Skip to content
Part 2 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Yau da ta kasancewa asabar tunda kannena suka tafi tahfiz nayi shirina na zuwa gidansu Halima da ni yau na Sallama tahfiz din kasancewar shirin da mukayi da Batul zamu gidansu Halima da Batul din nake jira da zamu dubo jikinta da tun laraba rabon Haliman da makaranta da tunaninmu bai bamu Halimar batada lafiya ba ,saida class master namu ya fada a aji a jiya data kasancewa juma’a da cewa litinin za’a dubata gaba ‘daya ajin namu dalilin da yasa mukayi shirin zuwa yau kenan.

Sallamar Batul da naji na kuma ji muryarta tana gaida Mama da take aiki a tsakar gidan yasa na karasa daura dankwalin da tun dazu nake fama da shi na kasa daurashi.

Inaji Mama tana cewa Batul
“Sumayyah tana dakinsu”

Dakinmu ta shigo tare da sallama.

Na amsa sallamar gami da harararta.

“Sai yanzu kikayi niyyar zuwa wajen sha biyu saura dana san ba zaki zo da wuri ba dana tafi makaranta kawai.”

Batul da ta zauna kusa dani tace,

“Kai Sumayyah  kina da matsala ba gani nazo ba,kinsan unguwarmu wuyar adaidata sahu ake”

Na kalleta

“Kai Batul da’dina dake akwai share guri,yanzu Magashin ce ba’a samun napep kamar kauye.”

Tayi dariya.

“Ai ta shigo kauyen gandun Albasa ne basa son yi.”

Na mike ina yafa mayafina dan na daka ta Batul ba zamu tafi yanzu ba
“Kinga muje da wannan firar taki mara k’arewa.”

Mama mu Kama sallama ta bani kudin Napep naira dari har zamu fito Mama ta kirani  ta fadamin na biya gidan Aunty Asma’u na gaidata,badan na soba na amsa mata da cewa zamu

A dari da hamsin daga gidanmu aka kaimu zoo road har kofar gidansu Halima
A ‘dakinsu muka tarar da Haliman itada Mamarsu bayan mun gaisa da Mama Haliman da mukewa sannu ta juyar dakai mamarsu Haliman tayi dariya ganin ta’ki kulamu Haliman

“Ai dama tace ba zata kula kuba koda kunzo ,kwana da kwanaki bata da lafiya ba kuzo dubata ba”

Nice na kalli Haliman da duk ta rame.

“Mama bamu sani ba,sai a jiya,ki bata baki”

Mama ta mi’ke ta bamu guri tana cewa

“Kunsan dai halin Halima sai dai ku lallasheta tunda kune kuka mata laifi”da haka ta fita tabar mana dakin.

Dakyar muka lallashi Haliman ta hakura mun dade muna fira da ita har wajen uku saura a lokacin na tuna da zani gidan Aunty Asma’u, Batul na kalla

“Kinga sai yanzu na tuna zani gaida Aunty Asma’u”

“Lah nima na manta”

Har na mi’ke na kalli Batul data sake gyara zamanta

“Ba zaki rakani ba ne”

Ta girgiza kai

“Sai kin dawo,dan gaskiya koda take kanwar Abbanku ba zani inda za’a wulakantani ba,da dai ‘yar uwata ce da sainace ta zamarmin dole,watarana ta yiyu na sake zuwa gidanta”

Sosai naji haushin maganganun Batul amma na sani ita ba ruwanta abunda ke ranta ko baida da’di saita fa’dama,wannan d’abi’a ta Batul yasa bama shiri sosai,Halimace tawa dako mai abunda za’a mata idan munje dangina bata nunamin taji haushi,bare harta fa’dawa wani,dukda itama Batul ni da ita take fa’damin ba wani take fadawa ba,amma hakan ba da’di

Zaman mayafina na sake gyarawa da banji haushin abinda ta fadamin ba
“Nace karki je,dama Halima ta fiki mutunci”

Hararata tayi

“Eh naji”

Halima ta dubi Batul

“Yanzu Batul da gaske kike ba zaki ba,ni da zan iya tafiya mai nisa da na rakata”

Batul ta harari Halima

“Halima nafa rantse ko Mamarmu ‘daya da Aunty Asma’u ba zan sake zuwa gidantaba haba kin manta wulakancin data yi mana,muna zaune a gidan ko ruwa bata bamu ba,’kannen abokan mijinta na zuwa,ta aje musu soyayyun kaji da ruwa da yoghurt saboda su suna da wadata,haba nifa kinganni Koda ubana baida komai ba wadda ta isa ta ri’ka wulakantani,dana fahimceki zan ja miki layi ko ya muke”

Haliman data ja zancen tace

“Ya isa haka Batul menene na tada abunda ya riga ya wuce,tunda kikace ba zaki ba ai shikenan,’dan uwa fa ‘dan uwa ne”

Murmushi tayi

“Halima kenan wani ba”

“Kowanne ma”

Jin zancen bazai ‘kareba nasani barin ‘dakin dan kaina ma zai iya ciwo ba kasafai nakeson hayaniya ba,kuma nima na tuna wulakancin data mana da sai da wa’dacen ba’kin nata suka tafi taja mana farantin ‘kasusuwan naman da suka rage,wai a matsayina na ‘yar wanta uwa ‘daya uba ‘daya talauci kenan ‘ya’yanta kuwa babu wanda ta bari yazo gurinmu suna can saman bene bama su sauko ba dan dama can kayan wasansu yake da komai da tunda nake so d’aya na ta’ba hawa up din.

