Cikin kuka Umma ta ci gaba da fadin, "Alhaji shikenan an lalatawa Nawal rayuwa, anyi mata fyade, Innalillahi ni Safiya me zan cewa ubangiji na akan amanar daya bamu akan 'ya'yanmu"
Lokaci daya kan Abba ya sara, yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,"
'Yarsa da ya keji da ita, kuma yake sonta fiye da kowa a cikin 'ya'yansa itace yau aka lalatawa rayuwa
Jiri Jiri yafara ji, kafafunsa suka fara rawa nan danan yatafi zai fad'i aqasa, daqyar Salisu yataroshi yafadi ajikinsa
Yace" subhanallah sannu Abba "
Shi kansa salisun jikinsa rawa yake, wannan wacce irin. . .