Skip to content
Part 20 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Mujaheeda sun cigaba da Zama da Taufiq babu yabo ba fallasa , domin dai maganar gaskiya ta kasa cire abinda Taufiq yayi mata aranta.

Kullum kafin ta tafi office ko bayan ta dawo takan je gidan su Taufiq ta duba Alh Yusuf lamido da jiki wanda ya ji sauki sosai ya warware , Amma kullum zata ganinsa bata tafiya hannu ba komai sai tayi masa sayayya,
Wannan nuna kulawar da take masa Yana daya daga cikin dalilin da yasa ta kara shiga ransa yana matukar jinta araina tamkar yar da ya haifa.

Ta bangaren Alh jibrin kuwa yana iya kokarinsa wajen ganin ya kusanta kansa da Mujaheeda, duk Kuma wani motsinsu Murtala na gefe Yana kokarin dauiar hotuna.
Yau da wuri mujaheeda ta tashi ,saboda ciwon kan da take yi, hakanan Kuma taji bata son komawa gida a wañnan lokacin dalilin hakan yasa ta wuce gidansu.

Tun zuwanta gidan tana kwance kan cinyar mahaifiyarta. Duk yadda ta so ta boye mata damuwar da take ciki saida ta gane tana cikin damuwa.

Duk irin abincin da Haj murjanatu tasa aka dafama mujaheeda ta kasa ci, ta Kuma kawo mata uzirin bata jindadi ne.

Haj murjanatu tayi Jim sannan tace ” ni Kam mujaheeda tun aurenki naji na rasa kwanciyar hankali, na Kuma rasa farinciki,” Mujaheeda tace “saboda mene mummy.”

Tace tana bubbuga Saman bayanta kamar Wata karamar yarinya , tace ” saboda ina ji ajikina kwata kwata bakya jindadin auren nan, ki dubeki kigani ko irin cikar dakin nan bakiyi ba Saima rama da kike yi kullum, mujaheeda babu abinda bazan iya yi domin Samun farincikinki ba amma kin ki Goya min baya, saboda baki son damuwar mijinki, amma ni kina son damuwata ko.”

Mujaheeda ta gyara kwanciyar ta akan cinyar mahaifiyarta gami da lumshe idanunta, tabbas tana cikin damuwar irin zamantakewar dake tsakaninta da mijinta, burinta a duniya bai wuce ta zauna lafiya da mijinta ba su zama abokin shawara su zama jini daya amma hakan ya faskara kuma ta rasa hanyar shawo kan matsalar, tunda tayi auren nan bata taba sati uku cikin farinciki ba kullum sabani kullum fada ta yaya Zama zaiyi dadi ahaka zai Kuma tafi yadda take mafarki.

“Mummy ba damuwarki nake so ba, illa iyaka bana son ki dinga samun matsala da yaya Taufiq don bana son raini ya shiga tsakaninku.”

Haj murjanatu tace” to naji, amma yanzu ina son ki gaya min menene matsalar, tsakaninki da Taufiq.” Ta girgiza Kai tana kokarin boye duk wata damuwarta tace, ” babu komai mummy tsakaninmu lafiya kalau” Haj murjanatu tace cikin ràshin gamsuwa da maganarta ” to damuwar meye a fuskarki idan bata Taufiq ba.”

Mujaheeda tace ” damuwar office kawaii mummy, domin na gano kamfanin nan akwai matsaloli masu yawa a cikinta.”

Tayi kokarin kauda maganar da Haj murjanatu take son ayi.
Itama Haj murjanatun nan da nan tace ” matsala a kamfanin?”

Mujaheeda ta tashi ta zauna tana kallonta tace ” sosai kuwa mummy, shiyasa nake mamaki da kike fadin kirki da rikon amana irin na Alh jibrin, domin bashi da wannan kamalar, Kuma ina zargin tamakar baida gaskiya.”

Haj murjanatu tace cike da mamaki” me yasa kika Fadi haka, domin tabbas ina alfahari da gaskiya da rikon amanar Alh jibrin”. mujaheeda tace ” sanin hakan yasa ban so na gaya Miki komai ba har sai binciken da nake yi ya tabbatar da lefinsa, don haka ko yanzu babu abinda zance Miki sai na Gama bincikena.”

