PLATEU SPECIALIST HOSPITAL
ABUBAKAR SADEEQ POV
Umar dama tun da safiya Sa'ad ya sanar da shi batun Sadiya, hakan ya sanya da ya koma ta yi rigimarta ya ce ta shirya, dan daman ko bata yi rigimar ba zai ce ta shirya ɗin.
Bayan dawowansa su Abba sun tafi, shi da Khalid ne zaune a ɗakin da aka kwantar da Sadeeq, Khalid ya ce, "Yaya Umar."
"Na'am Khalid", Umar ya amsa idanuwansa na kan system da ke gabansa yana dudduba ayyukan company.
Khalid ɗan sosa kanshi yayi sannan ya ce, "Yaya Umar please a bar Sady ta zo. . .