Da ƙyar Man Abba ya iya ce wa Yusuf, "ya ɗauke ta su wuce da ita asibiti".
Tsaban ya kiɗime kasa ɗaukan ta yayi, dole sai da taimakon Man Abba suka saɓa ta suka fita da ita da gudu. Man Abban ya dawo ya ɗauki Machine ɗin Yusuf suka wuce asibiti
Inna Rakiya kuwa tuni ta shige ɗakin ta tayi likimo ko damuwa bata yi ba, a ranta ma addu'a take yi, "Allah yasa ta mutu ko zata huta".
*****
Suna isa asibiti taimakon gaggawa aka soma ba su tunda Man Abba ya san ɗaya daga cikin likitocin. . .