Skip to content
Part 1 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

DEDICATION

In dedication to all Kanuris around the globe.

And to nisful hayatee, qurratu ayniy the woman behind my success, my Mom my wonder woman, without her by my side I won’t be where I am today thanks for everything Mammah. Allah ya albarkaci gabanki da bayanki ya kare mana ke a koina, lafiya da nisan kwana, Hayatee.

Zaune take a gaban madubi tun d’azu da ta fito wanka d’aure take da towel a jikinta, kallon creamy soft skin d’in ta takeyi a zahirance. Amma a bad’ini tunani mai zurfi ta tafi, yayinda fuskarta ta cika da mayalwacin murmushi wanda ba komai ya assasa shi ba face ganin burinta yana kan gab’ar cika a yau d’innan.

Tun d’azu take tsaye a kanta amma bata sani ba saboda zurfin da tayi a duniyar tunaninta, dafa kafad’arta Hajjah tayi hakan ya sa ta juyo a d’an firgice ganin wacce ta tab’ata ne ya sanya ta tale baki a shagwab’e tace ” Alah kàrwùkámmà! ( kin tsoratani!)” Haratarta tayi kafin tace ” kin zauna tun d’azu a nan ai dole kiji tsoro”.

K’aramin bakinta ta tura sama ba tai magana ba Hajjahn ce tace “wai kin tashi kin shirya ko sai yazo ya ganki haka a zaune?”. Dafe k’irji tayi tace “ina jin tsoro a k’asan raina, I don’t know what it means” dafata ta kuma yi cikin muryan rarrashi tace ” ba abunda zai faru habibtie, ki kwantar da hankalinki”. Gyad’a mata kai tayi kana ta janyo cream ta fara shafawa jikinta.

Cikin doguwar riga nude color ta shirya, coffee brown d’in veil ta yafa a kanta wanda hakan yai exposing brown well oiled hair d’inta. Turaruka ta shafe jikinta dashi kafin ta fito, a parlor ta tarda Hajjah zama tayi kusa da ita tana d’aura kanta a kafad’anta tayi shiru. Patting bayanta tayi a hankali a kunnenta tace ” Álà kámbò ( Allah mai girma), yau Lele ce take jin tsoro?” girgiza kai tayi kawai amma bata tanka ba.

Janta tayi da hira har sai da ta d’an sake kad’an, suna zaune a wurin akai honk a gate baa jima ba motar ta shigo gidan. Hakan nema ya sanya ta tashi zaune, Hajjah tace ”
ákkònjú ( ga shi nan yazo), ki tafi a natse kar ki bada mata ” dafe k’irjinta da ya k’ara bugu daga shigowarshi gidan tayi tana cewa ” in shaa Allah Hajjah, you too should pray for me”. Cewa tayi ” you have my blessings dear, Allah ya sa a dace”.

A dai-dai lokacin wayarta yai k’ara tana dubawa sunanshi ne ke yawo a screen d’in picking tayi tareda mak’ala wayar a kunnenta. Cikin kamammiyar voice d’in shi yace ” I’m outside”, kafin ta samu zarafin amsawa ya katse hakan yasa ta mik’e a natse ta kalleta ” ya na waje barin ganshi”, jawota tayi tana cewa ” a haka zakije babu abun tab’awa?, ki d’aukan masa ko ruwane mana”.

Girgiza kai tayi tace ” No lemme see him first, may be ma ciki zan shigo dashi “, ok tace alamar fahimta yayinda ita kuma ta fita zuwa wajen.

A zaune a cikin motarshi yake yana mai kallon entrance door d’in, tsaki yayi ganin bata fito ba kuma ya tabbatar ta ji zuwanshi ba dai tana nufin shi take jira ya shiga daga ciki ba?. Hakan ya sa ya d’aga wayar shi number ta dako saving baiyi ba ya latso ringing biyu ta d’aga ba tareda ya bata damar magana ba don ko sallama bai mata ba yace ” I’m outside” ya katse wayar ya na cewa ‘ I’ll surely deal with you today, stupid!’ In a bitter tone.

