Skip to content
Part 6 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Taufiq yayi kasa da Kansa zuciyarsa na tafasa ya kasa cewa uffan.haj saratu ta numfasa tace “To ni dai bansan me Haj murjanatu take son ayi Mata ba ,duk abinda tace ana kokarin yi duk dai don asami zaman lafiya Amma na rasa dalilin da yasa kullum take kokarin bata al’amarin nan, abin ya Fara damuna kwarai da gaske ,don ina ganin ko Anyi auran nan tamkar ba zaa samu wani kwanciyar hankali ba.”

Haj Bilkisu tace cikin fusata ” na rasa gane me take so Kuma me take nufi, Ko itace Yar Karuna iya karyar arzikin da zata dinga yi kenan, shin su kadaine masu kudi Kuma mu din bamu da rufin asiri ne meye abin kushe agaremu ,me yasa take jindadin wulakantamu?”

Haj laraba tace don Allah don son Annabi abar maganar nan kadama akara yinta.
A sukwane Taufiq ya tashi ya fita batare da yace komai ba Haj laraba ta bishi da cewa ” Adaiyi hakuri Taufiq babu komai rayuwarma guda nawa take.”

Haj Bilkisu ta juya ta cigaba da maganganun ta na bacin rai ayayinda Haj laraba ta cigaba da tausa su .azahiri Haj saratu abin ya Fara fita kanta ta gaji da wadannan kananan maganganun ,kamar yadda ta kasa gane ina matsalar take? Me Haj murjanatu take nufi? Meye tunaninta akan danta Taufiq?.irin tambayoyin da Haj saratu take ta yima kanta kenan.

Taufiq na zaune asaman kujerar fslonsa ya harde hannayensa a gaban kirjinsa Yana Kada kafafuwa Kaida kallon fuskarsa kasan Yana cikin damuwa.ya tashi ya shiga sintiri a tsakiyar falonsa.

Yana tunanin halinda yake ciki agame da lamarin mujaheeda.ya daga Kai ya na Karema falon kallo, ahankali ya tambayi Kansa shin meye aibun wannan wajen da mujaheeda ba zata iya Zama aciki ba?, Me yasa Haj murjanatu take kokarin daukarsa a sakarai ? Wane irin nakasu gareshi da suke kokarin kaskantar dashi shin ahaka zai auri mujaheeda idan ya aureta wace irin rayuwa zaiyi da ita.
Shin mujaheeda ta dace dashi kuwa? A hankali ya Sami Kansa da ba Kansa amsa da cewa mujaheeda bata dace dashi ba.

Rayuwar su ba zata taba Zama dai dai ba da muguwar rawa gwamma kin tashi baya Jin zai iya auran mujaheeda bayan duk wadannan abubuwan dake fsruwa.

Me zai hana bazai rabu da ita ba ya Sami dai dai dashi.
Ya koma ya zauna Yana kokarin sama Kansa natsuwa da dangana akan mujaheeda.
Ahankali ya Ciro wayarsa daga aljihunsa ya Danna ya Kira mujaheeda bugu daya acikin na biyu ta dauka.

“Taufiq” Bai amsa ba yace cikin dakakkiyar murya ” na kiraki nayi miki godiyar cin mutuncin da mahaifiyarki tayima yan’ uwana ” mujaheeda ta yi saurin cewa ” don Allah kayi hakuri nima banjidadi ba Kuma bana gidan hakan ya faru don Allah kayi hakuri.”

Ya girgiza Kai yace ” ba lefinki bane don haka basai kin Bani hakuri ba,tunda lamarin nan ya Zama haka ina ganin muyi hakuri kawai da juna Allah ya hada kowa da rabon sa don Bana Jin Zan cigaba da jure irin wannan bakin wulakancin daga mahaifiyarki,Wanda ke kanki da da gaske kina min son da kike ikirarin kina yimin da baki bari hakan na fsruwa ba Amma tunda haka kika zaba na hakura abar maganar aure…..?

Adaburce mujaheeda ta Mike duk ta gigice tace ” Abin bai Kai haka ba don Allah Ka daina wannan maganar ta yaya zakace Ka fasa don Allah kayi hakuri.”

Ya girgiza Kai yace ” kiyi hakuri Amma ina son ki sanar da mahaifiyarki na hakura da auran yarta ta je ta aura Miki Wanda take so Wanda zata samu natsuwa dashi, ni na hakura.”

Yana Gama fadin haka ya kashe wayarsa.lokaci daya mujaheeda ta kwala ihu Wanda ya dawo da hankalin Haj murjanatu kanta da take zaune afalo da saurin gaske ta tashi ta taho dakin.

