Bobbo da har yanzu be gamsu ba, wata muguwar azaba yake ji, sandar girmanshi duk ta tsage, ya fitar da ita yana jin wani mugun zafi, sai kuka yake yi, nan take ya sume ko motsi be iya yi saboda wahala. Mairo ko naƙuda ta taso mata zango-zango.
Wani abunda Asama bata sani ba Mamma da Bintoto sun zagaya bayan gari tsintar yanɗori, haka Asama ta dinga yawon nema wa Mairo ɗauki, dan ita har ga Allah tana kunyar ganin Bobbo ba kaya, kuma ita ba za ta iya kiran wani da ba su Mamma ba. Hanyarta ta dawowa gida ta ci karo da su Mamma, cikin haki da tashin hankali ta fara magana “Mamma Bobbo! “
Kallonta Mamma ke yi da mamaki fal ranta bata iya furta ko da ƙala ba ne.
Bintoto tayi saurin tarar zancen “me ya sami Bobbon?”.
“mu je gida ba kawai ku gani “Asama ta faɗa tana juyawa
Mamma da ji take kamar ta tashi sama ta fara tafiya sharaf-sharaf tana sharar takalmi.
Ɓangaren Mairo kuwa cikin ikon Allah haifi santalelen yaronta, nan take kukan yaron ya karaɗe gidan. Su Mamma na shigowa suka jiyo kukan yaro, ai cikin sauri suka nufi ɗaukin.
“innalillahi wa’inna ilaihir raju’un, muna ga rasulullahi, me ya samu wannan yaro ” Mamma ta faɗa cikin jimami, yayin da Bintoto ta nufi ɗan da ke gefen Mairo yana ta tsala kuka.
“Mamma ita ma Mairo bata motsi me ya same su” Bintoto ta faɗa.
“ki tambaye ni in tambayj wa? ” Mamma ta amsa maganar tana jawo wani zane, lulluɓe Bobbo tayi, sannan ta kalli Asama ta ce “me ya same shi”.
Asama dake lulleɓe jikin Mairo ta shiga yiwa su Mamma bayanin abunda ya faru.
Mamma ta shiga yin salati, dan ta fahimci abun Bobbo ya fara yawa.
Ruwa Bintoto ta ɗebo ta zuba musu, nan take Mairo ta sauke wata ajiyar zuciya, sai kuma ta fashe da wani matsanancin kuka.
Bobbo ko farcenshi bai motsa ba, ruwa aka ƙara kwara mishi, firgit ya buɗe ido, ganin mutanen da ke ɗakin yasa hawaye suka shiga tsere a idonshi, a hankali ya sauke idonshi kan Mairo da ke kuka.
Asama ta ɗauki yaron ta fito, Bintoto ta biyo bayanta, Mamma ma fitowa tayi aka ba su wuri.
A hankali ya fara matsowa kusa da ita ba tare da ya tashi ba, gaban Mairo kuwa duka yake yi uku-uku, ganin haka yasa bai ƙarasa kusa da ita ba.
“Kiyi haƙuri Mairo, ni na san mai laifi ne, dan Allah ki yafe min bani da wani zaɓi ne a lokacin ” ya faɗa.
Mairo dai ba ta ce komai ba, dan yanzu babu wanda yake jin ta tsana kamar Ibrahim Bobbo.
“ki ce wani abu dan Allah” ya faɗa, wani dogon tsaki ta ja, sannan ta ce “kai ka san Allah ne, mugu kawai azzalumi bazan taɓa yafe maka haƙƙina ba, macuci “, runtse ido yayi yana jin wani mugun zafi har cikin ranshi akan mugayen lafazin da take jifarshi da su.
Jallabiyarshi ya saka sannan ya tashi yana faɗi “ina fatan ki fahimce ni wata rana, sannan ki samu wuri a zuciyarki da zaki yafe min” yana gama faɗin haka ya fice, a tsakar gida yana jin su Mamma na mishi magana bai tanka su ba, har zai fita ya juyo.
Cikin taku ya ƙaraso kusa da Asama ya saka hannu ya ɗauki yaron da aka gama yiwa wanka yana shan hannu, huɗu ba ya mishi, sannan ya kalli Mamma da ta saki baki tana kallonshi tsabar yadda yake bata mamaki.
“Mamma sunan yaron Ibrahim ” ya faɗa sannan ya juya ya fita yana jin wani mugun zafi cikin ranshi.
Masarautar Sarki Banoto
Garin Mubanuwa gari ne da ake zuba tsantsar tsafi, sarki Banoto kuwa mugun hatsari gare shi, aljani ne da ke da matuƙar ƙarfin iko a garin Mubanuwa, Sarki Banoto bai haɗa komai ɗansa ba, so yake mishi da iya rayuwarsa, akan Barhim sarki Banoto ya zubar da jinin al’umma ba adadi.
Masarauta ta cika taf da Aljanu saboda saƙon mutuwar Barhim ɗan sarki Banoto, wata Muguwa ƙara ke tashi ko ina, yayinda ko ina na garin yayi baƙi, har yanzu sarki Banoto bai furta ko da kalma ɗaya ba, gawar Barhim kawai yake kallo, yayinda Bisamaji wato mahaifiyar Barhim take ta kuka, tana wani irin gunji kamar mayunwaciyar zaki, Barhim kaɗai ne ɗa ɗaya tilo da ta mallaka a rayuwarta.
Sai da suka shafe awa uku tsaye sannan Sarki Banoto ya miƙe tsaye, ya fara magana cikin ƙarfin ikon da yake ji da shi “Na rantse da Mahaliccina Allah sai na ɗauki mummunan mataki akan mutuwar ɗana Barhim, wallahi, wallahi, billahillazi la’ilaha illahu sai na halakar da rayuwa ahalin sarki Zawatunduma, na fi so a yi ɓarin jinin al’umma dan in halakar da rayuwar sarkin teku da Ƴar shi Naheela, wallahi sai yiwa ƴan garin Zawatu ɓarin duwatsu, na saukar musu da sauraye masu mugun dafi ” yayi maganar duka cikin tsawa da ɓacin rai.