Skip to content
Part 16 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Da tunanin wayarmu da Hamid na farka na Fara yini na da ita ina sake jin shi kamar mun jima da Fara soyayya daga ha’duwar mu zuwa yanzu na bashi matsayi mai girma nake ji a raina,zullumina ‘daya a yau ‘din wani kallo zai samu daga ni harshi wajen Abbah Hashim da tunanin na cire ta gumin da nayi na shiga toilet wanka na yi nayi alwalar sallar walha,dan kafin na shiga naga 9:30am lokacin Kam yama da’de dayi.

Shirina nayi cikin riga da siket atamfa mai black da coffee,batik ban tsaya dogon kwalliya ba,na fara tada sallahr sai da na idar na shafa powder da lipgloss a baki nasa brush na gyara girata kwalli ma ban tsaya nemanshi ba,dan bani da ma shi Dan kwali nayi zaman daurawa na nemi farin mayafi na aje gefena,kiran da naji wayata ya sa gabana fa’duwa sunan ubangiji na kira kafin na duba na ga mai kiran,Yaya Samir ne hakan yasa nayi saurin ‘dagawa

“Kin manta da break fast yau kenan naga baki fito amsa ba ko duk murnar wayar ne.”

Murmushi nayi kafin na bada amsa naji muryar Fatimah.

“Yaya yaushe kuma tayi waya,Ni inata fama ko Kai ko Abbah wani ya siya min sabuwa kunqi,nasan ma kaine zaka siyama ta.”

Tsaki naji yayi”Tanbayata kikeyi ko meye idan zakiyi shiriritarki kuyi da AbdulMalik”

Naji yana “kina jinah Sumayyah kizo ki dauki abincinki”

Murya a sanyaye “toh Yaya Samir”

Wayar ya katse ni ma na cire wayar kunne ina kallanta a raina ina sake ayyana ni da ma ya barta, ni takamaimai bansan anfanin da zata yimin,gani ma ina da gudun rigima akan waya,dama duka suna Yaya Samir ya fi sona a kansu,tom Ina ga sunji kawunsu yama siya min wayar gwiwa a sake na miqe na fita a qaton Dining Table na wuce su ina gaida Ummi da Abbah da Yaya AbdulMalik,Yaya Samir,duka da lafiya suka amshe dama nasan Yaya Samir baya tsawaita amsa gaisuwa duka harara suke miqamin musamman Abbah da Fatimah,ita dama exactly halin babanta gare ta,har gwara Yaya AbdulMalik yafi da na Umminsu,kawai saboda Fatimah ne da yadda Abbah ke nunamin suma suka fara tom bai nuna ina da muhimmanci ba a wajenshi bare su,har na shiga kitchen na gaishe da Baba Indo na dauki abincina na fito,zan wuce na na koma ‘daki naji muryar Yaya Samir.

“A’a Sumayyah shigo ki zauna falo,na ga ma kinci kwalliya haka Abid ko yau ma Ummi zata aike kune.”

Ina koqarin qarasawa na zauna Ummi ta fara”Samir bani son iskanci fa a aiken zan qare,sun janyomin Mahmud na tamin sababi na aikesu cikin rana nasan ana matsalar abin hawa unguwar nan,ni kuma nasan da mashiririciya na ha’da aiken kaga uwar kwalliyar da take fa”ta nuna masa ni ina qoqarin zama da dai mamaki tom tunda ni mashiririciya ce baga Fatima ba ta aiketa maganar Fatiman naji

“Ummi sai da nace ki Bari zanje,ni da mai ma ban tsaya shafawa, gashinan ai tayi sabar waya wa ye ya sani ma ko Kawu Mahmud ya siya mata saboda Aunty Asma’u,an bi an damemu suna Kama,har banasan zancen mukaje Gwarzo ma,su Khairat su bi su damu mutane,ni Aunty Asma’un ma haushinta nake ji”

Ummi naji ta fara magana cikin fa’da”Kinga fatima ki kiyayeni da zancen Asma’u karta kirani waya ta nemi cimin mutunci ki tsaya kan Mahmud shi take wasa daku,kinsan halin Asma’u batun waya ko ta millions zai siya mata ba ruwana,a cikin ku idan akace da munafukin da yake shirin fa’dawa Asma’u ma ke ko recording zasu iya yi,har Abban naku da kike biyewa,indai maganar Asma’u ne ware ki zaiyi,ba zan iya da halin Asma’u ba, shiyasa hanyar gidantama banaso na sani”

Abbah naji ya fara”Kinga Khadijah,idan kina magana da ‘yar ki ki daina sani a ciki,kunfi kusa da Asma’u da ta zauna nan wanne shiri ba kuyi ba,sai yanzu,dan bata auri naki ba ki kasan da rashin mutuncinta.”