Shigowarta yayi dai dai da lokacin da mujaheeda ta sulale kasa ta fadi sumammiya tana dafe da gefen kirjinta idanun Haj Murjanatu suka firfito nan da nan ta fita hayyacinta. Tayo kan yarta tana adduar Allah yasa ba ciwon zuciyarta bane ya tashi.

*****
Cikin matsananciyar damuwa Haj murjanatu ta cigaba da girgiza mujaheeda tana Kiran sunanta,cikin firgitacciyar murya.

Lami ta fado dakin da sauri itama ganin abinda yake faruwa yasa ta tsuguna agaban mujaheeda itama tana Kiran sunanta ,cikin Jan Ido Haj murjanatu ta dubi lami ta bata umarnin tayi saurin taje ta sanar da direba ya fito da mota.

Fitarta yayi dai dai da lokacin da Haj murjanatu ta Mike ta tattagi mujaheeda tana nishi tayo waje da ita sauran hadiman gidan suna ganin ta Suma cike da tashin hankali suka Sanya hannu suka tayata karasawa da mujaheeda wajen mota.nan da nan aka sanyata a mota kowa cikin tashin hankali domin sun san irin wahalar da mujaheeda take sha matukar ciwon zuciyarta ya tashi.

Haj murjanatu ta kusa tafiya asibitin babu gyale sai da lami ta tuna Mata sannan ta tsaya har lamin ta kawo mata gyalen sannan direba yaja motar a sukwane zuwa care hospital, babban asibitin kudin da mujaheeda take ganin likita a garin jigawa.

Tun kafin su isa asibitin Haj murjanatu ta Kira Dr Balarabe tasanar dashi suna hanya dafatan Yana asibitin domin ciwon mujaheeda ya tashi. Ya tabbatar Mata da cewa yanzu yake Shirin tashi Amma dole zai tsaya ya Jira zuwansu.

Isarsu asibitin babu bata lokaci aka ba mujaheeda gado sannan Dr Balarabe ya Fara bata taimakon gaggawa.

Ayayinda Haj murjanatu ta koma waje ta Sami kujera ta zauna,hawaye ta samu kanta da fitarwa kwarai matuka tana matukar Jin tausayin yarta agame da lalurarta Wanda hakan Yana daya daga cikin dalilan da suka sa take tsaye da Sanya farinciki azuciyar mujaheeda bata kaunar duk wani dalili dazaisa mujaheeda damuwa,

Hakan yasa tasha alwashin jiyar da ita dadi da gatan da zaisa natsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa.

Hakanan ta Sami kanta da addu’ar Allah yasa ba dalilin abinda yafaru akan Kayan lefen ta bane,Wanda tasan laifinta ne.

Ahankali ta Ciro wayarta daga cikin Jakarta, ta danna ta Kira Alh Mustapha bugu daya ya dauka Jin muryarta cikin damuwa yasa ya Fara tambayarta abinda ya faru , ahankali ta sanar da Shi suna asibiti da mujaheeda ciwonta ya tashi.

Cikin damuwa shima ya kashe wayar ya aje komai ya baro kamfanin ya taho asibiti.

Harya karaso asibitin mujaheeda tana nan inda take har zuwa lokacin bata farfado ba.dr Balarabe da wasu likitoci guda biyu sune akanta.zuwa lokacin kuwa Haj murjanatu taci kuka har taba uku lada, idanunta sunyi jawur.

*****

Alh Mustapha labaran ya zauna kusa da Haj Murjanatu Yana dubanta, sannan yace ” meya faru da mujaheeda wani abin ya bata Mata rai ne ,,ko kuwa dai hakanan ciwon ya tashi, abinda ya dade bai tashi ba.”

Tadan yi jim gami da muskutawa sannan tace ” Babu abinda ya faru , hakanan naji ihunta ko kafin na shiga harta sume” ta Karasa magana tana kokarin goge hawayen da suka Fara fitowa daga idanunta.

Alh Mustapha labaran ya girgiza Kai yace ” Allah ya bata lafiya ” asanyaye ta amsa ” Amin ya Allah.”

Sai bayan issha’ I sannan Allah ya nufa mujaheeda ta farfado ,idonta nakan mahaifiyarta wacce take ta murnar ganin ta dawo hayyacinta, ta dauke idonta akanta tana runtse idanunta ,kalaman Taufiq sune suke yawo a kwakwalwarta.