Ko bayan kiran nata sai da tayi kusan 3 mins kafin ta fito, yayi tsaki ya gaji don gani yayi kamar 30 tayi a ciki. A tsanake ta doso shi zura mata idanu yayi trying to figure how could she be beautiful yet d*mb, he knows she’s so clumsy and spoilt but never thought she can stoop this low. ” Vanity” he muttered!.

Fitowa yayi ya jingina da motar har ta k’araso gabanshi, sallama tayi kanta a k’asa ya amsa yana kallonta k’yar. “Ndâ dəbdu?” (Barka da yamma), hannu ya d’aga mata ” hey I’m not here for pleasantries, ni sa’anki ne?” Jikinta ne yayi sanyi girgiza kanta tayi yace ” open your mouth and talk jare!, how old are you?”. Ya sake jefa mata wata tambayar.

Muryarta na rawa ta bud’e baki zata bashi amsa ya tareta da cewa ” yaushe aka haifeki da har kika fara tunanin luring guys into your nest?, lalacewa da rashin kunyarki har ta kai haka are you this cheap?” D’agowa tayi da sauri jin abunda yace sai dai ya sake dank’aro wata maganar ” yes ba lalacewa bace?, as small as you are you know how to ask a guy out! shameless you!”.

” It’s not a sin nor a crime!” Ta furta tana murgud’a bakinta, wow ya furta yana cewa ” you are really shameless as I said”. A hankali tace ” I’m not, saboda ko a musulunce ba haramun na aikata ba Sayyidatuna Khadeejah bint Khuwayleed asked our Noble prophet Muhammad ( sallallahu alaihi wa sallam) out and he respected and married her ban kuma tab’a samun labarin ya kalleta as shameless or cheap as you are saying ba, rather he honored her request har yai wafati yana jinjina ma girma da darajarta so I’m not cheap I just love you that’s all I know”.

“Bravo Sheikha Nadeefah Yusuf Yerwa, you are amazing you know?. so you have grown wings like this bamu sani ba, well for your information I Burhaan Abdallah Yerwa can’t love you. Ohh my bad!! I won’t love you and I don’t have any business regarding love with you and ina so wannan ya zama karo na k’arshe that you will ever make such a silly request from me” Ya furta cikin d’acin murya.

Dukda kalmar ta daketa sai dai ta samu zarafin shanyewa tace ” what are we gonna do about it then?, as you can see I can’t let go of you” trying to provoke him more don kallonshi a hakan dad’i yayi mata yace ” Nadeefah!!! I’m warning you to stay outta my lane, ina d’aga miki k’afa ne saboda  àwágənân kúràngənà ( mu cousins ne) if not da kinga asalin color na I don’t love you ke I’ll never love a cheap freaking ass like you hár àwàdá!!(never) get this to your skull!”

Ji tayi tamkar ya jefa mata k’arfe a zuciya kafin ta gama recovering yace ” and mind you in kika sake zancen nan ya fita ga family then I’ll surely do the unthinkable that you’ll definitely regret knowing me. Now, lemme have your phone” mik’a masa tayi cikin rawan jiki. Juya wayar yayi kana yace ” IPhone14 pro max!, we are using same phone dole ki raina ni now, open it for me ouch what’s the passcode?”.

Gaya masa tayi ya d’ago da sauri yana kallonta jin ta ambaci DOB d’inshi, no doubt birthday d’in shine pass code d’in ta lallai dole yaci ubanta la’ada ciki ba waje ba. Bud’ewa yayi pic d’in art d’in ta na sunset da ta saka as wallpaper ya na shiga idanunshi. Message box d’inta ya bud’e nan ya tarda drafts na messages d’in da take turamai tayi canceling tsaki yayi yace ” delete these sh*ts!” Kallonshi tayi ta na mai jin abunda take ji a kanshi ya na hauhawa despite the fact that mutuncinta ya gama ci yanzu haka. She don’t know why!

