Skip to content
Part 4 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Ina ‘ko’karin ‘karasa ajin su Rumaisa da mu mun gama Exam ta qualifying da muka zana chemistry ranar,zan je na fa’damata sa’kon da Mama ta bani na kaimata da Rumaisa ta rigani ta howa a yau

Malam Hamid na hango jikin birandar ajinsu Rumaisa da waya kunnensa da alama waya ya fito amsawa daga cikin Library ‘din da ya kasance gurin zamansa dako kiransa za’ayi aji anan ake samunsa,a yadda na fahimci Malam Hamid bai fiye son hayaniya ba duba da yadda ko yana koyarmana yakeyi

Bansan ya hango ni ba shima da ina ‘karasowa inda yake tun kafin na gaishesa ya faramin magana da yake ‘ko’karin cire wayar kunnensa

“Sumayyah”

Na amsa da

“Na’am Malam ina yini”

Ya dubeni

“Lafiya lau, ina zaki haka”

Nace

“Gurin ‘kanwata”

Malam Hamid mutum ne mai son ‘dalibansa musamman indai kana gane subject din da yake koyarwa hakan yasa muke mutunci sosai dan nidai inason physics sosai maganarsa ta katsemin tunanina don banyi k’o’karin tafiya ba har lokacin da bansan dalili ba

“Kin dai hanani number ‘dinki,kawayenki duk sun bani gashi saura kwanaki ya rage nabar Kano”

Kallonsa nayi don indai ban manta ba a ‘karshen shekararmu Ss1 yazo makarantarmu kuma gashi yanzu muna Ss2 karshen shekara

“Kina ta kallona ba zaki bani ba ko,to kimin kwatancen gidanku nazo”maganarsa ta katsemin tunanina na kuma sauke kaina daga kansa

“Ba hanaka nayi ba Malam ba nida waya ne,batun gidanmu kuma..”

Ban ‘karasa zancen ba yayi magana

“Ba a bari irina yazo ko?”

Murmushi nayi Jin kalamansa ta don ta ina talaka kamarni za’ace saika za’bi wanda zaizo gidanku ba tare da kana da dalili Mai karfi ba, dukda bawai nasan rayuwar Malam Hamid ba amma inada ya’kinin rayuwarsa tafi tamu inganci

“A’a Malam kawai dai naga ba’a Kano kakeba ba lallai ka gane kwatance naba”

Ya ‘dan zaro ido

“Waya fa’da miki ,ni ‘dan kanone ina gidan kakanninane a Katsina”

Na dubesa alamun na tabbatar ‘dinnan

Kai ya ‘dagamin alamun eh yace

“Anan ma unguwar Gandun Albasa Babana yana da gida amma gidan wani abokin Babana nake zaune tunda nazo shi a can Nasarawa GRA gidansa yake, kinga ko ni ‘dan gari ne”

Na dubesa nace

“Hakane amma dai yanzu mune ‘yan gari”

Ya harareni

“Bayan naji ance zuwa kuka yi ko daga ina kike gwarzo ko gwarzaye ne namanta Halima ce dai ta fa’damin”

Nayi murmushi

“Gwarzo ne”

“Ok yanzu ba zaki bani number ‘dinba kota Mamace”na dubesa

“Mama ba tada waya saidai ta Baba”

Yace

“A’a barta ma rin’ka gaisawa a wayar Halima”

Na ‘daga kai alamar eh ba wai dan nagaji da hira da Malam Hamid ba mu kayi sallama,bansan daliliba bana ta’ba gajiya da hirarsa duk lokacin da muka ha’du haka harso nake period ‘dinsa ta shigo jinina da Malam Hamid sai nace ya ha’du kasancewar Malam Hamid ya iya tsara zance, dalilin da yasa ba ko yaushe nakeson ha’duwata da shi ba musamman ba tare da su Halima ba fassarar ‘dalibai tuni a fassara maganar da muke a cewa muna soyayya ne da malamai sunyi dokar hakan a makaranta ko malami saurayin kane to ku bari ki fita can waje kuyi firarku idan yazo gidan ku,ajinsu Rumaisa na ‘karasa na fa’da mata sa’kon na fito da nayi sa’a na tarar ba malami

Batul da ta gama kufula na tarar da ita inda na barta da shaf na manta da batun wata Batul da nace tazo muje ta rakani fa’dawa Rumaisa sa’ko ta’ki tace min dai bari ta jirani anan na dawo mu tafi kasancewar tare muke tafiya da muna karasawa layin gidanmu take tsayawa ta samu napep hakurin da nakeso na bata ta katse zancena

“Kinga ba’abunda zaki cemin taho kawai mu tafi “

Bayanta nabi da ita har tayi gaba ina sauri har na ‘karasa gurinta muka cigaba da tafiya da shiru ya ratsa tsakaninmu

“Yi hakuri mana ‘kawata”