Hakan yasa idanunta suka cika da hawaye .Alh Mustapha labaran ya Lura kwarai da hawayen dake fitama mujaheeda, ahankali ya nemi bakin gadon ya zauna Yana kallonta gami da Kiran sunanta, bata amsa ba sai hawaye da ya cigaba da wanke fuskarta.

Yadan Matso kadan kusa da ita Yana cigaba da kallonta sannan yace ” mujaheeda menene? Jikin ne? Ko wani abun Yana damunki ne ?”.
Haj murjanatu ta taso ” me zai dameta daya wuce ciwo” ya waiwayo ya dubeta yace ‘ kila bakiga damuwar da ke cikin kwayar idonta bane ,ko Kuma kingani kin zabi ki kauda Kai akan damuwarta ta ” ta dubeshi sosai tace ” Akan me Zan juyama damuwarta baya ,bayan duk duniya bani da wata damuwa da ya wuce damuwarta.”

Asanyaye cikin galabaitacciyar murya mujaheeda tace ” idan har damuwa damuwarki ce , da baki zama sanadiyyar damuwar tawa ba.”

A gaggauce Haj murjanatu tace ” nice sanadin damuwarki mujaheeda?” Ta Karasa magana idanunta na kafe akanta.

Ta jinjina Kai alamar hakane. Hakan yasa Alh Mustapha labaran ya dubi mujaheeda cikin kulawa yace ” ki kwantar da hankalinki ki gaya min abinda ya faru.”

Cikin kuka sosai mujaheeda ta sanar da Shi duk abinda yafaru da Kuma hukuncin da Taufiq ya dauka akan hakan.ta karasa magana cikin kuka tana cewa ” Kin fi kowa sanin irin son da nakema Taufiq Amma kin kasa dannems zuciyarki tsanar sa balle har ki tayani sonsa, shin meye illar Taufiq me yasa kike raina arzikinsa kike ganin tamkar bai dace dani ba , bayan NI kadai nasan irin dacen da nayi da samunsa,meye na dole sai kin muzanta Shi.

To abinda baki sani ba shine Taufiq zai iya jure ki wukakanta Shi ki ci masa mutunci kiyi . masa komai amma bazai taba jurar ki wulakanta masa yan’uwa ko iyaye ba, yasha gaya min matukar abinda kike masa ya wuce Kansa ya fada Kan iyayensa Ko yan’ uwansa to zai iya hakura dani har abada.”

Ta Kara tsare mahaifiyarta da Ido sannan ta cigaba da cewa ” Dalilin da yasa kenan dana dawo na tadda abinda kikayi akan lefen hsnkalina ya tashi saboda bansan irin abinda kika gaya masu ba, har sai da Taufiq ya kirani ya Kuma tabbatar min da wulakancin da kikayi ya Kuma gaya min ya hakura na gaya Miki kije ki aura min Wanda kike so Wanda zaki fi samun natsuwa dashi.bsyan kinsan duk duniya bani da wata natsuwa sai da Taufiq, bani Kuma da Wanda nake so nake Samun farinciki agunsa sai Shi .Na rantse idan ba Taufiq ba babu wani da namiji dazan iya aure sai dai na zauna babu aure har na koma ga Allah.”

Haj murjanatu ta kasa magana kanta na kasa har zuwa lokacin da Alh Mustapha labaran ya tashi ya dawo kusa da Haj murjanatu ya tsaya Yana kallonta , ta dago ta dube Shi tace fuska atamke ” Menene Ka tsare ni da Ido, don kawai an kawo kayan lefe na ce basuyi ba shine zai bullo da wannan maganganun na banza dama Yana neman na tafiya ne ,Kuma bai Isa ba ba’ a haife Shi ba aurenki dashi ya Zama dole.”

Alh Mustapha labaran yace ” Auransu ya Zama dole amatsayin ki na wacce zata ce dole ayi ko me? Taufiq shine yake da ikon dazai auri mujaheeda shine Kuma yake da ikon da zaice bazai aureta ba , saboda haka wannan izzar da kikeyi babu inda zata kaiki awannan Karon ya Zama dole ki sakko kije ki gyara abinda kika bata matukar kina son kwanciyar hankalin yarki,”

Ta harzuko ” To me zanyi ?” Ya gyara tsaiwarsa sannan yace ” Ki nemi Taufiq ki bashi hakuri, sannan ki fita acikin salon zubar da kima da kika shiga ki rungumi abinda Allah ya kaddaro acikin rayuwar yarki kija girma da mutuncinki tun kafin ki rasa su awajen Taufiq, ki sani ke surukace wacce kike dai dai da matsayin Uwa awajen Taufiq,duk wadannan abubuwan da kikeyi ba zasu haifar Miki da da me Ido ba.
Ya kamata ki dawo cikin Tunaninki zuwa yanzu dai ko ba abinda kika karama Taufiq na muzantawa to ya sani wasuma sun sani cewar bai Miki ba , Baki sonsa zaki aura masa yarki don dole ne don tana sonsa Kuma lsifinsa daya ne don kina ganin ajinsa bai Kai ajin mujaheeda ba.”

