Sai da Man Abba ya ja numfashi kafin yace, "Yusuf ba wai ina ƙin maganar ka bace, a'a sai dai don ka gane AMINATU ɗiya ce a wurin ɗan uwa na ɗaya tilo da ya rasu ya bar Ni, ita kaɗai nake gani na ji sanyi a raina, ina ganin ta tamkar ɗan uwa na Umaru ne, shiyasa bazan iya bari ta tafi nesa da mu ba, ko ba komi mu ne dolen ta, yanzu mahaifiyar ta tana can tana aure a Jigawa, bamu san wani rayuwa zata yi a can ba duk da kasancewar ta Uwa ce. . .