Skip to content
Part 28 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Mujaheeda na kwance a Kan gadonta dai dai misalin karfe daya saura minti hudu na dare.Alh Mustapha labaran ya turo kofar dakin Mujaheeda cikin sallama lokaci daya yana mai kunna wutar dakin, nan da nan haske ya wadaci dakin hakan yasa Mujaheeda ta tashi daga baccin da take idonta ya Kara wartsakewa alokacin da taga daddy ne a tsakiyar dakin, ahankali tace,

“Daddy lafiya” ya karaso cikin dakin gami da zaunawa akan kujerar kwalliyar dake kusa da madubi Yana kallonta sannan yace ” lafiya lau mujaheeda magana nake son nayi, bana so Kuma Haj tasan nayi miki maganar shiyasa na zabi dare a matsayin lokacin da ya dace muyi maganar.”

Jin hakan yasa mujaheeda ta Kara wartsakewa daga baccin data fara ta natsu sosai tana kallonsa tace ” to daddy ina jinka.”

Ya jinjina kai yace ” mujaheeda nasan kin dau zafi agame da abinda Taufiq yayi Miki, Kuma banga laifinki ba, amma ina son ki sani duk inda mutum yayi laifi ya Kuma yarda da yayi laifi harna ya nemi afuwa to abune kusan da ya Zama dole ayi masa afuwa” ya cigaba da kallonta Yana cewa ‘ don haka babu laifi idan kin yafema Taufiq kin koma gidansa kun cigaba da rayuwarki. A wannan rayuwar da ake ciki mujaheeda ko wace mace hakuri take agidan aurenta domin kuwa babu wacce take samun abinda take so dari bisa dari, komai jindafinki komai zaman lafiyarki komai son da miji yake miki dole sai kin hadu da abinda ba kya so. Kin san dalili?”

Ta girgiza Kai yace ” saboda aure Ibada ne anan Kuma mace take Samun aljannarta domin Annabin rahama ya fada duk matar data sallaci sallolinta guda biyar tayi azumin watan Ramadan ta kiyaye farjinta daga zina sannan tayi ma mijinta biyayya to sakamakonta gidan aljanna ne, haka zalika dimbin ladan da Mata suke Samu agidan aurensu Bai musaltuwa don haka Zama da aure shine darajar ko wace mace haka zalika yima Miji biyayya ya Zama dole ga Mata saboda haka ina ganin lokaci yayi da zaki tattara ki koma gidan mijinki Ku rungumi junanku.”

Ya numfasa ya cigaba da cewa “Ina gaya Miki wannan ne saboda kin rasa mai gaya Miki domin mahaifiyarki itace ta cancanci ta gaya Miki gaskiya amma kiyayyar aurenki da Taufiq ta hana ta gayá Miki, don haka don Allah na rokeki kiyi hakuri ki saurari mijinki ki Kuma koma gidanki, kullum surukinki da mijinki sai sun kirani awaya da rokon ki dawo, ni Kaina bana son su fahimci Bani da wani kima ko daraja acikin maganarki ban son su gane ban isa da mahaifiyarki ba, idan kika yarda kika koma ni Kaina kin taimakeni wajen tsira da mutuncina.”

Sosai mujaheeda ta tsaya ta fahimci Alh Mustapha labaran Wanda Dama itama ta riga ta sakko tana son ta koma gidan mijinta.

Ta dan muskuta gami da dubansa tace ” Babu komai daddy na yarda da dukkan maganganunka in sha Allah zan koma” ya dan yi murmushi yace ” Nagode ya ta ,yanzu idan sun Kara Kira me Zan ce musu” tace ” daddy Ka gaya musu Ka isa da yarka na Kuma yarda na amince Zan koma gidan Taufiq tare da mantawa da duk abinda ya faru’. Ya jidadin maganar ta yace,

“To shikenan koma ki kwanta kiyi baccinki Allah yayi miki albarka ” tace “Amin daddy ” lokaci daya ya tashi ya fice cike da farinciki, yau dai ya samu yayi magana da mujaheeda abinda Haj murjanatu bata so.

Mujaheeda ta numfasa ta koma ta kwanta gami da rufe jikinta da bargo. Hakika tana son Taufiq so me yawa tuntuni ta ji zuciyarta ta daina Jin haushinsa ta ji tana matukar begensa don haka lalle zata koma dakinta domin tasan duk inda Taufiq yake yayi matukar yin nadama idan tayi la’akari da irin sakonnin da yake turo Mata masu nuna nadama da son ta dawo gare Shi.

Kuma ma bayan haka tana matukar Jin nauyin Alh Yusuf lamido ko don Shi zata iya yafema Taufiq ta koma gidansa.

Washegari mujaheeda da Haj murjanatu da Àlh Mustapha labaran suna Kan teburin cin abinci Suna karyawa , duk wani abincin da mujaheeda ke son ci da safe an dafa Mata.