Batul ta dubeni da hararata

“Ba wani ha’kuri kina can kin samu Malam Hamid,banmasan wacce tattaunawar kuke ba”

Na kalleta

“Wai dama kina hango mu”

Ta ‘daga kai

“Eh man da nayi niyyar zuwa to saina hango ana kallon love shine naki zuwa”

Wata muguwar harara na gallawa Batul

“Banasan wula’kanci Batul,wanne irin kallon love”

Dariya tayi

“Nufinki ba musan komai ba,nifa nasan danke Malam Hamid ke kirana waya,tunda kullum in yana kirani tanbayarki kawai yake”

Na ‘dan ja tsaki

“Wannan matsalarkice ni soyayya ma bata dame ni ba,bare kuma har nayi da malaminmu”

“Kanki ake ji mudai ‘yan kai amarya ne Katsina dama ban ta’ba zuwa ba”fa’din Batul tana dariyar sha’kiyanci da nasan halin Batul bama ka mata komai ba tana zolayarka bare na ‘batamata rai amma baisa na ‘ki tankamata ba

na sake ha’de fuska

“Batul bansan irin wannan,ke kanki kinsan tsarin mijin da nakeso Malam Hamid bai kala da su ba kuma ma kinsan bana sha’awa soyayya da malami nasha fa’damiki ina gudun kar wasu su ji su Kama”

“To sai me dan sunji aibu ne hakan,ko harammunne kika aikata,kuma batun kala aike ma kinsan Malam Hamid komai ajin budurwa bazatace ta girmi  Hamid a wanda zata so ba”ta karasa zancen tana gyara littafan dake rungume hannunta

Cikin ‘bacin rai

“To ke mai zai hana ki sosa”

Ta sa dariya

“Ai dan bani ya nuna yana so ba”

Shirun da taji na mata yasata sassauta murya

“Gaskiya Sumayyah wannan ba tsari bane bansan kalar mijin da zaki ce yayi miki ba,Yaya Hakeem da yake tamkar yayanmu shima kin nuna bai miki ba da ya nuna yana sanki,haba Habiba bansan wanne kalar miji kikeson aure ba,tunda kinada tabbacin ba cigaba zaki yi da karatu ba ya kamata ki aje komai ki za’bi miji kiyi aure tunda kina samun maneman,sai dai kuma bansani ba ko maikudi kike jira”

Batul na kalla da badai abin haushi ba ana fara magana tiryen tiryen zata bau’de
“Batul bana tunanin Malam Hamid da Yaya Hakeem tafiyarmu zata daidaita badan nasan asalin Hamid ba amma nasan na Yaya Hakeem ,kuma kema sanin kanki ne ban ta’ba tsammanin zan samu dacen auren mai ku’dinba,amma darajata nakeso bayan aurena”

Batul ce taja ta tsaya da nima banida za’bi banda tsayawar

“Wacce daraja ce da idan baki tunanin zaki samu gurin Malam Hamid ba kike tunanin ba zaki samu gurin Yaya Hakeem yayan Halimanki da kowa ya shaida kaunar da take miki da ita da nata iyayen dama duka ‘yan uwanta,da kowa ma shaidane kedai kawai kice baki son Yaya Hakeem ‘din”

Nayi murmushi dan gaskiyane Batul ta fa’da kawai bana sha’awar auren Yaya Hakeem da ko Batul bata san daliliba bayan Halima da itace tayi ‘ko’karin ha’dani da Yaya Hakeem kawai don ta nuna soyayyarta gare ni,dukda ‘kawance tunna yarinta har zuwa yanzu ya ha’da Halima da Firdausi budurwar Yaya Hakeem da suke son junansu amma tayi ‘ko’karin canza akalar soyayyarsu take ‘ko’karin azata akaina,shima Yaya Hakeem don ya farantawa Halima yake ‘ko’karin biye mata,da akan hakan muka fara ‘ko’karin kai ruwa rana da Halima da har yanzu bamu dawo daidai ba,don na fa’dawa Halima ba za’a ha’da baki dani gurin cin amanar Firdausi ba da take nima ‘kawa gareni saboda dalilin Halima na daban nasan kawoni cikin danginsu…

Maganar Batul ta katsemin tunanin da nake

“Shikenan tunda kin’ki don Allah ki amince da Malam Hamid yanzu”

Nayi tsaki na cigaba da tafiya Batul badai matsala ba sam bata gane karatun kurma,kamar na fa’damata aurenne a gaba na kome ma oho toma auren ma ai daidai ruwa daidai ‘kurji dan ko da gani ma ido ba mudu ba yasan kima ina zan ha’da kaina da Malam Hamid dukda bansan asalinshi ba  na lura dalilin hakan,inajin kiran da Batul keyimin na shareta na cigaba da tafiya cikin sauri harna ‘karasa layin gidanmu na shige kwanar gidan namu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Cancanta 3Na Cancanta 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×