a family house ‘dinku yake Yasir,kinsan Halima bama zata samu natsuwar min zancen dallah dallah,ba murna ta isheta nayi waya ne fa,na  fa’da miki iPhone

Qara Batul ta samin”Wow Masha Allah, Alhamdulillah congratulations,nayi murna kice zamu sha photunan candy da ita ki qoqarta yawwa Sumayyah ki dawo gida anata wuce ki fa karatu”

Na ‘dan yi Jim kafin na ce”Ina nan dawowa insha Allah,eh kam zamu sha photo kinsan iPhone akwai camera”

Batul ta ce”yawwa eh hakane hala Halima ta cika ki da surutun Aliyu da gulmata nida Yasir bata baki news akan school ba?,ai Halima ta bani ita dai ke Aliyu ai gwara muyi muyi candy ‘din nan ayi musu auren nan,ni Allah yasa ya samu da ita haka ma”

Nayi dariya ka ‘dan “ai Halima ranta na san Aliyu,da gani ‘din yana santa ‘dinne ai ba banza ba,da kinji zancen shi,ya Mata laifi ‘din idan ko da ya nayi ko baya santa Kamar ita din”

Batul tayi tsaki”wai Halima ‘din kin manta halinta kenan,abu na cinta bata fa’da kai dai ta dameka da san ji ko ta fahimta,da kanta”

Nayi murmushi kawai Kamar gani ga Batul nima tuno halayyar Halima nake yi halinta ni kaina na burgeni ba ruwanta harkokin ta ta keyi ni ban ta’ba ji ma tamin zancen damuwarta ba ita dai kullum ta saka farin ciki Aliyu kuwa ba na ce ga irin qaunar da take masa ba kai a jiki na sai nake ji dole ne ma kowa na da nashi damuwar ciki harda Halima kuwa rufewa take yi kawai ko ba tayi yawa ba dai akwai ta na sani, maganar Batul ta katseni

“Ya dai Sumayyah kin tuno ko ai halin Halima sai ita,ita dai ki ga kamar Bata da damuwa haka take al’amuranta,ni dai muyi candy ‘dinnan tayi auren dai kawai ta kyalemu da zancen Aliyu Ni yanzuma na rabu da ganinshi,ko dan bana zuwa unguwarsu yanzu?”

Na ce”Eh hakane Batul lokacin da zaki ba lallai ya zo ba,nima dai burina dai muyi SSCE ‘dinnan mu gama mu sha bikin mu wuce wajen,har ke ma”

Batul ta sa dariya”au kefa din kina maganarmu,Dan Allah ki cire wasa Sumayyah ki natsu ki kar’bi Hamid kiyi aurenki ba za muso muyi mu barki ba,duk ko wanne yanayi muke Mai sauqi ne akan naku,Dan Allah karki biyewa wasu mu zaki biyewa ki kar’bi Hamid tunda da gaske yake ki bashi dama kawai”

Batul kenan ba dai nasiha ba,ita tasan ba kowa yake kamarta ba,ita Kuma Halima gani take kowa tunaninta gareshi,duk kowa da yadda sanin yakamatarshi take ina alfahari da su ni kam sun wuce qawaye na, sai dai su tsaya matsayin Rumaisa da khadijah,harma sun fi haka saboda su age mate nawa ne na dai qoqarin danne tunanin na ce”Insha Allah Batul ina ta qoqarin hakan ya ce ma zai zo shi bai dai fa’damin ranar ba”

Batul ta ce”oh hala baki kirashi ba kenan Bari zan turoma ki layinshi Hamid mutumin kirki ne Sumayyah”

Da haka muka yi sallama ba da’dewa naji karar message lambar nake ta kallo inajin kamar na kira Kamar kar na Kira shawarar qarshe na dauka na dauki lambar na danna Kira….

<< Na Cancanta 13Na Cancanta 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×