Da wannan tunanin na karasa fitowa daga cikin gidansu Halima da ina fitowa naci karo da Yaya Hakeem yayan Halima yana k’o’karin shiga gidan ni kuma na fito gaisawa mu kayi ya dubeni kasancewar jinina dashi ya ha’du fiye da sauran yayyen Haliman biyu da Yaya Hakeem ‘din shine babban a gidannasu

“Badai sai yau Kika zo duba ‘kawar taki ba”

Na ‘dan rufe fuska alamun kunyar abunda nayi

“Eh Yaya Hakeem bansan da rashin lafiyar Haliman ba sai jiya”

Yace

“Bansaniba jiya har unguwarku naje gurin wani abokina,kinga da nasan baki sani ba dana biya na fa’damiki,ko da ke ma idan naje bakiso nazo gidanku”

Na ‘dago kai na kallesa.

“Eh mana,kwanaki da naje unguwar naga Ahmad a waje nasa ya kiraki mu gaisa,’kin fitowa kikayi”ya ‘karasa maganar shima yana kallona.

Nace,

“Lokacin aiki nakewa Mama,kuma bata nan lokacin”

Ya harareni

“Da’dina dake da’din baki,har kin fito zaki tafi?”

Na girgiza kai

“A’a zanje gidan Aunty Asma’u ne,tare da Batul mu kazo”

Yace

“To shikenan saura ku wuce baku min sallama ba”

Murmushi nayi

“A’a zamu yi ma insha Allah”

Daganan ya shige ciki nima na wuce ina tunanin halayyar su Halima duk gidansu suna da kirki basu da matsala takowanne fanni,duk abinda wani daga cikinsu ya nuna yanaso suma suna sonshi,Yaya Hakeem kuwa kamar Yaya haka yake a gurina,yadda muke shiri da shi koda Halima basayi haka,duk abinda yayi wa Halima to nima saiya yimin Batul ma yana yi mata sai dai ba kamar ni ba ina tafe ina wannan tunanin har na karasa gidan Aunty Asma’u

Sai da na buga gidan maigadi ya le’ko dukda ba wani sani yayimin sai dai yadda nake zuwa gidan jefi jefi yasa ya ganeni da kuma kamar da muke da Aunty Asma’u dani dangin mahaifina na ‘debo sosai ba abunda ya banbantani da Aunty Asma’u saidai ita hutun data samu yanzu yasa kyawunta ya fito sosai,kofar ya bu’demin da murmushinsa ciki na shiga ina gaida maigadin Ya amsamin
“Lafiya lau,’yar hajiya ashe kina nan,yaushe rabonki da zuwa”

Nace

“Baba makaranta”

Ya ‘daga kai

“Hakane Allah ya taimaka”

Na amsa da Amin na wuce

Saboda kamar da muke da Aunty Asma’u Baban ya tanbayeni ala’karmu da Aunty Asma’u ya muke na shaidamata tun daga ranar yake fa’damin ‘yar hajiya,harabar gidan da motoci a kalla uku suke kuma duk masu tsada na wuce kofar falon na karasa nayi knocking kasancewar gidan upstairs ne nayi sa’ar ina knocking naji kofar bu’de na tura kaina falon da ‘kamshi Mai da’di ya bugi hancina Aunty Asma’u tanada tsafta sai dai matsalarta ‘daya rashin san talaka duk abinda talaka zaiyi mata baya burgeta koda ‘dan uwantane tun ina yarinya idan munje Gwarzo nake ganin hakan waima ni dalilin da yasa bata min wulakanci kamar ‘kannena saboda kamar da nake da ita amma dai duk da hakan bawai tsira nayi ba a gurinta,da ‘yar aikinta da bata wuce tsarata ba naci karo,tana goge center table da ya kasance na glass,sallamar da nayi ta amsa,tana yimin

“Sannu da zuwa”muka gaisa ta shige ciki da towel din goge gogen a hannunta tana cewa bari ta kira Aunty Asma’un “to” kawai nace na bita da kallo,ina ayyana wannan Harira da yake sunan ‘yar aikin wanne irin zama take gidan Aunty Asma’u dan Harirar ba wata wayewa tare da ita gaskiya tana hakuri dai da Aunty Asma’u a raina na ayyana hakan fa’dan Aunty Asma’u da na jiyo ya katsemin tunani

