Skip to content
Part 20 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Misalin qarfe goma na safe na kammala shiryawa, Halimah ma ta shirya dan Yaya Baffa zai kaini Tasha tako ce lallai sai ta bishi an rakani da ita Faisal ya dauki jakata ya kaita napep dake kofar gida,Abban Halimah da mamarsu ku’di suka bani nayi ku’din mota da inada niyyar qin amsa Halimah kuwa ta kar’be tace su bata ta bani,tasan halina na musu godiya duka gaisuwa suka bani nayiwa su Mamah da qannenah,haka muka fito ina sake jin qaunar Halimah da ahalinta a raina muna tafe a mota Halimah tana jana da fira har ni kam hankalina baya wajenta tunanikane kala kala a raina ga uwa uba kewar Halima da nakeyi ga Batul ma bamu ha’du ba babu damar hakan hankalina yayi gida ne,Halimah ta kalleni

“Haba mana Sumayya sai zance nake kinmin shiru”

“Yi hakuri Halimah ban jiki ba”

Yaya Baffa ya ‘dan juyo ya kallemu
“Haba keko Halimah tunanin gida takeyi barta tayi abunta,nasan ji take kamar tayi tsuntsu ta jita gida,na dauka zakuce ma zaku biya gidansu Batul ai,naga munzo unguwar”

Kamar jira muke yi yayi zancen Batul cikin ha’din baki muka amsa
“Zamuje mana Yaya Baffa”

Kwanar layin gidansu Batul yayi ba wata tafiya mai nisa sai gamu kofar gidan nasu,Dan qaramin gida amma jikin family house dinsu yake Batul tace mana duk cikin family house din nasu aka yi gidan nasu,Kamar jira muke napep din ta tsaya mukayi saurin ficewa a motar,Yaya Baffa na koramana kashedin kada mu da’de,da Batul muka ci Karo zauren gidan nasu muna tura kofar,wani ihun murna ta saki
“Sumayyah oyoyo ashe kin dawo ba labari,qila ma kina Kano shekaran jiya da mukayi waya,mu shiga ciki”

Halimah ta kalleta
“Ke malamah sauri fa muke da Yaya Baffa muke,kinsan ashe su Sumayya sun koma Gwarzo fa,nima sai jiya da Sumayya tazo naji labari,itama batada masaniya a gidanmu ta kwana ma, yanzu Gwarzo zata wuce muka biyo,muje mu gaishe da Mama dai mu fito”

Batul ta harari Halimah
“To aku mai bakin surutu aina dauka ma gaishe da Maman ma ba za’a shiga yi ba,Abbah ma yana ciki,amma banji da’di ba Kamar nayi kuka”

Da haka muka qarasa ciki Halima na fa’din “Nima haka naji Batul ya zamuyi an saba,kamar nayi kuka nakeji”

“Ke dama uwar kuka ba”
Duka dariya mukayi banda Halimah da ta ha’da fuska a tsakar gida brander muka sami iyayen Batul zaune a qaton tabarma da qannenta duka kasancewar Batul itace babba itama,kamarni,gaisawa mukayi Batul ta shiga koramusu jawabi cewar mun tashi mun koma garinmu Abban su Batul cikin rashin jin da’di ya kalli Batul
“Amma ba jimawa dai da hakan,da ai baza’ayi haka ba, indai matsalar haya ne ga gidan Abbahnku sai su zauna har Allah ya hore musu,aikinma Banda abun Abdullahi ai nema akeyi ba’a zama haka,amma banji da’di ba”

Maman Batul ta girgiza Kai da damuwa fuskarta
“Nima haka Abban Batul gashi duk sun saba, za’a rabu Kuma,qila shima yanada buqatar komawa,shiyasa ba labarin kome”

Cikin jin da’din yadda iyayen Batul suka nuna jimamin komawar na rashin Jin da’din su na yi magana
“Ai mamah mai gidan da muke hayarne ba zato yazo ya bada notice Abbah nasan bai samu lokacin tsayawa wani tunani ba sai ha’da kaya kawai suka koma gidan duka”

Abban Batul ya dubeni
“Hakane amma kwanaki baya mun ha’du ya fara jan napep yacemin Alhaji Yassar ya samu daga wajenshi,Ahmad ma ya samu yake ja”

Halima ce tasa baki lokacin
“Ai Abbah napep din Faisal yace ta lalace ba ku’din gyara shine ya maida musu kayarsu”

