Da sauri yasir ya katse shi "labarin yana da tsawo , mu shiga ciki mana, na barka a tsaye "
"No yasir, ina kan hanya ne, later zamu samu lokaci mu tattauna, dama kawai ka fado min ne naji ina san ganinka, wanne aiki kake yi yanzu? "
Kansa ya girgiza" babu aiki "
"Ok to Ga Email dina nan, katuramin ducument dinka gaba daya, zan nemeka insha Allah "
Yadauko kudi bundle daya ya bashi" kabawa su baba, kai kuma zaka jini "
Godia yasir yafara zuba masa,, sannan sukai Exchanging number
Daga haka sukai sallama, yana shiga motar ya lumshe. . .