Skip to content
Part 5 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Waya baba ya mi’komin da nake zaune ina wanke wanke a  tsakar gidanmu kar’ba nayi da ina duba wa naga alamun an Kira wayarne ina  ‘ko’karin tanbaya waye Baban yace

“Kiyi magana ‘dan uwanki ne Samir,ki kawon wayar idan kin gama ‘daki”
Nayi murmushi dana ‘ka’karosa  don tuni na gano wannan Samir ‘din ne mai tanbayarnan nace ma Abba

“To”

Nayi ‘kokarin kara wayar a kunnena

“‘kanwata ya kike.”

Maganarsa ta katse tunanina na maida hankalina ga wayar

Ban basa amsa ba na canza zancen

“Yaya Samir ina yini”

“Lafiya lau yasu Mama”hakan da ya fa’da na ayyana a raina Allah yasa kar tanbayar ta zarce

“Lafiya lau ya kowa da kowa”

Yace min

“Alhamdulillah”daganan shirun ‘yan sakanni ya rasa tsakaninmu Samir yayi ‘kokarin sauke numfashi.

“Hala tsoron mutane kike ko?”

Na tsaro ido kamar yana ganina

“Ni ‘din kuma?”

“Eh mana ina kallon yanayinki wancen karan saboda tsoro haka kika tafi bamu gama gaisawa ba”

Nayi murmushi kamar yana ganina

“Kai Yaya Samir banda gaisawar da mukayi

“Ina wata gaisawa bayan tanbayata tasa kin gudu”

Nayi dariya nace

“Waya fa’dama saboda tanbayarka na gudu”

“Saboda nasan hakanne ,dan haka nake duk inda naje don duk na fara manta mutane tunda na dawo daga karatu kinsan ba anan ‘kasar nayi ba,ko ‘yan Gwarzo saida suka yi zancen tanbayartawa,to bare ke da mukayi nesa da juna,yaushe zaki zo Katsina?”ya ‘karasa maganar yana tanbayata

“Babu rana”

“Ah haba dai idan kun gama qualifying zan zo na tafi dake?”jim nayi jin abinda Yaya Samir ya fa’da sai da ya sake magana

“Ko bakya son kizo gidanmu,bayan kuma yanzu muka gama magana da Abba ya ce min saina zo”

Bani da za’bi jin Abba ya amince sama da nima na amince
“To shikenan Allah ya kaimu lafiya”

Yace

“Amin amma yaushe zaku gama qualifying ‘din”

Kamar bazan basa amsaba

“On 20”

“Ok zan zo On 25 sannan kin shirya komai ko?”

Shiru nayi Masa

“Shikenan tunda bazaki magana ba na lura har yau baki gama sabawa dani ba”ban basa amsa ba.

“Sai anjima”kawai na fa’da na katse wayar na kaiwa Abba wayarsa na dawo na cigaba da wanke wanke na a raina ina tunanin ko wanne zama zanyi gidan Baban Katsina muna nesa da juna basu taimaka mana bare kuma naje inda suke na ‘dora musu nauyi, inada ya’kinin Baban Katsina baisan da zancen zuwana ba kawai Yaya Samir ya shirya zancen zuwan nawa,amma dai a yadda nasan babu mai sonmu a dangin Abba babu wanda zai bu’kaci muje inda yake hakanan ba tare da wani daliliba da nima nasan dalilin Yaya Samir dana fahimci yanasan zumunci zanje haka na karasa aikin da nake jikina a sanyaye ‘dakinmu kawai na shige na kwanta ina tuno wayata da Yaya Samir bansan dalili ba tun bayan gama wayarmu naji hankalina bai kwanta da zuwana Katsinan ba.

Sallamar Halima ta katsemin tunanin da nakeyi da sai yanzu nasan tazo gidannamu amsa mata, nayi gefen tabarmar da nake kwance ta zauna  tare da cewa

“Hala dai lafiyarki ‘kalau kizo kika kwanta haka ke ka’dai.”

Nayi murmushi

“Bakomai,nayi aikine na gaji”

Hararata tayi tace

“Wanne irin gajiya,yanzu Mama ta fa’damin kika shiga ‘daki bayan kin gama wanke wanke,dan Allah ki fa’damin damuwarki”

Na ‘dan ja numfashi Halima ba ‘kawar da za’a ‘boyewa wani abu bace don tafi ‘karfin a kirata koda aminiya saidai ‘yar uwa na dubeta na fara magana

“Halima ‘dazu Yaya Samir ‘dan Baban Katsina yayan Abba ya kirani waya a wayar Abba akan cewa mana gama  qualifying zaizo ya ‘daukeni mu tafi Katsina,shine hankalina ya kasa kwanciya”

Halima ta zaro ido tace

“Katsina fa nidai bana yi miki sha’awar zuwa  dacen da kuke ‘kananu waya ta’ba tunanin ya ‘dauki wata cikinku sai yanzu da kuka fara girma,dama zaman bauta ka’dai zakiyi da sauki amma wulakancin da zai rika biyo baya nake gudarmiki da za’a ri’ka shimfida miki, shi Yaya Samir ‘dinma akanme zai tunanin hakan.”

