Skip to content
Part 8 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela.

Cikin kakarin jini ta shiga kiran sunayen dabbobin tsafinta “Binaf! , Mazib, Bunut, kilkila” haka ta dinga kiransu suna sauka gabanta da ɗaɗɗaya, yayin da idonta suka rikiɗa suka yi ja.

Sarki Zawatunduma kuwa tun da Bilbil ya sauke shi bai motsa ba, sai wuta da kuma idonshi ke saki.

Dabbobin tsafin Naheela kuwa sai zagaye ta suke yi yayinda take ƙoƙarin tashin Zamzila.

Sarki Banoto yayi kukan kura da gudun tsiya ya nufo ta kafin ya kawo ya ji wani ƙarfe ya tokare mishi gaba, da sauri ya ja baya yayi juyi zuwa ɗayan ɓangaren ya nutsar da kanshi cikin Ƙasa.

Sarki Zawatunduma yayi wani ihu mai haɗe da gurnani ya nutsar da kanshi ciki.

Naheela kuwa jikinta ya sauya launi zuwa tsanwa shar. Dabbobinta sun fi hamsin waɗanda suka sauko sai ƙara rufe ta suke yi dan su ƙara mata ƙarfi. Wuta kawai suke saki ta baki. Daidai lokacin Zamzila ya tashi, shuuuuuuuu ya tashi sama ya sauko da kanshi ta ƙasa dai-dai saiti da gefen ƙirjinta ya ɗora bakinshi tare da ziro harshenshi inda mashin ya cake ta ya fara fitar da dafin da mashin ya sakar mata.

Idonta sun yi ƙulu-ƙulu kamar zasu faɗo ƙasa jijiyon idon sun yi baƙi ƙirin, zut ta ki fitar wani abu cikin Idonta nan take ta faɗi ƙasa sumammiya.

Zamzila ya rikiɗa zuwa majiji mai kai shida, yayinda sauran dabbobin suka haɗe kansu wuri ɗaya suka cira sama da ƙarfin gaske Zamzila ya sauko, garin ya ƙara turniƙewa da duhu da hayaƙi. Aka fara girgizar ƙasa a garin Zawatu.

Mutanen garin sai fitowa suke labarin mutuwar Naheela ya fara zagaye ko ina na garin.

Da ƙarfi dabbobin suka diro nan take suka dawo kamar mutane.

Binaf ta rungume Naheela yayinda ta rufe Idonta tana tuno duk abubuwan da tayi ma Naheela da irin taimakon da Naheela ke bata.

Da sauri ta miƙe tsaye ta rufe idonta tare da kara hannunta saitin kan Naheela ta fara sakar mata ƙarfinta.

*****

Ɓangaren sarki Zawatunduma kuwa musayan wuta ake ayi tsakaninshi da Banoto.

Cikin ƙarewa Sarki Zawatunduma ya sako wani siririn tsinke wanda ya kawar da  Sarki Banoto daga ganin wannan tsinke. Da gudu-gudu tsinke ya nufi sarki Banoto ya cake maƙogwaronshi.

Ko daƙiƙa ɗaya be ƙara ba ya faɗi ƙasa ba rai.

*****

Ɗakin Mairo ya shiga da sallama a bakinshi “Assalamu Alaikum “, ciki-ciki ta amsa mishi, bai damu da yadda ta amsa sallamar ba.

Wuri ya samu ya zauna gefenta, cikin tausasa lafazi ya ce “kin samu kin ci abinci ko?”, gaɗa mishi kai kawai tayi alamar eh.

“Ya Sadauki yake ” ya tambaya yana kallon Ibrahim dake hannunta.

“Yana Lafiya “ta faɗa a taƙaice tana Miƙa mishi Ibrahim da ya kira da suna Sadauki.

Karɓarshi yayi ya ƙara mishi Addu’a sannan ya Miƙa mata shi yana tambayarta “ba wani abunda ke miki ciwo.”

“Eh” amsa mishi cikin nuna ƙulewa.

“Allah ya ƙara sauƙi ” ya faɗa tare da tashi tsaye.

Can ƙasa-ƙasa ya ji ta ce “Ameen”.

Bai ce komai ba ya fita.

