Skip to content
Part 6 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Yau muke zana jarabawar Physics da ta kasance ƙarshen jarrabawar qualifying ɗin da muke hakan yasa ta wani fannin muna farin ciki wani fannin akasin hakan muna zullumi domin a ɗayan biyu muke kodai mu samu komu faɗi dani sai nace namafi kowa zullumi domin Wanda yake neman abincin yau da gobe ina zai nemo dubu 13 na biyan kudin neco ko wa’ec da indai baka ci ba saika biya,gwarama idan kana da English ko math Koda baka cinba daga baya gwamnati na biya ma idan na tuno hakan nakan ji damuwa sosai a raina amma dukda hakan nabarwa Allah komai kuma kullum cikin addu’a nakeyi bawai ni ka’daiba har Mama da Abba addu’arsu kenan kullum gareni.

Fitowarmu daga exam ‘din kenan naci Karo da Malam Hamid a bakin class ‘din namu da kayansu na bautar ‘kasa da tun bayan wayarmu bansake ganinsaba dan banama fatan nagansa yau ‘dinma ba hakan nasoba saboda nidai ba gwana bace a fannin so bare harna tattaro kalmomin da zasu dace da amsar dazan basa,dukda zuciyata ta gama amincewa da Malam Hamid, saboda baida wata makusa tako wacce fuska, murmushi ya sakarmin tun kafin na matsa kusa da shi da ina ha’de ‘kafa na ‘karasa dan kallon da yake jifana dashi gaba ‘daya ya fara kokarin rikitani,inda yaken na ‘karasa da sallamata amsa munyi yayi tare da sakarmin kallo Daya sakani jin kunyarsa hakan yasa nayi ‘kasa da kaina inamai gaishesa amsamin yayi tare da fa’din,

“Kunyata kikeji kenan maza ,’kawayenki suzo su fassara.”

Hakan da ya fa’da yasa saurin ‘dago da kai.

“Malam Hamid fassara ta mene.”

Ya ‘dan lumshe ido ya bu’de ya cigaba da kallona.

“Na alamun muna soyayya,bayan kuma kin hana hakan”kallensa nayi nima ni ya kalla ‘daga kansa yayi”baki yarda ba ko?,Habiba bazan ‘boye miki ba inasonki son da bazai it’s misalta miki kalarsa ba ko nuna miki shi saidai na kwatanta miki rashin  amsarki gareni ya karyarmin da zuciya,ko dai inada wani aibu ne?”

Ni zancensa ma dariya ya bani yadda yayi maganar tasa na dai daure na saki murmushi.

“A’a Malam na amince,tun lokacin.”

Ya kalleni gami da hararata.

“Shine kika dinga bani wahala ko,toma dame Kika amince.”

Na dubesa ina k’o’karin basa amsa su Halima suka karaso inda muke tsaye sallama su kayi mana muka amsa musu cikin ha’da baki.

“Malam Hamid ina yini,ashe kai ka ‘boyeta muna fitowa exam muka fara nemanta”suka ha’da baki gurin fa’din hakan.

Murmushi yayi yace,

“Lafiya kalau,a’a ku tanbayeta dai inda ta tsaya nima yanzu muka tsaya.”

Kallonsa nayi ba tare da nace komai ba,nima ni ya kalla”wannan kallo haka na fara karya ko kike nufi?”

Halima ta dubesa “kai malam Hamid yaushe ta kalleka kuma”ya ‘dan rausayar dakai yace”karfa kicemin baki ga kallon tuhumar da tayimin ba,ko kuma shigar mata zaki “
Halima tayi murmushi “a’a fa,Kuma koda ma na shigar mata ai banyi aibu ba kasan ruhina nace.”

Dariya yayi” kamar gaske.”

Batul ta dubesa da sai yanzu ta saka baki”gasken gaske kuwa Malam ai ruhinmu ‘daya ne?”

Nidai tunda suka fara maganar da murmushi nake binsu inajin su a raina sosai Halima da Batul musamman Haliman ma.

Muryarsa ta katse tunanina”shikenan to dama yau nake saka ran komawa gida, saina barku da ‘kawartaku tunda kun nunamin kunfi sonta akaina.”

Kai na ‘dago na kallesa bayan ya ‘karasa maganar.

Halima ce tayi saurin yin magana”malam Hamid yau fa?،,ka bari zuwa gobe mana,zaka yi daren hanya”Batul itama tace “sosai kuwa zaka iya kaiwa sallar isha’i ga ‘kasar ba tsaro sosai.”

Murmushi yayi”har fa na shirya komai.”

Kallonsa nayi cikin marairaicewa nace”Dan Allah kayi ha’kurin safiyar kaji?”wani mayataccen kallo ya bini dashi ya kuma sauke idanunsa saman nawa ba zan jure ha’da kwayar ido dashi ba hakan yasa nayi saurin janye idanuna”akanme zan bari zuwa safiya bayan wadda nake zaune dan ita batasan ina wannan ba” yayi maganar yana dubansu Batul alamun yana Jin haushina shiyasa ko amsar tambayata bai bani ba,dukda nasan Malam Hamid ya damu dani amma nidai nasan badanni yake zaune a Kano ba saboda bautar ‘kasarsa yakeyi kawai tsarin kalamaine irin na ‘da namiji da yadda matan suka iya suma sun iyasu maganar Halima naji cikin tunanin da nake

“Waya fa’dama bata damu dakai ba,ai saboda damuwarma malam na fa’dama garinku zata taho a satinnan.”