Na girgiza kai nace

“Wallahi bansaniba Halima amma shi baisan duk abinda ke faruwa ba,ta yiyuma Baban Katsinan baisan abunda Yaya Samir ‘din yayi ba”

Halima ta ‘daga kai tace

“Eh hakane amma dai Mama ya kamata tayi magana akan bazaki ba”

Na dubi Halima nace

“Halima Mama fa tayi magana kikace to ai tanayi abun zai zama abun magana ,dama ita da hakannan ma ba tsira tayi ba a gurinsu,Kuma Abba fa ya amince”

Tsaki Halima tayi daga bisani tace

“Allah ya kyauta zance kawai don nidai nasan ba wani farin ciki zaki acanba dan da zaman da zakiyi acan wallahi gwara na nan ko ba kullum zaku ci ba”

Da haka muka cigaba da fira da Halima da muna cikin firar wayar tayi ‘kara da wayar dukda  keypad ce ta bani sha’awa saboda ni ko kamarta bani da ita da itama yayanta Yaya Baffa ya bata tsohuwar tashi daya canza sabuwa duba wayar ta kalleni tayi murmushi tana ‘kokarin ‘dagawa tace min “Malam Hamid ne ‘dazu ma ya kirani waya,yana tanbayata naje gidanku nace masa a’a zanzo dai anjima shine kinga yanzu ya sake kirana.”

Daganan ta ‘daga wayar Sallamar da tayi a wayar naji daganan naji tace “to” ta mi’komin wayar

Na kar’ba kawai na kara kunne ba tare da nace komai ba Malam Hamid naji yafara magana cikin muryar da banmasan ya iya irinta ba tunda banta’ba ji yayi ba kamar mai jin barci yace.

“Sumayyahty babu magana”

Jin sunan nayi banbarakwai nanma dan nasa ba da Sumayyahty yake fa’damin shiru nayi don bansan amsar da zan bashi ba,shirun da yaji nayi ya cigaba da cewa

“Nayi laifine”

Kaina girgiza kamar yana ganina na ce

“A’a”

Ya ‘dan marairaice murya

“To mai nayi”

“Ka canza”kawai na iya fa’da

“Dame kuma”ya bani amsa

Nace”da komai”

Ya ‘danyi ‘yar dariya da naji sautinta a waya yace

“Kin bani dama na sanardake dalilin canzawartawa”

Nace masa”Eh”

Sai kawai naji yace

“To kece sila”

Zaro ido nayi kamar yana ganina tare da cewa

“Ni kuma saboda wanne dalili Malam”

“Dalilin inasanki,tun farkon ganina dake Sumayyah  naji hakan da a yanzu nafi tunanin lokacin sanarmiki yayi….”

Ba tare da na ‘karasa jin mai zai fa’daba na katse wayar hawaye suna wanke min fuskata da bansan da taruwarsuba saidai zubarsu kawai

Halima ta dubeni bayan mi’ka mata wayar da nayi da duk abinda nake fa’da tana ji
“Lafiya Sumayyah  mai yafa’damiki Malam Hamid din”

Hawaye na na cigaba da zubarwa na dubeta

“Halima so na yace yanayi,bazan iya ha’da rayuwata da mutum kamar Malam Hamid ba”

Kallona tayi cikin nuna danuwa

“To saboda ance ana sonki kike hawaye,to sai dawa zaki iya soyayyar,gaskiya Sumayyah  ki tsaya ki nutsu kima kanki fa’da haba,dan ance ana sonka ba’abun gwama numfashi bane,so dai game hankali ga wanda ya nuna yana sanshi ai shi akeso,babu ala’ka tsakaninmu amma buri na kiyi aure”

Na girgiza kai

“Eh nasani amma Halima ke kanki kinsan kina kallon Hamid kinsan rayuwarsa tafi tawa koma da ya ne,ni Kuma na fison auren wanda rayuwarmu tayi dai dai da juna”

Tsaki Halima tayi

“Wannan ba hujja bace kwata kwata,kuma banga aibun Malam Hamid,bare kuma naga wani alamu na da zai nuna Malam Hamid yafiki ba,ki tsaya ki nutsu ki fahimci hakan dai tukun”