“Aini Abdullahi na rasa irinshi tunda yara sun ha’da mu ba’abun yana boyemin abubuwa da yashafemu duka bane,ko yazo wajena ko mun ha’du ba wata magana da za’a taru a jajanta ko abunda ya shafi buqatar taimako da zai fa’damin na rasa wannan abun nashi,tafiyar Sumayya ma sai bakin Batul naji yanzu ai an zama ‘daya,dama ‘daya ne tunda school ‘daya ma mukayi a lokacin da yake yin masters”Abbah ya qarasa zancen da alamun damuwa

Haka duka jikinmu sanyaye muka miqe sosai nasan halin Abbah shi kullum maganarshi ‘yan uwanshi su kasa taimakonshi inaga wasu abokai kowa yana ta iyalanshi da familynshi,shi kanshi Abban Batul din ba wata dama gareshi ba sai da muka shiga JS3 muka fahimci akwai sanayya tsakanin Abbanmu da nasu Batul ‘din dukda kawai zaman aji ne ba wata gaisawa ake ba ayi lecture ne a fito saiko assignment ya ha’da ko presentation ko wani research ‘din a irin wannan Abbah yasan Abbah Ahmad ‘din

Batul hanyar falonsu ta yi a maimakon mu qarasa fita waje Halima ta Kira sunanta”mukam ba falon da zamu shiga”

Batul taja hannuna
“Kinga Sumayya zo mu shiga dan Allah,kyale wannan Haliman ta jira mu a wajen,nasan saboda Yaya Baffa kada ya Mata banbami take wannan”

Ummansu Batul ta kalleni
“Au wai ba ku ka’dai bane?,ya kamata ku kyale Batul ‘dinnan,Kuma zo ku rakata sai ku dawo da Haliman su ajiyeki”

Halimah tayi saurin amshe zancen
“Eh Ummah mu da Yaya Baffah ne kuma yace sauri yakeyi saboda muma yayi lattin fita”

Ummah da take Shirin sake magana Batul tayi saurin marairaice murya
“Ummah dan Allah wata kawai ‘yar magana fa zamuyi minti uku ma yayi yawa”

Ummah ta maka mata harara
“Tatsuniyar gizo dai nasan bata wuce koqi zancen dai Yasir ne”

Abbah dariya yayi wa Ummah
“ai Batul da Yasir bansan wa yafi san wani ba,har nima na qosa na musu auren nan,zance kullum saboda yana ganin shi ‘din dan gidane”

Da wannan muka shige falon muna zama a kujerun Batul dariyar data kunso ta fara yi,Halima ta dube ta
“Kinga ba musan hauka fa malama meye wai dama aje mu kikayi ki dinga dariya”

Batul ta ha’da rai kamar ba ita ta ke dariya ba
“Kinga Halimah bafa ni nakai zomon ba,Ni nace ki ‘bata da naki saurayin mai kan kwakwa”

Halimah da masifa ta dubeta
“Kinga Batul ki fita idona da cin mutuncin Aliyu fa,Kuma gwara shi ke naki saurayin kan giginya gareshi”

Ni abun nasu dariya ya bani na kallesu”kunga ya isa haka dan Allah,Halimah barta tayi maganarta kinsan Yaya Baffa na jiranmu dai ku nake jiyewa karya juyeku a Rijiyar zaki ya kwashi passenger ko ya dinga yawo da ku da passenger kuma a motar,ko biyu yake samu ya rage zafin ‘bata masa lokacin da kukayi”

Batul ta makamin harara “Aniyar ki ta biki mai baqin fata,insha Allah ke Zaki hau rigwagwaar mota banda munafinci ina Kano ina Gwarzo amma tun goma Zaki ce zaki wuce saboda kin gaji da ganinmu,babu amana,bansan ya zaki koma kikayi aure ba Hamid ya kwasheki Katsina ya kaiki ya ajiye”

Halimah ta kalleni kafin ta kalli Batul
“Kinga wanne Hamid ai anbar yayinshi ga Samir nan yayanta kinga ko banza Abbah Hashim ya mareta ta wata rana idan bata Kai ga dukan ba”

Batul ta kalleni”Subhallah meya faru kumin bayani haba ni dai nasan ba lafiya ba,tunda naga Sumayyah haka ayam”

“Uhm ina ko lafiya matsiyacin mutumi nan ya kama Sumayya ya mata shegen duka,yanzu ma saida ta gasa jiki da ruwan zafi”Halima tayi zancen ta qarasa bawa Batul labarin komai

Batul ta kalleni cikin tausayawa”,Kuma yanzu kin amince da Samir din,gaskiya ki yiwa Hamid adalci da babu Hamid ko dan Abbah Hashim da saiki amince da Yaya Samir ‘din amma kin bawa Hamid dama tun farko”