Ummi na ji ta daura”To ni dama ai nasani, Asma’u ba tada mutunci,dana ga Kamar da gaske zasu dai daita da Mahmud ne da farko,tom ta raina arziqinshi lokacin ana zugata ana sai mai wasu trillions gefe, gashinan Mahmud shima yana dasu,har ya siyawa ‘yarku waya da kuka kasa ubantama baku rufamasa ‘dakuna ba,a cikin gidanku ya dawo ya zauna,sai nan gaba kunu na iko kan ‘ya’yan shi,sun gama wahalsu.”

AbdulMalik na kai doya baki na naji ya fara magana”Haba Ummi ya kike mana haka yarinyarnan tanaji fa ba bataji ba,yanzu ma meya ruwanki da familyn su Abbah,kinata maganar za’a samu maiyin recording nasan dani kike ni Asma’un banza da wofi me zata bani,waye baya zaginta a family,din,ni mai zwn aje layinta nayi mata ma.”

Ni dai dariya ma suka koma bani yau anyi walqiya an gansu a rana kafin anjima su sake ha’da kai,anjiman idan Hamid ya zo,Abid da Yaya Samir abincinsu suke ci suna kallansu,dansu da alama sunma qoshi da abincin shiyasa suke hayaniyar su

Kwanan na kai bayan na gama ci Yaya Samir ya ca na sameshi waje

A tsaye na sameshi a inda ya saba tsayawa na tsaya kusa da shi kallona yake Kamar ba zai cire idanshi akaina ba dukda ‘dinkin ba wai kamani yayi ba sai duk naji kunya dan ko mayafi ban saka ba,dan ba wai girman jiki ma gareni ba, gyaran murya naji yayi na dawo daga tunanina na kalleshi nima ni ya sake kallo

“Sumayyah!, hankali na ya kasa kwanciya da kwalliyar nan taki,kiya haquri amma dukda ba yawa tayi ba,ina zakije nasan hakanan kamar yanzu ma baki isa wanka ba ma.”

Inda inda na fara Ina”Zan….uhm…eh..”

Tsawa Yaya Samir naji ya dakamin sai da na tsorata ya fara”Ina wasa dake ba magana nake maki ba,ina zakije dama yawo kike ficewa kenan ko,gidan waye kike zuwa,waye naki anan bayan mu duka nawa ne kike wai, fa’da min gaskiya?”

Shiru nayi ina qoqarin ha’da kalmomin da zan fa’da masa ya yarda dani dan tsoron shi ma na Fara ji.

“Dama Yaya wani malamin mu zai zo nan Ni da Abid muka ha’du dashi wajen hanyar gidan Aunty Ramlah”

“Sai akace kice ya zo nan ko?”yayi maganar yana sake kallona

Na yi saurin girgiza Kai”A’a saqo zai bani Halima ta bashi ya kawo min yaje Kano ne wancan satin.”

Kai ya girgiza ya fara qoqarin tafiya”ya miki kyau baki Fara sanar dani , baruwana ke da Abbah ai yana gidan.”

Hankalina ya tashi Kamar nayi kuka jin an anbaci Abbah Hashim dama ya lafiyar giwa bare tayi hauka,na Fara magana”Yaya Samir I’m sorry dan Allah ba zan sake mistake haka ba,kama Abbah bayani”

Juyowa yayi ya kalleni yana hararata”kinga by mistakenly Kika sake cemin wani abu ha’duwar mu ba zata miki kyau.”

Na sake “Yaya dan Allah Kaya haquri”

Idanshi har sun fara ja ya ‘dago ya sake juyowa”shout up your mouth,kinji ko, wuce ki bani waje,sannan yazo naga kin wuce minti biyu ma,zakiga yadda zamuyi,wato ‘yan iskan malamai kuke kulawa a makarantar har layinsu kike ajewa akanki ma kenan,Halima kike min magana ko waye duk zasu shigo hannuna”

Da wasu hawaye fuskata na koma ciki na bu’de kofata na shiga da’kina,gado na fa’da ina kuka wiwi,ya zanyi ne ni Sumayyah, Yaya Samir ya kasa tsayawa ya fahimceni maiyasa ne ni,me nayi meye laifina anan,wayata da take qara ko kallanta banyi ba na cigaba da kuka na,qofar naji an buga da qarfi Yaya AbdulMalik na wai go nagani ranshi a ‘bace ya fara
“Fito munafuka, zaki San kin shigo gonar Abbah ne yau,baki Fara kuka ba ma”

Idona na shiga toilet na wanke har fuskata,bayan ficewarshi da yaja qofar da qarfi ,wayar na duba missed call a qalla 6 duk na Hamid na gani dama a within lokacin na tsammaci zuwan nashi,amma nasan zuwan zai qaramin ‘bacin ran ne da Yaya Samir ya sani yanzu ga Abbah Kuma kafin na qaraso falon naji muryar Ummi ta na

