Malam Abba wanda aka fi sani da Man Abba, dashi da ƙanin sa Malam Umaru asalin su fulani ne mazauna yankin Cadi, abinda ya baro su can sakamakon ƴan boko haram dake addabar su da kashe-kashe da sace-sace, dole suka yo hijira saboda wani farmaki da suka kawo musu duk suka rasa ƴan uwan su, su ma kansu daƙyar suka sha a lokacin, inda a cikin faɗi tashin da suka yi ne suka rabu da sauran ƴan uwan nasu, daga nan suka shigo cikin Nigeria wurjan-jan, abinci ma gagaran su yake yi, haka suka yi. . .