Skip to content
Part 8 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Ana kiran sallar Azahar na farka daga barcin da bansan ya ‘daukeni ba, da ambaton Allah na bu’de idona gami da ‘dora idona tar a fuskar Halima da ta zuba tagumi hannu biyu tana kallona wanda nasan ba kallona take ba tunda har bata ji motsina ba,da Kuma maganar da nayi, tsabar tunani ta fa’da da nasan Halima akwai zurfin ciki, da kuma nuna damuwarta ga al’amarin kowa musamman al’amarin abinda take so,ta yiyu nice sillar taguminta ko dai wani abu daban, motsin da na qarayi yasa Halima a zabure ta kalleni.

“Sumayyah har kin tashi.”

Murmushi nayi Halima ba dai tsoro ba abu ka’dan zaka yi ka firgitata,ita ko fa’dama tsoro yake bata sai dai fa akwaita da fushi,ban bata amsa ba na dubeta.

“Halima yaushe Kika zo ne?”

Kallonnata tayi ta kuma canza magana.

“Kinga Sumayya ba batun zuwa na ba ki tashi ga abinci na kawo miki duk da nasan ba muradinki bane shinkafa da miya ne, dan Allah karkice bazaki ci ba, nasan da qyar idan kinci abinci kika kwanta,Habiba kina wasa da cikinki ina jiye miki ulcer ta kamaki.”

Ta qarasa zancen da alamun tsoro.

Banyi mamakin abincin da Halima ta kawanba da idan aka bibiyama shine dalilin zuwanta gidanmu da wuri haka gidannamu dan kuwa Halima macace mai kyautatawa duk wanda yake tare da ita,na rasa kulawar dangi amma na samu ta qawa,lallai Allah abin godiyane a kowanne hali bawansa ya shiga yakan  kawo masa mafita,domin shine ya kawo min Halima a lokacin da na rasa kulawar dangina,bama ni ka’dai ya kawowa ba hatta ‘yan uwana da iyayena duk ya kawo mana ita.

Maganar Halima ta katseni.

“Sumayyah dan Allah ki tashi kici abincinnan karya wuce,kular bata wani riqe zafi.”

Murmushi nayi na miqe da cewa,

“Bari na wanko hannuna da baki.”

Daganan na miqe na fice daga ‘dakin da Mama naci karo tsakar gida ta kalleni
“Hala yanzu Kika tashi wato Haliman bata ta shekinba da nace tana zuwa ta tasheki.”

Murmushi nayi na ce,

“Mama kema dai kinsan Halima bazata iya tashina ba, yanzu ma abinci tazo min dashi, ina tashi ta matsamin nazo na ci.”

Mama ta girgiza kai ta kalleni.

“Sumayyah bansan yazan misalta qaunar da Halima ke miki ba da har muma ta shafemu, dukda Suma ba want qarfi garesu ba amma duk sanda ta samu saita tunkaroki, ta fahimci rayuwar da muke ciki fiye da danginmu, da su suka kasa fahimta,bansan da me zamu iya biyan Halima ba,sai dai kawai Allah ya biyata.”

Na ‘daga kai na ce

“Kwarai kuwa Mama dan yanzuma ta yiyu ko abinci bata ci ba ta tawo kawomin, saboda ta lura da wuya naci abinci na tafi makaranta da safe, nasan zai wuya ba haka za ta ce ba.”

Mama ta ce,

“Sai kije kuci tare, karki shiga haqqinta da yawa, Halima akwai lura sosai, rayuwarta mai burgewa ce.”

Na ce,

“Hakane Mama.”

Daganan na qarasa gefen banbum ruwanmu na ‘dauki buta na wanki hannu muka da baki na koma ‘dakin da sallamata,Halima ta amsamin na zauna kusa da ita da harta bu’de kular da qamshin miyar keta ta tashi kamar ansa kifi ciki,har zan fara ci,na dubi Haliman

“Kisa hannu muci Mana,inada tabbacin baki ci abinci ba kika taho kawomin”

Halima ta dubeni.