Murmushi nayi da bani da za’bi da ya wuce yadda amma dai ni haka zuciyata tafi tunani ni kuma nafison auren wanda rayuwarmu tayi dai dai da juna

“Shikenan na amince to”

Dariya tayi

“To ai bani zaki fa’dawa ba,kuma baki shawara da zuciyarki ba ta ina zaki amince masa”
Nima dariya nayi nace

“Aike radiyonsace,kuma kamar zuciyace ke a gurina,ke kin mafi zuciya saboda zuciya ba lallai duk abinda ta tsakani na aiwatar ya zama daidai ba,amma ke zuciyace mara sirki da duk wani abun da zai jawo aikata da nasani,dan haka shawararki itace abar ‘dauka,danko Mama itama nasan hakan zata fadamin”

Murmushi tayi

“Wato kin janye min ko?”

Nayi dariya

“Ai dole a janye wa ‘kawar kwarai da kowa ke fatan samu a rayuwarsa,ke na fa’damiki ko aminiya na fa’damiki sunan baidace da keba”

Kai Halima ta girgiza

“Sumayyah  banison yabofa,komai nayi miki cancantarki ce hakan”

Na dubeta

“Cancanta fa kika ce”

Ta ‘dagamin kai

“Kwarai kuwa, Sumayyah kinada halin da kowa zaiso zama dake,ya kuma ‘karar da komai gurin don son zama dake,kina da juriya,tare da sanin darajar wanda duk kike tare dashi”

Dariya nayi

“Idan harna kasance hakan to kece sanadiyyar zamo wata haka,Halima da ace zan rubuta littafi akanki littafi ‘daya yayi ka’dan gurin bayyanarwa da jama’a halayyarki,halinki ya girmema kyawunki da shekarunki,kin tallafamin a lokacin da kowa ya nuna bayason mu hatta a dangi kinyi tarayya dani bisa tsantsar ‘kauna da gani har zuriyyata kuma kin zauna dani bayan kin fahimci mu talakawane da kullum suke neman abinci yau da gobe,kikan iya ‘kin ci ki bani ni naci,duk abinda kike dashi nawane ni dake,Halima bansan ta ina zan biya ki ba”

Murmushi tayi

” Ai Sumayyah ‘kawa ta gari ba dubawarta abinda kika mallaka bane dubawarta cancantarki ya ‘dabi’unki suke kyawawane ko kuwa,shin kina umarni da kyakkyawa ko kuwa,kuma yaya soyayyarki da duniya take,kina tuna Allah a dukkan lamuranki,ni a nawa tunanin sune abin dubawa bawai arzi’ki ba domin su ababene masu ‘karewa,a lokacin da akace ba zakayi ‘kawance da wadda ka fita wani abu a duniya ba  to ta ina zaka fahimci ta inane zaka tallafi rayuwar wasu kuma  idan kace sai da wa’danda suka fika  zakayi mu’amala ta ina zaka san kanada wani matsayi a gurin wasu,idan baka mu’amala da wa’danda kafi su wani abu ba bama zaka fahimci Allah yayi ma baiwar da wasu ba su samu irinta ba kullum tunaninka yadda zakayi kakai gurin da wa’danda suka fikan suka kai shikenan sai ka fara rashin godiyar Allah ni a ganina kayi Mu’amala da kowa ta yadda tsoron Allahnka zai ri’ka ‘karuwa malam mai ahalari yana cewa idan zaka so mutum ka soshi domin Allah,kuma dukkan musulmine ai ‘dan uwan musulmine”

Na jinjina kai alamun gamsuwa

“Amma Halima ‘yan uwana sun kasa fahimtar abinda ke ‘din kika fahimta”

Kafa’data ta dafa

“Yi hakuri Sumayyah zasu fahimtane wata rana,domin talaka da ace an tanbayesa Yaya yakeso ya rayu a duniya da bazaice yanaso yayi rayuwa cikin talauci ba,kuma arzi’ki nufin Allah ne idan zagayenka yazo zaka iya samu idan Allah ya ‘kaddara zaka samu,shiyasa kullum addu’ar da yakamata mu ri’kayi idan Allah baisa zamu samu shiga wata ni’imaba a duniya Allah ya bamu dacewa ta shiga cikin ni’imar aljannah,a wannan duniyar idan akace talaka bai kyautata bautarsa ga ubangiji ba bana tunanin zai samu hakan”

Jinjina kai kawai nayi alamun ina gamsuwa da maganganun Halima.

<< Na Cancanta 4Na Cancanta 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×