Na kalli Batul”nifa Batul wallahi komai ya fita raina fa,na rasa tunanin da ya dace dani Dan Allah ma kada ku bawa Hamid labari game dani,ni dagashi har Yaya Samir na haqura da su,idan na qi kar’bar Yaya Samir saina kega nayi butulci dukda shi ‘dan uwana ne,tun ina yarinya nakejin labarin irin son da Yaya Samir ya nunamin,wajen Mama kafin su koma Katsina mu dawo Kano dana mantashi da kanshi ya daukeni kawai dan na tunashi wannan abun da ya faru qaddara ce kawai,da nasan da cewa Yaya Samir na Sona bazan iya amsawa Hamid ba saboda bansan shima daga gareshi mai zan tarar ba”

Batul ta dafani”Dan Allah ki daina wani tunani kiyi addu’a insha Allah zaki samu mafita, addu’a itace mafita kawai Allah ya za’ba mafi alkhairi,kuma ni kaina bansan me zan cewa Hamid ba idan ya tanbayeni game dake kin riga kin gama masa magana kince ya yi hakuri,tunda Kuma ga qudirin Abbah Hashim akan hakan kinsan halin wasu mazan idan yaga Fatimah ta fiki a wajenshi zai fi amincewa da ita qila a hasashena fa tunda zumuncin naku ya zama ga irinshi,ni kinga Yasir babanshi yana da ku’di sosai amma ba wani wanda yakai korafin Abbanmu akan shi talakane kada Yasir ya aureni,kinsan ko da muke ‘yan uwane da danginkune sai sunyi,yanzu haka kinga Yasir har ya kawo ku’din aurena ma,shine zancen fa da zan muku”

Fatan Alkhairi da addu’a muka mata, kuma naji da’din kalaman Batul sosai,sai naji zuciyata ta nutsu

Halima ta kallemu”kunga ku taso dan Allah kun cikamu da zancen soyayyah ni wayata ma kashe take kada ma kiyi tunanin Hamid zai kirani blocking nashi ma zanyi dan bansan me zance masa ba,nifa tunda Aliyu ya bani haushi kowanne namiji ciki nake dashi”

Tsaki naja mata”kinga kin damemu Aliyu Aliyu dai kawai idan da gaske yake ya turo muyi dai mu gama fa’da kuma ta yiyu ke kika ja tunda ke ‘din zuma ce sai da wuta wani lokacin,sanda Kuma zaku shirya bamu sani ba”

“Allah kina wasa ko Aliyu ya bani haushi ba ka’dan ba ku tanbayi Faisal ku ji ma shi nace ya fita yace kada Aliyu ya sake zuwa qofar gidanmu”Halimah tayi maganar tana miqewa

Batul ta galla mata harara”kinga mu fa ba muda lokacin shiriritarnan taku,tun yaushe kike cewa Kun ‘bata Kuma azo a shirya mu tuno miki zancen kice baruwanmu,yanzu nagane ma ciwan so kikayi kwana biyu”

Halimah ta hararemu duka dukda ni ‘din bance wani abun ba”wallahi ku duka ku fita idona,Kuma ni zazzabi na tun kafin muyi fa’da nakeyi kada ma ku min wata fassara”

Da wannan muka fito waje Abbah ku’din mota shima ya bawa Batul ta bani godiya muka musu suna mu gaida su Abbah Abban Batul yace zaima kira Abbahnmu insha Allah,abinda muke gudu muka tarar munsha fa’da wajen Yaya Baffa ya fa’da wa su Halimah saidai ya basu ku’di su hawo wata napep su juyo gida shi ya makara ma yanzu,Ni dama nasan za’a rina indai Yaya Baffa ne,har cikin Tasha muka qarasa sai da na shiga mota na zauna Yaya Baffa ya biya ku’din motar kafin suka wuce badan naso ba sai dai ya zama dole na rabu da qawayena masu qaunata a dalilinsu na yarda akwai qawayen da sun zarce qawaye saidai akirasu ‘yan uwa sun dauki matsalata kamar tasu,abinda muka rasa daga ‘yan uwan mahaifinmu,da su yafi cancanta su kula damu da tarbiyyarmu,a hakan wata ‘yar kulawar saboda Abba ce akeyi mana ita kaina na qasa Ina zubda kwalla har motar mu ta ‘daga jin mun Fara tafiya nayi addu’a na cigaba da tunanin da nakeyi

<< Na Cancanta 19Na Cancanta 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×