Haj murjanatu ta Kai lomar kwai bakinta kenan ta ji maganar mujaheeda kamar daga sama tace “mummy xan koma dakina in sha Allah”, nan da nan Haj murjanatu tayi kasa da cokalin hannunta daker ta iya hadiye kwan , ta juyo gaba daya ta zuba Mata Ido tace ” me kika ce?”

Kafin mujaheeda tayi magana Alh Mustapha labaran yace ” tace tana son ta koma dakin mijinta Kuma wannan magana ce me kyau domin abinda ya kamata kenan.” Ta sakar masa harara afusace tace ” babu ruwanka da shiga maganar nan domin nasan Baka ganin lefin Taufiq duk abinda zaiyi babu assha aciki saboda duk halinku daya, Kuma Ka sani yadda na shaki bakincikinka bazan taba barin mujaheeda ta shaki bakincikin Taufiq ba don matsayin yata ya wuce haka.”

Mujaheeda tayi saurin aje cokalin hannunta cikin damuwa ta buga tebur tace ‘ don Allah mummy kada ki Fara domin babu laifin daddy ko daya nice na yanke shawarar komawa gurin Taufiq domin ya yi nadama ya Kuma bada hakuri” afusace tace “Nadamar Shi din banza da wofi ban hakurin me ya jefeki da irin wannan mummunan zargin sannan har kiyi tunanin koma masa, ai nayi zaton kina son na baki lokaci ne idan kin gama Tunaninki sai ki bani damar raba auren Ku , domin dai kinfi kowa sanin cewa dama Taufiq bai dace da ke ba so ne kawai na Shi da kika dora ma kanki yasa na barki kika aure Shi , yanzu Kuma bayan ràshin cancanta harda ràshin iya rukon aure ke karewa ma dai Taufiq baya sonki.”

A gaggauce mujaheeda tace ” Taufiq Yana Sona, babu abinda zai canja hakan, mummy nasan kin goyi bayana kin share min hawaye alokacin da na shiga damuwa amma hakan bashi zaisa kiyi tunanin kashe aurena da Taufiq ba acikin dan kankanin lokacin da nayi da aure kike son na zama bazawara mummy?”

Shi dai Alh Mustapha labaran bai kara cewa uffan ba, domin yasan yadda Haj murjanatu ta fusata idan yace zai cigaba dasa baki acikin maganar allura tana iya tono garma tana iya fadan maganganun da zasu iya Zama damuwa Shi yasa ya ja bakinsa yayi shuru.

Haj murjanatu tace a harzuke” Yanzu kina nufin kice zaki koma gidan Taufiq duk irin abinda yayi Miki kin manta”. Ta gyada Kai tace ” ina son na koma, saboda na fahimci ko zargin da yake min din so ne ya haifar da haka , Kuma ko ba don hakan ba ko don mahaifinsa zan koma gun Taufiq domin Yana so na ya Kuma fi kowa damuwa da faruwar abinda ya faru, bayan haka Kuma ina son Taufiq so na hakika son da bazan iya rayuwa babu Shi ba, na Kara fahimtar hakan ne bayan zaman da nayi a gidan nan ba tare da shi ba.”

Haj murjanatu ta saki tsaki tace ” idan hakane kuwa to tir da irin wannan soyayyar da kike masa, Kuma ki shirya karbar wukakanci da ga gare Shi tunda ya riga ya gane son da kike masa yafi wanda yake Miki.”

Mujaheeda ta nisa tace ” mummy bana son kina damuwa akaina don Allah” tace ” dole na damu akanki domin nafi kowa sanin muhimmancin ki, Kuma zanyi fito na fito da duk Wanda zai daga Miki hankali.”

Mujaheeda tace ” Duk dai aikin nan ne ke son Haddasa min fitina da damuwa agidan aurena bayan Kuma duk yadda na Kai da son aikin nan to na fi son mijina da Shi don haka na yanke shawarar Zan bar aikin nan kawai.”

Alh Mustapha labaran yayi karaf yace ” Alhamdulillah da kika gane hakan babu abinda aikin nan zai amfaneki da Shi domin dai duk arzikin nan kusan naki ne babu amfanin ki wahalar da kanki Akan abinda yake mallakinki ne, zaman lafiyar aurenki ya fi komai.”

Haj murjanatu ta saki wani irin dogon tsaki tace ” Ka dakata anan domin Taufiq Bai Isa ya hana ki mallakar abinda kike so ba tunda kina son yin aiki dole sai kinyi bai Isa ba bai Kai wannan matsayin ba da zaki bar mafarkinki domin farincikinsa ba.” Alh Mustapha labaran yace

“Aiko ya isa har yayi yawa duk wañnan abinda kike yi Taufiq ya fiki iko da rayuwar mujaheeda gaba daya idan kika aje sharadi ya aje sharadi shima dole mujaheeda ta dauki sharadinsa ta aje naki Haj girman miji fa ya wuce duk yadda kike tsammani.”

