"Abba..."
Ɗif maganan da yayi niyan yi ya ɗauke saboda maganganun Sadiya da suka yi clashing a kunnuwanshi kaman lokacin take mishi maganan.
«Yaayaana Allah da gaske da wayo na da hankali na, am 18yrs fa Yaayaa, na san me so nasan me shirme ko yaudara, Yaayaa ina son Haidar da dukkan zuciyata, irin soyayyan da ba dan tsoron Allah da imani ba, da kuma kasancewanka a tare da ni, da kuma kasancewan Haidar mutumin kirki, ba dan duk waɗannan ba, da ace Haidar mutumin banza ne to a irin yanda nake jin shi a zuciyata da ya jima. . .