“Sai akace kice mata bari ki kirani,Wai maike damunki Harira”

Naji muryar Harirar

“Ya hakuri Aunty gani nayi ‘yar uwarkice”

Cikin fa’da Aunty Asma’u naji ta cigaba

“Da take ‘yar uwata mai zanyimata nima ba wani abu gareni ba,idan ma wani abu ubanta ya turo ta kar’ba masa danni bani nace ya’ki neman nakansa ba,koya zauna da mace mai ‘kashin tsiya,tunda Allah ya rufamin asiri dangi duk an zuramin ido”

Banga laifin Aunty Asma’u ba saboda NA CANCANTA ta  fa’damin hakan laifinane a karo na barkatai na sake tun karar rayuwar da gininta bai dace dani ba,karar takalmanta da naji yasa ni maida dubana ga matakalar benen da Aunty Asma’u take sakkowa da takunta na kasaita daka ganta zaka tabbatar ku’di sun zauna mata duba da kalar kayan jikinta da yanayin jikinta fatarta sai sheki take alamun hutu ya ratsata da murmushin da nake da tabbacin ‘kir’kirarsa tayi ta karaso cikin falon tana ‘ko’karin zama kujera tace
“A’a Sumayyah kece a gidan nawa yau”

Na ‘dan murmusa nima

“Eh Aunty ina yini”

“Lafiya kalau,ya mutanan gidan ya hanya”ta fa’di haka tana danna remote ‘din da ta ‘dauka a kujerar da take zaune

Nace”Alhamdulillah,Aunty dama gidansu Halima nazo bata jinda’di shine  na biyo mu gaisa”

“Allah ya bata lafiya” ta fa’da

Na amsa da

“Amin”,daganan na mi’ke ina gyara zaman mayafina tamkar babu komai naji tace

“A’a badai har tafiya zakiyi ba ko ruwa ba’a kawo miki ba”

Nayi murmushi mai ciwo

“Alhamdulillah,da batul muke tana jirana ne”

Ta mi’ke itama

“Eh dukda hakan dan Allah koma ki zauna na kawo miki kudin ko napep saiki hau da su”

Nace

‘A’a Aunty ki barsu da ku’di a hannunta”

“Eh dukda hakan nawa dabanne”ba tare dana sake cewa komaiba ta sake hayewa sama ban jira dawowartaba nayi saurin ficewa daga gidan a raina ina ayyana nida gidan Aunty Asma’u ko ba har abada ba zan da’de ban jeba dan wanna abun da take min tunaninta naji abinda tace ne shiyasa yau bata yimin rashin mutuncin data sha yimin ba,a haka na iso bakin gate ‘din ganin banga maigadinba yasa na bud’e kofar na fice dan raina ‘bace yake bazan iya jira ya dawo banbarmata gida ba,a haka na fito a raina ina mai takaicin rayuwa irin wannan saboda damar da Allah ya baka hatta danginka saika za’bi da wa’danda zakayi huldar zumunci dasu nida kaina nasani muba masu dukiya bane da abinci yau da gobe yake gagararmu bare har azo inda muke dan kyautar dubu ashirin ba zamu iya bayarwaba da itako Aunty Asma’u d’ari ma ta bayar ba abun a tanbaya bane dalili mai ‘karfi yasa ta ‘dauki duk mai  zuwa gurinta kwa’dayayye muddin bamai ku’di bane,niko a nawa ra’ayin dukda idan aka bamu muna bu’kata amma ba zanje inda za’aci fuskata ko a’ki darajani ba dukda NA CANCATA a yimin hakan a tunanin mafi rinjaye a cikin al’umma amma ni anawa tunanin da yardata Allah ke rabawa nima zai iya rabawa ya bani,dukda ba kudi gareni ba a hannuna amma na gwammace na tafi a kasa saboda maganganun marasa da’din da kunnuwana suka jiyemin,koma ba haka ba nasaba zuwa biyar bata hadani da ita kawai inaso Aunty Asma’u ta fahimta a cikin talakawanma akwai wanda yasan darajar kansa,bansan irin yadda zan misalta canjin rayuwarnan ba da ‘kar’karin koda kyautar muce ga ‘yan uwan Abba dubu biyar shima sai Mama ta haihu dan mai ku’di inda yake kai kyautarsa inda yasan zasu dawo,bawai gurinmu talakawa ba,amma na sani Allah yana tare damu hawayen da suka zubomin nagoge ganin na karaso gidansu Halima,ko minti goma bamu ‘karaba bayan komawata gidan muka fito a ‘kasa muka fara tafiya dan ba ku’di hannunmu ragowar hamsin ta rage mana da sai munje unguwarmu Batul zata hau napep ta karasa gida da sai bayan fara tafiyarmu na tuna da Yaya Hakeem yace na masa magana idan zamu tafi.

<< Na Cancanta 1Na Cancanta 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×