Haj murjanatu ta jinjina Kai tace ” naso Naji abinda kike tunani amma tunda kince haka Zan Jira har ki gama bincikenki amma kafin sannan ina son ki Kula matukar kulawa don Allah ” ta jinjina Kai tace ” insha’Allah mummy Zan Kula.”

Ta jidadin zaman gidan su bata so ta koma gida amma tunda bata son Haj murjanatu ta fahimci irin zaman da take yi da Taufiq.hakan yasa ta tattara ta koma gidanta gaf da magriba.
*****
Tunda aka tashi islamiyya, muhseena ta Lura kwarai da yadda wani matashi yake binta.
Har zuwa lokacin dá suka zo inda zata dauke hanyar shiga gidansu.

Sannan taji matashin saurayin yayi Mata sallama , ta amsa lokaci daya tana waigowa, saurayi ne matashi ba wani kyau gare Shi ba, Amma Yana da matukar kwarjini da Kamala Kuma kallo daya zakayi masa Ka gamsu da natsuwarsa.

“Kiyi hakuri na tsayar da ke ahanya, bayan daga islamiyya kika fito”.ta girgiza Kai tace ” badamuwa , wani abun kake son tambaya ko me.”

Ya dan gyara tsayuwarsa yace ” kawai sunanki nake son sani.”

Muhseena tayi mamakin wannan tambayar domin dai karamin kauye kamar Durmi idan tace babu Wanda bai Santa ba ko labarinta to tana ganin batayi karya ba.

Kamar yadda bata taba cin Karo da wani da ya tsaya ya tambayeta sunanta ba.
Tadan dubeshi sosai tace”

Amma dai da alamar kamar Kai bako ne ko”.
Yadan yi murmushi yace ” kusan hakanne, Amma dai nan gari na ne nan cibiyata take sai dai nace banyi rayuwa sosai acikinta ba.”

Ta gyada Kai tace ” sunana muhseena “.
Ya lumshe Ido ya bude yace ” suna Mai dadi” tace ” nagode, shikenan Zan tafi” yace ” ina son yin magana da ke Amma ina ganin tsayuwa ahanyar bai yi tsari ba, don haka idan babu damuwa ina son ki amince min nazo gidan Ku bayan sallar isshai domin mu tattauna”

Ras muhseena ta Sami kanta da faduwar gaba tunda take yau ce rana ta farko da wani saurayi yayi Mata irin wannan maganar.
A hankali tace” babu damuwa kana iya zuwa”

Yayi murmushi sosai har kasan gemunsa ya lotsa tace,” to ina godiya, ina ne gidan naku”.sannu ahankali ta Gama yi masa kwatancen gidan sannan sukayi sallama ta tafi.

Ba tare da tasan sunansa ba ko ta tambaya.bayanta shima yabi da kallo harta bacema ganinsa.

Tunda muhseena ta koma gida,take tunanin zuwan saurayin nan, hakan taji tana adduar Allah yasa karshen wahalarta ne yazo , don a yadda take Jin komai aranta ko waye komai talaucinsa in dai zai aureta zata yarda ta aure Shi domin ta fita daga cikin kangin da take ciki Wanda babu Wanda zai fahimci irin kangin da take ciki sai Wanda ya dandani irin rayuwar da take ciki.

Tun bayan idar da sallar isshai , muhseena ke zaune Kan tabarma ko hijabin bata cire ba,bakinta na cike da adduar Allah yasa yazo kamar yadda yayi alkawari.

Sallamar mahaifinta yasa ta dago da sauri tana yi masa sannu da zuwa
Ya amsa Yana kallonta , sannan yace ” muhseena kije waje kina da bako.”

A gaggauce Hajara da take zaune a gefen tabarmar da muhseena ke zaune tace ” bako? Wanene”. Mallam Umar yace ” yanzu dana dawo daga masallaci na tadda Shi a kofar gida , shine na tambaye Shi abinda yake nema shine ya sanar da ni wajen muhseena yazo, Maza ki tashi kije, ki saurare Shi.”

Ande Dije ta dago labule ta fito daga dakinta tana fadin” ikon Allah mafarki ko ido biyu yau muhseena ake sallama da ita tikisa.”

Ba tare da kowa ya bata amsa ba, Hajara tace ” tashi kije.”