“I said delete it ” shine ya dawo da ita daga dreamland d’inta, hannu ta kai zata amshi wayar ya dakatar da hakan don hannunshi ya sa ya rik’e nata tamau da hannunshi dake had’e da nata ya goge duka messages d’in har wanda ta tura masa yau, bai tsaya nan ba har number shi da tayi saving da ” Aorta ” da emojis sai da ya goge har icloud kafin ya sakin mata hannu. Nashi wayar ya d’auko ya goge message d’in nata yace.

” Yanda aka goge messages d’innan haka na goge each and everything that happened today, sannan kika sake zancen nan ya fita ki kuka da kanki, I’ve said it and I’ll repeat it for the last time I don’t have and don’t need anything to do with you, loving you will be the last mistake I’ll ever do stay off my lane” yana furta hakan he spit on the ground kafin ya shige motarshi ya jata da mugun gudu a sukwane mai gadi ya bud’e don daga ganin yanda ya ja kasan ba lafiya. It hit so hard bata tab’a sanin haka rejection yake ba sai yau.

She want to cry her heart out loud, wai shin wani tsautsayine ya sa ta fara son shi ne? Shin meyasa bata cigaba da had’iye abunda take ji ba ne?, wai ma meya zugata ta tura mai message yau?. Tabbas ba wanda ya kaita ya baro sai banzar zuciyarta wacce garin biye mata gashi bata samu rabin abunda take so ba saima b’arewar kambun darajarta ga idanunshi. Abun haushi ma maimakon ta ji tsanar shi da na zuciyarta a take taji wani yanayi mai dad’i yana ratsa zuciyarta yanda kasan an mata bushara.

A sanyaye ta cira k’afarta ta jashi zuwa cikin gidan ta na mai sak’e-sak’e, har zata shiga d’akin Hajjah sai kuma ta fasa don bata san mai zata gaya mata ba. Wani d’aki ta nufa wanda yake shak’e da kayan art kala-kala, veil d’in ta d’aura a kanta ta nufi board d’in dake a tsaye colors, paints da brushes ta ajiye a gabanta. Murmushi tayi ta runtse idanu a take moments d’in d’azu ya dawo mata tar a k’wak’walwa, hannunsu da ya had’a d’azu ne yake ta replaying a mind d’in ta zane ta fara yi cikeda k’warewa har lokacin murmushi ne kwance a face d’in ta.

Driving yake cikeda takaicin abunda ya faru yau, tsaki ya k’ara ja yayinda k’asan ran shi yake masa zafi ga mugun tsanarta da yai masa katutu ya tsaya masa a k’irji. A dai-dai junction d’in street d’in yayi kicib’us da ita, tana shirin shiga layin da motarta. A take k’irjinshi ya buga yayinda b’acin ran shi da ya kwaso ya fara washewa yana cikewa da farinciki, slowing down yayi yana bin ta da ido amma cikeda basarwa don in ba shiba babu wanda zai iya cewa ita yake kallo.

Suliem Aliyu Yerwa kenan! Kyakkyawa dai-dai misali, bak’a ce irin na cikakkun kanuri kana bata da tsawo sosai she has the perfect shape and figure. Suliem macece mai aji sosai hakaza bata da kwarafniya irinta Nadeefah da takeda rawar kai ga wasa da dariya while Suliem is a no nonsense person bata barin ta kwana, kuma bata d’aukar raini ko ta sisin kwabo ita ko Lele damo ce sarkin hak’uri ga sauk’in kai da muamala wanda yana d’aya daga abunda Burhan ya tsana a tattare da ita gani yake tamkar bata da aji da kamun kai.

Yanda sukeda banbancin halayya haka ma sukeda bambancin kamanni don ita Lele kyakkyawa ce ajin farko irin matan da ake musu lak’abi da” hurul in on earth” duk wanda ya kalleta sai ya kuma kallonta har a cikin turawa balle a k’asarmu ta gado kana fara ce tass though suna da haske saboda jinin fulanin da sukeda shi amma hasken Lele ya banbanta saboda jinin larabawa da take da shi a jikinta.