“To fara ci ki ragemin,dan Allah karki sake magana kici abincinki kawai.”

Bansake maganarba kamar yadda, Halima ta buqata na fara cin dadda’dan girki,da tunda Halima ta bu’de nasan zaiyi da’di saboda qamshinsa da tun kafin na fara ci na ha’diyi yawu,sai da naci na qoshi na ragewa Halim ta wanko hannu ta fara cin abincin da a lokacin qannena ‘yan makaranta sun dawo,Ahmad da Rumaisa da Sadiq da Khadija da suka shigo a tare,kamar sun ha’da baki,Mama naji suna tanbaya abinci,sai dai ban sake jin mai Maman tace musu ba naji sunyi shiru da ‘dai da ‘dai suka riqa shigowa ‘dakinmu suna gaida Halima suna kwasar kayansu suna fita da Ahmad a kofar ‘daki ya tsaya suka gaisa yayi gaba saboda shi ganinsa yake babba kayan sa ma Rumaisa ta ‘daukarmasa dan kayansa duk suna ‘dakinmu kwana ne dai a zaure yakeyi,da idan ana ruwa sai dai yaje shagon da wani makwabcinmu ‘ya’yensa ke kwana ya ra’ba ya kwanta,saboda yadda kwanon zauren gidannamu ke shata ta kamar me.

“Yanzu Sumayyah kin kyauta kinwa mutumin alkawari zaku ha’du yau amma ki cemin gidan Mama Atika zan rakaki,da nasan da haka wallahi da tuni nayi tafiyata,wannan ai abin haushine,kamar wadda bata zuwa islamiyya kice zaki sa’ba alkawari”

Na rausayar da kaina jin Halima ta Gama sababinta

“Dan Allah Halima karki ce komai a kaina kimin uzuri Mamace tace lallai sai naje Kena kinsan ba san zuwa nake ba”

“Duk da haka gaskiya banji da’di ba,da tun zuwana kin fa’damin inada tabbacin da tuni mun dawo,yanzu gashi uku harta gota,yaushe har muka je muka dawo”

Na ce

“Oh Halima kenan,ke ‘dinfa badai mita ba.”

Hijabinta ta ‘dauka ta miqe tana cewa

“Idan kin gama zancenki saiki biyoni”

Tsaki naja mata na miqe nima ina cewa

“Kiji rainin wayau irin naki waye mai zancen idan ba ke ba,kin isheni da mitarki”

Tana qoqarin barin ‘dakin ta ce

“Mita ta akan gaskiya take”

Nayi murmushi jin zancen Halima wato ita dai akan Malam Hamid zata iya fa’da dani kaina,bayanta nabi ina saka hijabina da yaketa kyallin guga a kofar ‘daki naci Karo da Halima muka qarasa ‘dakin Mama ta bamu ku’din napep da jaddada mana mu gaida Mama Atika ta Kuma bimu da addu’a muna amsawa da Amin har muka bar cikin gidan da addu’ar fita gida a bakina.

Bamu wani ‘bata lokaci bakin titi ba muka samu napep na fa’damasa unguwar da zamu mukayi sa’a zaije Nnasarawar,daalima tunda muka fito gida har muka shiga napep ‘din bata furtamin komai ba tanajin haushina

Na dubeta nace

“Amini nayi laifi ne,tunda muka baro gida baki sakemin magana ba.”

Tsaki tayi.

“Dan Allah Sumayyah ki kyaleni da Aminin munafurcinki,gaba ‘daya yau haushi kin riga kin gama bani,bawan Allahn nan Hamid yana sonki amma ke ‘din kina nuna baki sonsa,kina nuna masa ko in kula,saboda ke fa yaqi tafiya jiya.”

Wani tsaki nima nayi.

“To ni banison shi kenan kike nufi ko ya ya.”

Ta kalleni.

“Allah masani,ina zan sani,wannan sai zuciyarki.”