Tace a kufule” me Ka sani akan hakan tunda kai dai baka taba Zama Miji Nagari ba , har wane girman miji Ka sani” yace ” komai zamana ba Miji nagari ba babu inda addini ya baki damar da zaki ci mutuncina ko ki ki yi min biyayya ba” nan da nan ta Kara fusata tace ” Anki ayi maka biyayyar, zaman dolen da akeyi.”

Cikin kagauta mujaheeda ta toshe kunnanta ta Mike ” na tsani wannan rayuwar na tsani abinda kuke ma junanku, ni gidan mijina zan koma ya fi min Akan na zauna ina cigaba da ganin abinda tun da na taso nake gani na Kuma tsana” tana Gama fadan hakan ta juya da sauri ta shige dakinta.

Cikin jajayen idanu Haj murjanatu ta juyo Kan Alh Mustapha labaran tace ” Kai har kana da bakin yin irin wadannan maganganun Kai da babu Allah agabanka ko kana ganin akwai ranar da Zan manta da bakin halinka agareni ko kana ganin akwai ranar da zaka wanke kanka da ga bakin fentin da kayima kanka awajena saboda haka yafi sauki kayi shuru idan aka zo magana akan aure domin baka da bakin magana.”

Kwata kwata Alh Mustapha labaran baya son maganar ta Kara yin tsawo domin yasan hakan bazai haifar da da mai ido ba.don haka shima ya ture kayan karyawar tasa gefe ya tashi ya dau makullin motarsa ba tare daya tanka irin maganganun da Haj murjanatu take sakar masa ba ya fice, fadan da take yi tuni ya Fara janyo hankalin masu aikin gidan.

Haj murjanatu ta tashi jikinta babu laka tabi mujaheeda daki. Tana shiga ta tadda ita ta shiga wanka.ta tsaya jugum komai ya kwance Mata ta dauka zatayi nasarar cire Taufiq acikin rayuwar mujaheeda amma ya Zama dole ta yarda da cewa mujaheeda ba zata iya barin Taufiq ba saboda mugun son da take masa. To Amna fa babu yadda zatayi ta iya yarda da Taufiq ya tauye mata rayuwar ya ya hanata walawa da jindadin rayuwarta lalle dole tasan yadda zatayi ta ladaftar da Taufiq ta yadda zai biyu yayi duk abinda mujaheeda take so atakaice dai tana da bukatar mujaheeda ta mallake Taufiq ya Zama rakumi da akala ta yadda ko kudi aka bashi akace ya batama yar ta rai ko ya sata damuwa bazai iya ba.tana son mujaheeda ta Zama ita kadaice me juya rayuwar Taufiq yadda ta so ta ga dama tana ganin lokaci yayi da zata mayar da Taufiq kamar yadda ta mayar da Alh Mustapha labaran ta yarda zata Zama Mijin Shi Kuma ya Zama matar.

Cikin sassarfa ta fice daga dakin mujaheeda ta shiga dakinta ta rufe kofa ta sa makulli, ta dauki wayarta ta Kira aminiyarta Haj Nana bugu biyu Haj Nana ta dauka Jin muryar Haj murjanatu cikin tashin hankali yasa ba ta ja maganar da tsawo ba tace, ” Haj yaya dai lafiya kuwa” tace tana Kai gauro da Mari atsakar dakin ” kina gida ne Haj” ta gyada Kai “Eh ina gida lafiya dai ko?” Ta saki numfashi tace ” Ba lafiya ba gani nan dai zuwa gidan yanzu.”

Haj Nana tace ” To shikenan sai kinzo”. Nan da nan ta fada bandaki tayi wanka cikin kankanin lokaci ta fito ta Gama shiryawa cikin kiriyar atamfarta super exclusive ,ta dora gyalenta akanta ta dau Jakarta ta fito.

Bata ko bi ta kan mujaheeda ba ta fice abinta.

Direba na ganinta ya Mike ya nufi wajen motoci ” barka da fitowa Haj, awace motar zaa fita?” Ta dube Shi tace ” ko wacce ma Ka dakko” fahimtar tana cikin sauri ya sa ya wuce da sauri ya fito da makullin daya daga cikin motocin da suka cika rufunan motocin gidan.

Ya Bude Mata ta shiga da sauri ya rufe ya shiga ya ja maigadi ya bude masa kofa ya fice Yana tambayarta ” ina mukayi Haj” Kai tsaye tace ” gidan Haj Nana” ya gyada Kai kamar tsohon kadangare yace “Angama ranki ya dade.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 27Nima Matarsa Ce 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×