Muhseena ta mike ta gyara zaman hijabin da ke kanta , sannan ta wuce kofar gidan.
Tsaye ta tadda Shi, sai kamshi yake yi, hatta kayan jikinsa ba su bane na dazu ya canja.

Tayi masa sallama ya amsa, Yana kallonta duk da babu wani haske agun to hasken farin Wata ya rsgema garin duhu sosai.

Yace ” gani na zo” ta Dan yi murmushi tace ” barka da zuwa”.daganan ya gyara tsaiwarsa cikin murya Mai cike da tabbatar da muhimmancin abinda zai fada yace ” dazu shine Karo na uku da na ganki tun bayan dawowata garin, Amma tun ganina da ke na farko naji na aminta da ke, naji zuciyata ta Sami nutsuwa da ke ,ma’ana ina sonki so ba na wasa ba, so Wanda zai kaimu ga aure”.
Muhseena taji wani abu ya ratsa ta cikin zuciyarta , iya tsawon shekarun da tayi a duniya sai yau ta ji abinda yammata ke ji idan saurayi yace Yana sonsu, domin dai ita bata riskar rana irin ta yau ba.

Tayi kasa da kanta dadi da kunya suna Kara lullubeta . Yace ” Baki ce komai ba, Allah yasa wani bai rigani ba”.
Ta girgiza Kai a hankali tace ” babu Wanda ya rigaka”. Yace ” Alhamdulillah,”. Ya cigaba da cewa.

“Ni suna Kabir , kamar yadda na gaya Miki nan itace mahaifata to hakane nan aka haifeni Amma duk rayuwata nayi ta ne a garin Kano wajen kawuna Wanda shine ya rikeni, a gunsa nayi karatu naje har matakin degree ayanzu haka Kuma ina Taya Shi rike daya daga cikin kamfanoninsa.”

Ya hadiye yawu gami da Kara gyara tsayuwarsa, sannan ya cigaba da cewa ” iyayena suna cikin kauyen nan mallam Hamza wanzami shine mahaifina,” cike da gamsuwa muhseena tace ” na fahimta “.
Yace ” kinsan a yanzu daga mahaifana har uban goyi na burinsu daya shine nayi aure, to ayau dai adduar su ts karbu domin na Sami matar aure.”

Tayi murmushi aranta tana adduar Allah ya tabbatar da hakan, domin dai taji ta aminta da Kabir , gashi dan gayu, gashi dan birni, ga natsuwa da Kamala. Lalle wani hanin ga Allah baiwa ne.

Sun dade Kabir na Kara gayama muhseena ko waye shi.sosai Kuma ta gamsu dashi ranta yayi fes, hakanan Kuma taji ta Bude ma soyayyar Kabir zuciyarta gaba daya.

Awannan daren dai muhseena taji ajikinta itama macece .har suka rabu da Kabir ji take kamar wasa.

Tana zaune a Kan katifa kusa da Hajara magana suke ” yace Shi dan gidan mallam Hamza wanzami ne.”

Hajara ta dubi mallam Umar da shigowarsa kenan dakin tace ” kaji wai sunansa Kabir Dan gidan mallam Hamza wanzami, dama mallam Hamza Yana da babban yaro ne bayan dansa marigayi habibu.”

Mallam Umar yayi Jim alamar tunani , sannan ya dubesu yace, ” Kai anya kuwa ko Yana dashi gaskiya ban san Shi ba.”

Muhseena tace ” eh , yace a Kano ya tashi , bai zauna anan ba”. Hajara tace ” yauwa ko da naji, to Allah dai yasa alheri , Allah ya kauda duk wata fitina yasa a fahimci juna.’

Mallam umar yace ” Amin ya Allah, in dai da maganar aure yazo babu wata matsala”.daganan ya fice zuwa dakinsa.
Ranar daker muhseena ta iya bacci saboda murnar yau Allah ya kawo Wanda yace Yana sonta , adduar ta daya Ce Kada Allah ya kawo duk wani abu da zai kawo matsala acikin tarayyarta da Kabir, domin dai KO bata son Kabir to fa tana da bukatar tayi aure, balle tana sonsa.

<< Nima Matarsa Ce 19Nima Matarsa Ce 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×