Bata qarasa fa’dar zancenta ba wayarta tayi qara tasa hannu aljihun doguwar rigarta ta ‘dauka tana kallon wayar kafin ta maida kallon ta gare ni tana miqomin wayar.

“ungo malam Hamid ne.”

Na kalleta nima nii ta kalla

“Ki amsa mana kada ta katse,ki san mai zaki fa’da masa” ta qarasa zancen tana miqomin wayar,haka na amsa da tunani da yawa a raina sallamar da yayi na amsa inaji sanda yayi ajiyar zuciya kafin ya cigaba

“Sumayyah ce ko?”

“Eh nice ina yini”

“Lafiya Lau,da fatan kin shirya zuwa na yau ko dan harna fito gida”Jin maganarsa da ya fa’da yasa ni yin shiru sai da ya sake magana

“Baki jina ne”

Na ‘dan daure na ce

“A’a naji amma kaya haquri,ina komawa gida Mama ta aikemu ni da Halima,kaya haquri”

Shiru yayi a wayar ba tare da ya bani amsa ba sai bayan wasu sakanni

“Shikenan Sumayya na fahimta ba laifin ki bane,amma naso ganinki a yau,wani unguwa aka aikeku?”

Na ‘danyi jim kafin na ce

“Nasarawa GRA”

“Oh God unguwar da nake zaune bara na dawo yanzu, amma yimin kwatancen layin da gidan da zaku”

Shiru nayi ina zullumi,ni ‘din daba wata bace a gidan ina ni ina kwatancen gidan Mama Atika,ni ‘din ni ka’dai ba tarbar arziqi nake samu ba daga gurin ‘ya’yan gidan bare naje da saurayi,maganarsa da tamin amsa kuwwa a kunne ta dawo dani tunani

“Ko baki ji ne?”

Na daure na ce

“A’a na jika,kawai dai bazan iya kwatancen gidan bane”

Ba tare da naji mai zai fa’da ba wayar tayi qara na sauketa a kunne na ina dubawa naga ta ‘dauke da yiyuwar cajin ya qare kenan, na miqawa Halima wayar

“Ta ‘dauke rigwagwar wayarki”

Tsaki tayi ta amsa

“Zaki barni da jin haushinki da nike ko Zaki qaramin da cewa wayata rigwagwa”
Na ‘dan kunshe dariya ta na ce

“Tuba nake Amini”

Halima ta dubeni

“Sumayyah  maganar gaskiya banso kika ki fa’dawa Mama gaskiya ba zakiyi baqo yau ba zaki gidan Mama Atika ba,dan gaskiya ni banda banaso kiji babu da’di a ranki bansan mai zai kaini karo na da yawa zuwa danginki ba,saboda kinfi kowa sanin halinsu,banga mene anfanin kayi zumunci da wanda baisan muhimmancin zumunci ba”

Na runtse ido ina tunanin wasu abubuwa da sukemin ciwo idan na tunosu na Kuma bu’de ido na kalli Halima

“Halima ba laifin su ba ne, su ka ‘dai harda laifinmu fa muma talakawar munada kwa’dayi

Na tsinkayi muryar dieban adaidata sahun da muke ciki ya na cewa

“Yarinya kinyi tunani mai kyau halinmu yaja mana,sai dai kuma duk abinda ka bawa ‘dan uwanka baka fa’diba matsayinsa gareka yafi komai daka mallaka,shi ‘dan uwa kamar qashin baya ne,kana iya dawo da komai daka rasa amma banda ‘dan uwanka,dan ka kyautatama sa ko kullum zaginka yake baka fa’di,amma yarinya zumuncin ne kawai masu ku’din basu buqatar yi damu,wanda duk wuya duk rintsi mu kuma karmu yankesa domin munsan muhimmancin sada shi mun kuma san hukunci yanke shi”

Na jinjina maganar mutumin da duk ta ratsa mu wanda daganinsa dattijo ne dan duk ya haifi kamarmu zamu iya kiransa Baba,Halima ta jinjina kai ta fara magana
“Amma Baba masu ku’din basu buqatar zumuncin damu ne”