While Suliem is a bit chubby Lele is not she’s so slim with slender un curvy body, wato matan da ake kira da 1 ba kuma ba k’asa sai dai ta iya d’aukan wanka na fitar hayyaci she’s a fashionista, hakan yasa Burhaan kiranta da slay queen while a zahiri she’s nothing like that lifestyle d’in ta kenan tana son gayu.

“My own weakness!” Yai muttering under his breath, cikeda ajin da a jininta yake ta shiga layin ba tareda ta nuna ko alamar ta gan shi ba. Yarfe hannu yayi ya ja motarshi zuwa gida, yana mai jin nishad’in ganinta a yau d’in a take a wurin ya kwashi takaicin Lele ya watsar gefe don ganin Suliem kad’ai ya ishe shi warakar ko wace damuwa

Jan motar tayi tana furta ” arrogant ass” harda tsaki dogo, bata san dalili ba but ita a rayuwarta Yah Islaam haushi yake bata saboda muguwar girman kan da yake dashi sannan ga nuna isa da rashin kyautata mu’amalar dake tsakaninsu dashi as cousins. She see no reason a girl as fine as Lele will ever like a guy like him, tsaki taja a karo na barkatai tun bayan da ta ganshi. Honk tayi security ya bud’e ta shiga da motarta ba tareda ta kula gaisuwar da yake korowa ba, sai hannu da ta d’aga masa kawai.

Da sallama da shiga parlorn babu kowa a ciki sai TV dake aikin karad’i shi d’aya, wucewa tayi zuwa small parlorn Hajjah don tana da tabbacin samun su a can. Hajjah kawai ta tarda zaune rik’e da carbi tana kallon NTA, zama tayi tana cewa ” Hajiyar Allah barka da yamma” yawwa ta amsa tana mai tambayarta mutan gidan. Fira suka d’an tab’a ba laifi har ta kai kusan 1 hour babu Lele ba dalilinta hakan yasa ta cewa Hajjah ” Lele fa?”.

Tab’e baki tayi kafin tace ” tana can fira yayi dad’i tun d’azu, baku had’u ba halan ko garden ta kai shi?”. Girgiza kai tayi kana tace ” Aa, bamu had’u ba waye yazo hala?”. Amsa ta bata da ” yayanku Islaam ne ” ware idanu tayi a mamakance don taga Islaam ai kenan daga nan yake?, toh ai ya wuce ita Lelen aina ta tsaya. Cewa tayi ” to ai shi ya tafi don mun had’u a junction, Ita Lelen ta tsaya aina ne tunda ban ganta a waje ba”.

Hajjah tace ” toh k’Ila ciki ta shiga “. Tashi tsaye tayi tana cewa ” barin shiga wurinta tohm”. ok tace tana mai maida hankalinta kan TVn, komawa baya tayi zuwa room d’in Lelen babu ko alamun mutum a ciki haka ma bedroom d’in Hajjahn. Art room d’in ta da yake can gefe ta nufa, A can ta iske ta tsaye rik’e da k’ugu tana kallon zanen har lokacin tana mai murmushi.

Kallon zanen tayi sai dai bata gane kan komai ba kasantuwar bata kammala ba, k’arasawa tayi gabanta tareda dafata a d’an firgice ta waigo ganin Suleim ce yasa ta sauke ajiyar zuciya tace ” Lovie yaushe kika shigo” amsa ta bata da ” just a little while ago, Hajjah tace your man was here me ya faru”.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace ” Yau na samu na amayar da abunda ya dad’e yana damuna and… “Sai tak’i k’arasawa sai ma murmushi da ta saki hakan yasa Suleim cewa ” and what? Did he accept it?” Bata tanka ba instead gaban board d’in ta ta nufa paint ta d’auka ta cigaba da abunda takeyi hakan ne yasa Suleim furta.

“This thing that you are blushing says it all, so that arrogant fellow isn’t that hard to get?” Girgiza kanta tayi yayinda ran ta ya b’aci da jin sunan da Suleim take kira  ‘Aortan’ ta ba, tun ba yau ba zuciyarta kanyi zafi idan ta aibata Islaam. Sai dai ba yanda ta iya don tasan tabbas gaskiya take fad’i but zuciyarta ta kan gagara jurewa ko misk’ala zarratin indai kanshi ne.

