Skip to content
Part 1 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Falo ne kato wanda yake dauke da duk wani nau’i na kayan alatu wanda falon hamshakan masu kudi ne kadai ake iya samunsu, falon ya kawatu kwarai matuka. Kan kujera me zaman mutum daya Taufiq ne zaune cikin shiga ta kamala kyakkyawan matashi ne ajin farko baki ne amma bakinsa me kyau ne.

An cika teburin glass din gabansa da Kayan ciye ciye da lemo Kala -kala Amma babu abinda Taufiq ya iya dauka ya ci saboda zuciyarsa cike take da sake-sake na dalilin Kiran da Haj. Murjanatu tayi masa na gaggawa wanda ko kadan bai son duk wani dalili da zai sa ta kira shi domin yayi Imani da cewa bakinta bazai taba furta abinda zaisa ransa yayi masa dadi ba ,tunda bikin nan ya kusa kullum cikin fito da sabbin abubuwa take wanda suke barazana ga Samun nutsuwarsa.

“Wai har yanzu babu abinda ka ci,” muryar Mujaheeda ta katse masa tunaninsa ya waiwayo yana kallonta fara ce amma irin farin da akance bai rufama muni asiri ba ahaka Ka kalleta zaka iya kiranta da kyakkyawa Kai tsaye amma da zaran Ka zuba Mata Ido zaka fahimci tsabar iya kwalliya ne zaisa Ka kirata da kyakkyawa,sai dai kallo daya zaka Mata Ka gamsu da cewa yarinya ce yar Hutu me ji da kanta wacce aka bata dukkan gata da kulawa na musamman.

“Na gaya Miki akoshe nake bazan iya cin komai ba”ta gyada Kai gami da yarfar da hannunta gefe alamar bai dameta ba ràshin cin nasa,tace “mummy tace Ka sameta afalon sama,muje KO”,da sauri ya amsa da toh gami da mikewa tana gaba Yana binta abaya har zuwa falon sama Wanda har ya so yafi falon kasan kyau da tsaruwa can Kan doguwar kujera haj.murjanatu ce kishingide ,Taufiq ya zube akasa Yana gaisheta ayayinda mujaheeda ta koma kusa da mahaifiyarta ta lafe ajikinta tana sangarta kamar yadda ta Saba.

Haj Murjanatu ta dubi Taufiq tace “Taufiq na bukaci kazo ne saboda ina son nayi wata magana da mai muhimmanci”, ya dan gyara zamansa yace “Allah yasa lafiya”ta jinjina Kai tace “lafiya kalau”ta dawo da kallonta kan tilon yarta sannan ta dauke idonta ta tsaidashi Kan Taufiq tace “ina son kasan cewa duk duniya Bani da wani abu da nafi so sama da yata mujaheeda farincikinta da kwanciyar hankalinta shine nawa Zan iya yin komai domin dauwamar da farinciki acikin rayuwarta,hakan Yana daya daga cikin dalilin da yasa na amince Ka aureta duk da nasan ba Kai bane kalar Mijin daya dace ta aura saboda abinda Ka mallaka ba zaka iya rike yata dashi ba, Amma tunda ta nuna Kai take so dole na tayata son abinda take so babu yadda zanyi.”

Ta hadiye yawu gami da Kara kafe Taufiq da Ido Wanda yake Jin maganganunta tamkar ana watsa masa wuta ajiki me yasa bata taba daukarsa wani abin kwarai ba bayan duk tarin nagartar dake gareshi?kullum ta Sami Dama Saita kushe Shi ta nuna Bai dace da yarta ba .acikin isa ta cigaba da cewa “atakaice na kiraka na gaya maka cewa bqbu yadda Zan amince ace Ka aje yata acikin gidan gado inda iyayenka da Matan yayyanka suke bata taso airin wannan rayuwar ba, ba Kuma zata iya ba arana tsaka,saboda haka cikin biyu saika zabi daya ko bayan daura auren Ka dawo nan gidan da Zama KO Kuma na Baka gida acikin gidajena Wanda zaiyi dai dai da rayuwar yata inda zata wala babu takura balle tsangwama.”

Taufiq yayi gaggawar dago da Kansa ya dubeta ta jinjina Kai tace “eh haka nace,ya rage naka kaje kayi shawara biki dai saura sati uku.” Wani gululun bakinciki ya tokare makogwaronsa ahankali yace,

“Toh shikenan,ni Zan tafi” ya fada Yana kokarin mikewa tsaye haj murjanatu ta bishi da kallo ba tare da tace masa uffan ba har ya Fara tafiya sannan mujaheeda ta taso ta biyo bayan Shi fuskarta babu KO alamar damuwa da maganganun da mahaifiyarta ta gaya mishi ya juyo ya dubeta fuska a hade yace “,da kin koma nagode “,tsayawa tayi cike da sangarta tace “Okey bye bye sai munyi waya” ta juya ta koma.

Cikin matukar bacin Rai da damuwa ya fito ya shiga motarsa discussion continue maigadi ya Bude masa get Yana a sauka lafiya hannu kawai ya daga masa ya figi motarsa ya tafi.

Tuki kawai yakeyi Amma tunani ne fal aransa,sau tari yasha tambayar Kansa shin meyasa bazai hakura da auren mujaheeda ba bayan yasan irin takun sakan dake tsakaninsa da mahaifiyarta,tunda ya Fara son yarta yake kunsar bakincikinta take kaskantar dashi don kawai mahaifinsa yayi aiki a karkashin mijinta tana ganin kaskanci ne ta aurama yarta Dan yaron mijinta bayan Mijin nata ma baya raye,Wanda Kuma take aure Bai Isa yasa KO ya hana ba,shin me yasa duk yasan wannan Amma yake kwadayin auren mujaheeda yarinyar daya fi kowa sanin irin shagwabata da sangartar da ita da mahaifiyarta tayi,sau tari yasha yin tunanin ya fasa auren Amma sai yaji ya kasa saboda masifar da Allah ya Dora masa na Sonta .Amma dole yaje ya zauna da mahaifansa ya gayá musu bukatar haj murjanatu Wanda Suma inda gajiya yaci ace sun gaji da irin korafin da da takeyi kullum.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Nima Matarsa Ce 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×