Baban yace

“‘Ya ta kenan ni zan fa’damiki basu san zumunci damu qanina uwa ‘daya uba ‘daya mai ku’dine sosai Abuja yake da zama yana kasuwanci amma da ‘diyata ta fa’damasa zataje hutun waya ya kirani ya ce”Shi dai yanzu ba wani jin da’di yake ba maleji yake amma wasu gani suke kamar wani Abu yake da shi amma duk an zuba ido Shi zai yi komai a dangi,hakanma bai isa ba har sai yara sun riqa zuwa hutu kowa ‘daukarsa wani jin da’di suke” “na baku labari sai da na ci ma sa mutunci saboda nasan dani yake kira yayi ta yimin rashin mutunci a fakaice dake shi wawane bai iya ba,kuma na baku labari ni da shi saina qirga abunda ya ta’ba ha’dani da shi,amma daga ‘ya ta zata hutu ya kira yana fa’damin maganar banza kamar yayannan nawa,kuma dukda hakan saida yarinyartawa ta tafi hutun dan ni banaso yarana su fahimci komai kuma ko da sun fahimta bana so ya zama su fahimta a guri na,bare ma zumunci ba mune muka ce a yi ba Allah da manzansa suka ce ayi,kuma idan na yanketa nasan makomata,shi fa zumunci abu ne mai girma dukda yadda zumuncin ya lalace banaso a ha’du dani gurin lalatashi,idan na tuno yadda zumunci ya lalace a wannan zamanin har mamaki nake ku duba da fa,da babu ko da abun Hawa yadda ake zumunci ba tare da an yi tunanin wane zai kawomin nauyi ba,shi kuma mai zuwa ba yana tunanin mai za’a basa ba idan zai taho,to amma yanzu fa da hanyar sada zumuncin tayi sauqi yanzune ba’asan sada shi.”

Kai muke jinjinawa maganar mutumin tana ratsa ilahirin jikina dukda bansan Halima ya take ji ba amma nafi tunanin hakanne itama,haka ya cigaba da Yi mana Nasiha mai shiga jiki yanayi yana jawo mana ayoyi da hadisai,wannan ya qara tabbatarmin mutumin mai ilimi ne musamman na addini kuma yana anfani da iliminsa wanda qasarmu irinsu take buqata a yanzu,ba wa’danda boko ta ratsasu ba ilimin addini ba,haka na cigaba da tunani akwaisu irinsu a qasarnan ashe amma qasar bata buqatarsu shiyasa ba wanda yasan dasu,dukda tarin ilimin Abbanmu amma na fahimci wanna yafisa saboda shi Abbanmu yafi zurfafa ilimin boko inda yake da Masters na addininma yanada shi sosai amma dai wannan ya fisa amma saina dubi yadda rayuwarsu take tafiya kamar wa’danda basu yi ilimi ba babu wani cigaba sai dai godiyar Allah tun daganan na qara fahimci rayuwar bawa arziqinsa da talaucinsa duk a hannun Allah suke,shine yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba wai dan baya qaunarsa ba sai dan ya jarrabasa,A haka muka qarasa Nasarawa GRA da har kofar gidan Mama Atika ya kaimu,wanda ko da mu ka fito motar muka basa ku’din napep bai ansa ba yadai ce.

“Ku dai ku sada zumunci karku gaji,ladanka kake buqata gurin Allah,dan ‘dan Adam indai danshi zakayi abu to a ko da yaushe kana iya dainawa,dan shi mantuwa garesa”
Zancen Baban ya qara ratsani kuma nayi alqawarin zan sada zumunci ba tare da gajiyawa ba da yardar ubangiji,godiya muka masa muka qarasa kofar gate ‘din gidan Mama Atika muka bu’de kofar shigar muka same ta bu’de hakan yasa muka danna kai cikin gidan da harabar motocinsu ke ciki a qalla guda uku,da ginin ya kasance self contained ne mai kyau.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Cancanta 7Na Cancanta 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×