Riga da skert ne a jikin ta, duk da yayi ƙoƙari wajen zaɓo mata kayan amma sai da suka yi mata yawa, kuma rigan ba na skirt ɗin ta ɗauka ta saka ba, akwai maka-wuyan shi sai ta soma saka shi a ciki kafin ta sanya me dogon hannun a sama
Dariya ce ta so kama shi ganin ta fita daban da kayan, amma sai be yi ba illa murmusawa da yayi kawai ya zuba mata idanu
Ita kuma sai ta matso kusa dashi tana faɗin, "yaya ina magana. Yayi min kyau ko?"
"Sosai ma Minal. . .