“Ni kaga Hashim yarinyata Fatima ba neman mijin aure take ba kuma ba wanda zaisa ta fita waje saboda ba ita ake Kira ba,’diyar qaninka da baku sonshi shi da matarshi bare ‘ya’yan shi to su masu arziqin Katsina suke kira ba ‘yata ba bana baqin ciki bare jin haushi ‘ya’yan naka ma da ‘dai da ‘dai zasu gane halin naka na baqin ciki da kyashi,kai a gidanka nufinka arziqi zai qare ko menene, Asma’u ma data yaudarar min qanina aka ha’da baki da Kai data samu gidan da kuke mata hangen kaf cikin familyn mu har Mahmud murna muka mata bare kuma Sumayyah ‘yar cikina…”

Da wannan na qarasa shigowa n durqusa gaban Abbah ina “Abbah gani”

Wani mugun kallo Abbah ya bini da shi “kece ko Fatima wanene cikinku ya ha’du da Hamid Saraki ,gidan Muhammad Saraki”

Ummi naji tayi saurin dakatar da shi haka “A’a ya zaka dauko wani zance dogo haka iya Hamid kace ai zata gane ni banasan rashin gaskiya”

Ummi ta kalleni “ke ce ko?”

Na ‘daga kai ,ta nunamin hanya “ki fita yana jiranki a waje ki shigo da shi har ciki”

Naji ta cigaba kafin na qarasa fita”Abin kunya,uba na yiwa ‘ya hassada,danni ko a mafarki banyi tunanin ko ‘dan shugaban qasa zaizo wajen ‘diyar qaninka Abdullahi zaka yi haka ba,meye ubanta baiyi tsaya yayi da guminshi,da ‘yan ku’dinshi yayi ma ba,amma bakada tabbas akan alaqarta da yaro,bakasan asalin uwarta ba,baka tunanin ko familyn Hauwa’u nema kazo kana abubuwa haka gaban yara….”

Da wannan na qarasa ficewa ina goge hawayen idona,ummi ba tada laifi dama tun farko yadda taga Abbah Hashim na nunawa yasa bata nuna kulawarta a kaina,dama ance naka ke ba da Kai amma naji matsayin Ummi ya qaru da ganin martabarta,Yaya Samir na tuno inaji kamar na koma na fara bashi haquri amma nasan bazai saurareni ba,ko dai hasashen su Halima ya tabbatar shima Yaya Samir sona yakeyi ya zanyi da Hamid gabana ya fa’di,idan nasan cancanta ne Yaya Samir ya cancanta na aureshi fiye da kowanne namiji amma ya zanyi da Abbah Hashim shine bazai amince ba ko da Hamid na ce masa ga Fatima yadda naga Abbah Hashim yake so,nasan bazai bari da yawunshi na auri Samir ba duka ‘dinma nawa nake amma inajina wata daban a yau din kamar bani ba kofar gate na bu’de na fita a tsaye na hangoshi da waya hannunshi yasa ta a speaker inajin ringing nasan wayata yake ta Kira da damuwar da na hango a fuskarshi na qarasa inda yake

“Assalamualaikum”

Saurin ‘dagowa yayi
“Sumynah,da nayi tunanin ba zaki fito ba” yayi maganar yana nunamin wayarshi “kingani na miki missed called a qalla 15 ma,dukda Abbah yacemin kina zuwa,amma naji yana Fatima dai ko na ce ma sa, Sumayyah nake kira na kiraki ma missed Called 6 baki ‘dagaba to ya shiga yana kokwanto wacece Fatimah?”

Na murmushi kawai kafin na ce” kaya haquri kaina yayi ciwo shiyasa ban ‘daga ba,Fatimah sister na ce,’diyar Abbah Hashim ‘din ce yayan Abbahmu ne, kaga sune anan ‘din,dangin mamarta kusan kaf suna nan ‘din,kowa bashi zaiyi wajenta a kazo,ni Kuma na manta banyiwa Yaya Samir maganar ba,ya fa’dawa Abbah”

Hamid ya kalleni “Ayya sorry sannu ba da’dewa zanyi ba saiki kwanta kisha magani amma,baki bani labarin Fatima ba jiya”

Na ce “na manta Ummi ta ce ma ka shigo ciki”

Hamid ya girgiza kai”A’a zan koma zan dawo wani lokacin”

Shiru nayi ina tunanin ko Abbah Hashim ya masa wata maganar ne bansani ba na dai daure na ce”Amma kuma danni fa ka zo”