Ɗakin Bintoto ya shiga. Washe haƙora tayi tana faɗin “sannu da dawowa ashe ka shigo? “.

Murmushi ya ɗan yi ya ce “eh yanzu na shigo, ɗakin Mairo kawai na shiga.”

“Allah sarki bari na kawo maka fura yanzu na gama dama ta tana bayan Randa ” ta faɗa.

Numfashi ya sauke, sannan ya ce “a’a ki bar ta barci zan ɗan yi zazzaɓi nake ji.”

“Kaƙi cire damuwa ranka wallahi kar ka mutu cikin damuwa ” ta faɗa.

“Fatima kin kwashe shekara tare dani ina tauye ki, dan Allah ki faɗa min in zaki iya jure zama dani.” Ya faɗa yana ƙara jin zafi cikin ranshi.

Cikin rashin Fahimta Bintoto ta ce “ban fahimce ka ba?”

Iska mai zafi ya furzar ya ce “kina so mu raba auran nan?”

Da sauri ta ce “eh, eh walla……. “

Bata ƙarasa maganarta ba sanadiyyar kallon da BOBBO ya kafe ta da shi.

“Yanzu har na kai lokacin da kike gudu na?” ya tambaya.

Sai yanzu ta ji nauyin abun da ta faɗa, cikin noƙe kai ƙasa ta ce “Kayi haƙuri wallahi ni bazan iya jurewa ba, ina da buƙatar lafiyayyen namiji tun ina da saura na dan Allah Bobbo kayi haƙuri ya sawwaƙe min wallahi na daɗe ina neman ranar da zaka ce ka sake ni ” ta kai ƙarshen maganar hawaye na bin kuncinta.

“Kar ki damu Fateemar Sadauki yau ni Ibrahim Bobbo na sake ki saki biyu, idan kin gama idda kiyi aure Allah ya baki mai sonki wanda zai kare miki haƙƙinki” ya faɗa yana runtse idonshi.

Hawaye suka biyo kuncinta ta ce “a zamana da kai Bobbo baka taɓa muzguna min, matsalarka ɗaya ce kuma na fahimci lalura ce haka Allah yayi ka dan haka ba wanda ya isa ya canza maka taka ƙaddarar ina roƙon Allah ya haɗa ka da mahaɗinka, kayi haƙuri na gaza.”

Murmushi yayi waɗanda suka zo da hawaye masu zafi ya ce “Fatima da ina da mafita da nayi, bazan iya zama da wata mace ba dan na san cutar da ita zan yi, kiyi haƙuri na san matsalar daga ni take ina miki fatan alkhairi.”

Cikin kuka ta fara haɗa kayanta, yayinda zazzaɓi mai zafi ya rufe Bobbo, cikin minti biyar barci yayi awon gaba da shi.

Bintoto kuwa fita tayi, sai da tayi sallama da duka ƴan gidan, yaran gidan ma sun sha kuka da zata tafi.

“NAWA ƁANGAREN ” ya ji ana faɗa, da sauri ya ɗago daga jikin bishiyar da yake jingine jin muryar wadda ke kira shi da NAWA ƁANGAREN, murmushi ya ga tana mishi, babu abunda yake gani sai fararen haƙoranta.

“Ki faɗa min wacece ke?”ya faɗa

“Sadauki na faɗa maka ni ɓangarenka ce” ta faɗa.

“ɓangarena kamar yaya? ” ya tambaya, cikin ware hannu ta ce “ iya abun da na sani kenan”.

Matsowa ya fara yi kusa da ita yana faɗi “wacece ke na ce? “.

“Bobbo ban san ko ni wacece ba” ta faɗa tare da juyawa ta fara tafiya, gudu ya fara yi dan ya samu ya kamo ta amma sai ta dinga noƙe mishi, har ya gaji ya fara haki ita kuma ta wuce ba tare da ta juyo ba.

Kamar kullum yau ma  Bobbo farkawa yayi ba tare da ya samu ya ga wace ita ba.

Take ya ƙara jin zazzaɓi ya rufe shi yana jin wani zafi cikin jikinshi.

“Wacece ke? “ya furta a bayyane.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nawa Bangaren 7Nawa Bangaren 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×