Haj murjanatu tayi shuru nadan wani lokaci sannan tace ” Nice Zan nemeshi na bashi hakuri” ya jinjina Kai yace ” kwarai da gaske ammafa matukar kina son mujaheeda ta tashi daka Kan gadon asibitin nan ,ta Kuma Sami lafiya da Kuma mallakar abinda take so”.
Haj murjanatu ta girgiza Kai tace ” Gaskiya bazan iya zuwa naba Taufiq hakuri ba, ai Bama zai yuwu ba.”

Mujaheeda ta runtse idanunta zuciyarta na wani irin tukukin ciwo lokaci daya maganganun Haj murjanatu sukasa ta Kara birkicewa nan da nan idanunta suka Fara kafewa numfashi ya Fara Mata wahalar fita , gaba daya sukayo kanta daga bisani Àlh Mustapha labaran ya fice yaje ya Kira likita .
Tambayar farko da likita ya Fara yi itace ” Meya faru wani ya bata Mata raine” babu Wanda ya bada amsa acikinsu har likita ya Gama dubata yayi Mata allura wacce cikin kankanin lokaci bacci ya kwasheta.

Likita ya dubi Àlh Mustapha labaran da Haj murjanatu yace ” Gaskiya dole fa Ku dinga kulawa Kan abubuwan da zasu dinga sa ta adamuwa saboda damuwa itace babbar hanyar tashin ciwonta ,Kuma ahalin yanzu ba’ a bukatar yawaita tashin ciwon saboda hakan zai. Iya kaimu da dole sai anyi Mata aiki a zuciya , saboda haka don Allah a Kula ”
Babu Wanda ya iya magana har ya Gama maganganunsa ya fice.

Sannan Àlh Mustapha labaran ya dubeta yace ” Har yanzu kina nan akan bakanki na cewa ba zaki ba Taufiq hakuri ba ya janye maganarsa ko kuwa?”

Tayi Jim duk wata damuwa ta gama mamaye ta komai ya tsaya Mata , shin me zai faru da izza da isarts matukar tabs Taufiq hakuri? Yaron da bai Isa ba ba’ wani ba ba dan wani ba Shi zata je taba hakuri don kawai ya auri yarta.

Ta dago Kai ta dubi mujaheeda da tayi nisa cikin bacci ta dubi irin ramewar da tayi farat daya kamar ta shekara tana jinya. sannan ta dawo da idonta kasan dakin ta rasa abinda ke Mata dadi . Wannan wace irin masifa ce ? , Karo na farko kenan da taji ta Kara tsanar Taufiq tsana me yawa, domin ayau ta hango abinda bata tabs hangowa ba , na cewa tabbatar Taufiq zai iya rabata da yarta matukar ta cigaba da yi masa irin wannan son da take masa.

“Ke nake Jira inji abinda kika yanke” cewar Alh Mustapha labaran, ta waiwayo a hankali ta dubeshi tace ” Kai ba zaka iya zuwa Ka Sami mahaifinsa kuyi magana ba ka bssu hakurin?” Ya dubeta sosai ysce ” Kin taba ganin Wanda yayi laifi daban Wanda zai bada hakuri da ban , ta yaya zanje na basu hakuri bayan bani nayi laifi ba.”

Ya karasa magana Yana kauda Kai gefe saboda Shi Kansa yau Yana son ganin karshen izzar Haj murjanatu Yana son taji abinda ake ji idan Ka muzanta agaban wani.

Ta aje numfashi ahankali sannan tace ” Naji Zan kirashi awaya nasanar masa halinda mujaheeda take ciki ,nasan duk fushin da yayi idan yaji tana kwance a gadon asibiti zai taho ya dubeta don shima yasan lalurarta, saboda haka idan yazo sai muyi maganar.”