Cikin raunin murya tace ” he didn’t Lovie!!, instead I was REJECTED! yace shi ba ajina bane ” tana murmushi mai ciwo. Tsaki taja da sakin ashar tace ” har shine zai ce shi ba ajinki bane?, uwar meye abun so da burgewa tattare da shi da har zai yi tunanin shi d’in daban ne da maza? Ko an gaya masa ba alfarma kikai masa da son shi d’in ba?….” Ta k’are maganar da tsaki mai tsawo.

Ta d’aura da cewa ” ni wallahi ban ga abun rikicewa a kanshi ba da har ki ka mace masa. Ni dai ina mace kamar ki da kyau da maza suke rikicewa a kai ai sai na zab’a na dirje balle har in yarda in zubda hawaye kan ya Islaam ba!”. Yanda tayi maganar sai da Nadeefah ta k’yalk’yale da dariya don ta fad’i son zuciyarta ne kawai amma matan da suka fisu ma sun mutu akan Islaam, hakan ne ma ya sa shi tunanin shi d’in wani abu ne har yake girman kai.

Amma ai Islaam ya wuce gaban tunanin duk wata mace mai ji da aji da kuma isa. Islaam ingarman namiji ne da kowace ‘ya mace take burin mallaka a rayuwar ta, ta kowani b’angare ya kai inda baa tunani. Ga kyau, physique, aji ilimi both side, ga kud’I ga iya wanka. Kai ita a duniyarta bata tab’a ganin mutum irin ya Islaam ba, matsalar da kowa yake kuka da shi itace girman kai da kuma rashin jan ‘yanuwa a jiki hatta k’annenshi da suke d’aki d’aya.

Da yawan mutane suna masa kallon mai mugun hali, ciki harda Suleim hakan ne ma yasa take ganin wallan Lele akan son da take masa har bata ganin rashin dacewarsu da juna. Lele is a delicate flower and is so full of love and life like a spring while he’s so opposite of her, he’s so harsh and toxic.

Lele ce ta katse tunanin da suka tafi tace ” let’s be fair and just to ourselves, ni dake mun san yafi gaban kwatancen mu he’s far beyond all we can think of, and ya cancanci duk wata isa da aji ya kuma cancanci a so shi har ayi fatan zama dashi na dindindin sai dai in ba’a samuba”.

Gyad’a kai tayi tana cewa ” ban miki musu ba but you are too far from stooping down to his level, Lele take a look at yourself first wallahi you don’t deserve him you deserve someone better!”. A hankali tace ” why will I go around wondering and looking for better when I have the best?, Lovie he’s the best I can think of!”.

“He rejected you fa!?” Ta furta da mamaki gyad’a mata kai tayi kana tace ” yes,and that makes me love and respect him more, and I won’t stop har sai na same shi “

Tsaki tayi tana figar jaka ta fita ganin maganar bata da amfani duk kuma yanda taso tayi convincing d’inta ta toshe kunne. Ita fa ko a yanda take tafi k’arfin wulak’ancin namiji balle ace tana da rabin kyau irin na Lele. Ko sallama ba tayi wa Hajjah ba taja motarta zuwa gida cikeda jin haushi wai don ma bata san wulak’ancin da shi Burhaan d’in yayiwa Nadeefahn bane da shakka babu sai ta ji tamfar ta shak’e shi ta huta.

Murmushi tayi jin k’arar fitar motarta a hankali ta furta ” baki san zafin so bane dad’in ta kawai kika sani, and that’s because Yaya El-sadeeq is an easy going person”. Sai kuma tace ” ahh….I too dey pity my brother sef irin wannan hawa haka!” Dariya ta sanya tana komawa ga aikin da ke gabanta, bata fito ba sai da aka kira magrib d’akinta ta nufa don gabatar da farillah….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Nisfu Deeniy 2 >>

3 thoughts on “Nisfu Deeniy 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×