Murmushi ya yi “kinga Sumy ai Zan dawo ne da abin mamaki ma Zan dawo ba dai nazo din naga sumynah ba,yawwa Abbah ya ce min idan ina sanki na fito kawai,bai dai gane ba ya ‘dauka wajen Fatima nazo ne,yana mamaki ne nake tunani yadda Kika fa’damin kinga Fatima ce anan,ke Kuma baquwa ce to da mamaki”

Gabana naji ya yanke ya fa’di nayi jim kafin na ce”Amma dai kuma…dai…”nama kasa maganar

Yayi dariya ya Fara kwaikwayata”Amma dai kuma dai Kuma me oya fa’damin yayi kusa kenan kome,nayi laifima da na fara zuwa qofar gidanku ba tare da magabatana sun Fara zuwa nemarmin izini ba,tom kinsan zamani ne gaba ‘daya nama kasa tunanin ya kamata sai yanzu da Abbah ya nunamin,insha Allah da kawuna ya dawo,zasu zo ,Sumy ina tsoron rasaki,ke fa?”

Ido na rufe ni kam ya bani kunya ma gashi ya tsareni da idanunshi

“Au bazaki magana ba,mene na kunya anan oya ‘dago fuskarki,kimin magana kice nima Ina tsoron rasaka”yayi maganar yana sake kallona yana sake lumshe idan shi ina hango hakan duk da rufe fuskar da nayi na dai daure

“Tom nima haka”

Murmushi yayi “yawwa ko kefa ya’dan yi ba laifi,Zan tafi?”

Na ‘dan ‘bata fuska na ce”haba mana AbdulHamid ka shigo ciki kaqi,Ummi ba zataji da’di ba”

“Oh Sumynah zan shigo fa,har cikin falo ma Amma ba yau ba,ko kawu bai zo ba,zan ma Hajiya magana,Abbahna da kanshi zaizo ko sati biyu ma bance miki za’ayi ba ‘daya ma yayi yawa a gurina insha Allah,ki mana addu’a kawai, Allah Ni a shirye nake fa,zan tafi fa,Zan biya gidan Auntyna maman Halima da na baki labarinta” yayi maganar yana kara kallona

Na ce”tom shikenan,Allah ya kiyaye hanya agaida Halima da mamarta”

Murmushi da ya zamar masa jiki kusan zan iya cewa ya sake yi ya ce”Yawwa Sumy zan wuce,kingama na manta ma ne,zan Kai Hajiya unguwa to bata san,kowa yayi driving nata sai ni”

Sai lokacin na lura da motar da aka Parker ta gefen gate ‘din gidan Abbah Hashim da ga gefe a rubuce jikin motar na karanta sunan motar mercendes ce White color banyi wani mamaki ba dan dama tuni zuciya ta ta rayamin hakan tun daga kallan farko da na yiwa Hamid ‘din su Halima da Batul ne banjin sun fahimta,keys ya ka ‘da shi ya dawo dani daga tunani na ya ce
“Yadai Sumy baki so na tafi ko,sorry Zan dawo fa,baga waya ba ban maga wayar ba,idan na dawo karki manta ki fito da ita na gani”

Na ‘daga Kai kawai a haka mukayi sallama ya ja motarshi ya tafi,shidai a gefenshi nasan iya gaskiyarshi da yardarshi ya aza a kaina ni Kuma abubuwan da ke danqare a tunanin gobena bama ta soyayya ba nake ina dauka ta Hamid kamar me sauqi ce akan tawa,ina tunanin kawai shawarar da Zan yanke ne kawai inason cigaba da samun farin ciki a cikin yanayin rayuwata yadda ta fara,ana cewa kwaryama tabi kwarya nasan da Hamid ya gama fahimtar wacece ni nima a farko na gama fahimtar waye shi babu soyayyar da zata ha’da mu,jina nake kamar ba Ni ba mema ke shirin faruwa dani ne ma, qoqarin mai da kwallar idanuna nake kar ta cigaba da zubowa a lokacin da banajin ta da ce ta zubo qarar bu’de kofar dake jikin gate din ta fitowa ya dawo dani tunanina na juya naga mai bu’dewar Yaya Samir na gani fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce

“Idan kin gama kizo ina San magana dake”

Yana shigewa bani da za’bin da ya wuce na bi bayan shi,inajin takaicin ma komaima na rayuwar duka ma nawa ne nake,Amma matsalar rayuwar da muke komai cikin godiyar Allah,yanzu Kuma ni Sumayyah wai soyayya banmasan qarfin halin da yasa na saurari Hamid ba,wai harna qirqiro kalaman da suka da ce na furta,oh ni Sumayyah da wannan tunanin na qarasa shigewa gidan.

 

<< Na Cancanta 15Na Cancanta 17 >>

3 thoughts on “Na Cancanta 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.