Ina kallon yadda fuskarsa ta cika da annuri ya dubi Batul”hakane Batul?”

Kai Batul ta ‘daga masa tare da cewa”eh hakane zata tafi gidan yayan Abbansu.”

Halima ta kallesa tace”au da baka yarda da maganata ba, shikenan na daina baka labari game da Sumayyahn.”

Daganan taja Batul ‘ki Batul ta juyo ta kalleni”muna jiranki” na bita da “to” da ba lallai ta ji ba saboda yadda Halima ta ke janta Halima badai iya fushi ba Kuma ita fushinta akan abinda baikai ya kawo bama take abinta amma dai daka fahimci halin Haliman shikenan tanada da’din zama

Suna barin gurin ya juyo da kallonsa gareni”Halima dama fushi gareta haka”

Dariya maganarsa ta bani na dai kunshe ta nayi murmushi nace”sosai kuwa,amma fa mara anfani tunda batasan akan abinda zatayi fishin ba.”

Shima murmushi yayi”hakane,da gaske Katsinan zaki tafi.”

Na daure dan kawar da damuwar data riskeni da ya tunomin zancen tafiyata Katsinan nan da kwana biyar dan karya fahimci inada matsala da dangin nawa nace”Eh gidan yayan Abbanmu zani,acan yake da zama da aiki.”

“Alhamdulillah ,ashe bazan yi nisan da nake tunanin zanyi da Sumayyana ba da tuno hakan yakan sani zullumi,wacce unguwar suke a katsinan?”ya karasa fa’din hakan yana kallona.

Nace”a layout suke”a raina ina ganin zancen da Malam Hamid yake fa’da game da soyayyata kamar zancensa ne kawai domin dai duka kwanansa nawa da fa’damin yana son nawa,sai dai tunowa da ubangiji yakan iya komai a lokacin da yaso hakan yasa na cirewa raina soyayyar malam Hamid ‘din ‘karya ce na yarda gaskiya ce
Kamar yasan tunanina na tsinkayi muryarsa Yana cewa,

“Alhamdulillah, Sumayya nasan zakiyi tunanin soyayyar da nake miki tamkar karyace,amma na da’de da fara sonki,tun farkon kallona dake.”

Murmushi nayi dan gaba ‘daya a tsoroce nake ina tsoron wani malamin yazo wucewa yaji kalmar so tana fitowa a bakin Malam Hamid d’in gareni.

Kamar yasan tunanin da nake a karo na biyu yace”kin amince anjima zanzo gidanku,dan naga anan kamar a tsorace kike.”

Kai na ‘daga alamun amincewa ba tare da na tsaya yi masa sallama ba nabar gurin,Inna tunanin ya zaiyi yazo gidanmu bayan bai sani ba tunowa da Halima da Batul da nayi suna waya na sallama zancen a raina.

A tsakiyar makaranta naci karo dasu sun tsaya da Malam Mukhtar malamin English ‘dinmu,dan su Halima badai magana da malamiba da nima nabi bayansu,saboda abotarmu tasa kusan komai namu iri ‘daya nee,sainace a malamanmu ka’danne basu san sunanmu ba amma dai sani a fuska dai sunyi mana dukda badai a batun rashin ji ba a dalilin monitor data kasance Batul yawanci anan mukayi sanayya, Malam Mukhtar ‘din na gaisar daganan muka fice a makarantar muna firarmu.

Halima tace “Batul kinsan me yau gidansu Sumayyah  zanje?”

Batul tace”yanzu,ko anjima,mai zakiyo?”

Halima tayi ‘yar dariya “zanje sanar da Mama soyayyar da Sumayyah takeyi da Malam Hamid,Kinga sai ta fara shiri da wuri”

Dariya Batul tayi tace”hakane kuwa Halima kin kawo magana mai girman gaske.”

Tsaki nayi tare da cewa”Allah ya shiryi ‘dan iskan mutum.”

Batul tayi saurin cewa”ni ko Halima.”

Nace”Wanda ya tsargu,banda iskanci ku da kuke soyayyar na ta’ba cewa zanzo gida nasanar dasu Mamanku.”

Dariya ‘kasa ‘kasa Halima tayi tace”wato dai nice ‘yar iskar,kema kuma guguwa,kuma ai ni kinsan ba wanda baisan Aliyu a gidanmu ba ko yaron goye yasanshi.”

Tsaki nayi”ba dole a sanshi ba an nace saurayi ‘daya kamar mayya.”

“Ai anan darajar take idan Allah yayi Aliyun ba mijinta bane,bayan rabuwarsu sai kiga ta samu mafiyinsa,amma tara samari ai baida da’di.”

Jinjina kai nayi”amma dai ai baka ce namiji ‘daya zaka kula kamar autan maza.”

Halima ta buga tsaki”please Sumayyah ki ajiye kalamanki bawai dan bazasumin tasiri ba idan naji su ba,amma dai kawai ba zasumin tasiri ba dan na da’de ina jinsu,amma ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci waye Aliyu.”

Jinjina kai nayi a raina ina tunanin maganar Halima.

Note: Wasu zasu ce ko sun ta’ba ganin littafin continuation ne kawai anyi editing ne wani ‘bangaren.

<< Na Cancanta 5Na Cancanta 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×