Alh Mustapha labaran ba haka yaso ba Amma baya son ta gane cewar shima Yana da ra’ayi acikin maganar hakan yasa baija ba yace ” shikenan idan kina ganin hakan ne yakamata ”
Batace komai ba ya dubi agogon dake daure a tsintsiyar hsnnunsa karfe goma sha daya na dare ya dawo da kallonsa gunta yace ” kina bukatar wani abu ne , don ina Jin Zan tafi gida dare yayi,”

Ta gyada Kai tace ” komai akwai vabu wata bukata kana iya tafiya ” ya matsa kusa da mujaheeda ya yi Mata addua ya tofa Mata a fuska sannan ya juya yayi sallama da matarsa ya tafi.

Saida ya natsu acikin mota kafin ya tada motar ya fito da wayarsa ya danna ya Kira Taufiq bugu biyu acikin na uku ya dauka cike da girmamawa ya gaishe shi , tun rana yakesa ran Samun Kiran Àlh Mustapha labaran Amma shurun da yaji shiya tabbatar masa da cewa mujaheeda bata sanar da kowa abinda ya faru tsakaninsu ba.

Alh Mustapha labaran yace ” Taufiq yakamata ace zuwa yanzu kasaba da halin Haj be kamata Ka dinga juyawa kana kallon abinda take yi ba shekara hudu kayi kana neman auren mujaheeda babu abinda batayi ba yadda Ka jure Ka yi hakuri haka nake son Ka cigaba da hakuri , domin dai akwai tarin kalubale acikin wannan tafiyar dole saika jure, don haka maganar Ka fasa aure Ka ajiyeta a gefe domin adalilin maganar da Ka fadama mujaheeda yanzu haka tana kwance a asibiti ciwonta ya tashi babu yadda take.”

Gaban Taufiq yayi mummunar faduwa yayi saurin mikewa tsaye yace ” ciwonta ya tashi ” Àlh Mustapha labaran yace ” Kwarai da gaske kaima Kuma kasan hakan zai iya faruwa ,tunda kafi kowa sanin duk irin halin ko’ in Kulan da mujaheeda take nuna maka tofa kasani tana sonka so me tsanani wannan halin datake nunawa cikin irin halayenta ne da babu Wanda zai iya canjata Mata.

Amma ina son kasani mujaheeda tana matukar sonka sannu ahankali wata rana kana iya maida ita yadda kake so, wannan sangartar da shagwaba da raguwar tarbiyyar data ke dashi duk zaka iya canjata,” Taufiq ya numfasa yace ” nima bacin rai yasa nace na fasa domin har yanzu ban sanar da mahaifana cewa ga abinda na yanke ba saboda nasan KO kowa ya yarda Abba bazai yarda ba,”

“Nima nasan Alh Yusuf lamido bazai amince ba shiyasa ban damu ba ” Taufiq yace ” sha biyu saura ne yanzu na dare yanzu Zan je asibitin na dubata.”

Alh Mustapha labaran yayi saurin girgiza Kai yace” Aah kada kaje ” a hankali yace ” me yasa Alh ” a hankali Alh Mustapha labaran ya Gama gaya masa komai ba maganar hakuri da yake son Haj murjanatu ta bashi KO ta dawo hayyacinta da Kuma abinda ta fada ya Kara da cewa ” ina son ta zo har gida ta baku hakuri hakan zai karya lagwanta zaa Sami sauki ko yayane saboda haka Kota kiraka Kada Ka sake Ka dauka Ko number ta canja idan kaji muryar ta to Ka kashe wayar hakan zaisa ta yarda tazo har gida ta bada hakuri , kayi hakuri da zuwa asibitin har sai ta zo gida ta bada hakuri.”

Taufiq yayi Dan murmushi tikisa Haj murjanatu da bashi hakuri lalle Shi Kansa zaiso ganin hakan ” Ka fahimceni” cewar Alh Mustapha labaran Taufiq ya amsa da sauri ” Na fahimceka shikenan hakan za’ayi Amma don Allah Ka dinga sanar dani halinda mujaheeda take ciki a asibitin saboda na Sami natsuwa” yayi murmushi yace ” Kada kadamu.”
Daganan suka yi sallama cike da mutuntawa da girmamawa.

Alh Mustapha labaran yaja motarsa zuwa gida zuciyarsa cike da tunanin irin wannan badakalar dake faruwa sai kace akan Haj murjanatu aka fara neman aure ya rasa irin tunaninta. Shi Kansa ya kosa ayi ayi auran nan ko hankalin kowa ya kwanta. Sai dai abinda bai sani ba shine yin auran nema zai Zama sanadiyyar ràshin kwanciyar hankalin.

DAGA TASKAR YAR GIDAN IMAM.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 5Nima Matarsa Ce 7 >>

3 thoughts on “Nima Matarsa Ce 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×