Skip to content
Part 10 of 11 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

She Is Back

Runtse idanu ya yi yana mai jin damuwa ya yi mai yawa, Abba ne yazo ya amshi Hajjah a hannun shi yana cewa ” I’ve told you in wani abu ya sameta sai nayi sharia da kai, now ka fita ka nemo min ita” ya k’arashe a tsawace. Mommy Kuura tace ” Yaa abi a hankali dan Allah in ya fita yanzu ina zai fara nemanta?”.

Cewa yayi ” duk inda zai shiga ya shiga damuwarshi ce ai shi ya san inda ya ajiye ta”. Daga haka ya wuce da Hajjah da duk ta susuce hankalinta ya tashi, su Zulfaa ma anci kuka ita da Suliem idanun nan luhu-luhu. Musamman ma Suliem ta kira number yafi sau adadi amma baa picking, har ta kai ga ta daina shiga ma saboda yawan kiran da ake ta mata. Ga kiran da Elsadeeq yake ta jero mata ta kasa picking, don bata a nutsuwar da zata iya d’aukar wayar har message ya turo yana tambayarta ko yayi laifi ne ko dubawa ba tayi ba ta notification bar ta ga message d’in.

D’an saita kan shi yayi yana komawa motar shi, Farhan ne ya biyo shi motar ya shiga d’ayan side d’in. Yana zama yaji ya zauna akan abu, hannu ya sa a inda ya zaunan wayar Lele ce da take jone a jikin power bank d’in ta.

Yayin da misscalls rututu su kai masa sallama, kallon Islaam da yake sharara gudu har sun kai gate d’in fita daga estate d’in yace ” Dude ina ka baro ta ne wai? ba zan tambaye ka dalilinka ba don nasan baka abu sai da solid reason but babu wani hujja a duniyar nan that can justify what you just did”.

Yawu ya had’iye yana mai sak’a abubuwa a ran shi cewa kawai yayi ” ba zata b’ace ba, ba kuma abinda zai faru da ita In shaa Allah ” ajiyar zuciya ya sauke kawai yana kallon hanyar da suke bi, ganin kamar bai san inda za shi bane ya sanya shi cewa ” mu je muyi reporting a PS kawai “.

Har zai yi gardama don ya san definitely shi zasu yi blaming, and he’s not ready for their tantrums sai kuma yace ” ok ” kawai yana karya mota tuni nearest PS. Ko da suka je can d’in abunda ya gudan ne ko ya faru, rufe shi sukayi da fad’a bai ko kalli inda suke ba takaici ya sa DPO cewa ” ba zamu sake ka ba, we’ll press charges against you saboda kai ne no. 1 suspect d’in mu”.

Kallon banza ya bisu da shi arrogantly yace” ni zaku rufe or who?”. D’an dafa shi Farhan yayi a hankali yace ” Dude please”. Kana ya juya ga DPOn yana cewa ” Ba ma sai an kai nan ba yallab’ai shine fa wanda zai aureta kuma ko babu aure k’anwar shi ce kaga babu ta inda zai salwantar da rayuwarta y’ar rashin fahimta ce aka samu ba komai ba”.

DPO yace ” tunda shi zai aureta kuma abune na gida toh ina ganin babu buk’atar mu shiga cikin abun sai ku magance matsalar in-house zai fi, Allah ya bayyanata you can excuse us zamu fita duty”. K’ask’antacce kallo ya bishi dashi yana shirin magana Farhan yayi saurin cewa ” ba haka bane y’allab’ai consider us please, the life of our sister is at risk”.

Cewa yayi ” ai naga baku buk’atar sa hannunmu a ciki”. A gaggauce yace ” no sir, ba haka bane kawai dai kamawar da kace ne yayi nauyi” tsaki yayi yana tashi daga kujerar sosai ran shi ke b’aci, ji yanda Farhan yake zubar musu da mutunci har haka. The way he’s begging this low ranked officer kamar basu ke da manyan officers na k’asar ba one call kawai ya wadatar duk inda take sai an nemo ta, amma ba zasu yi haka ba sai in abun yaci tura.

DPO yace ” in dai har zamu saka hannu a lamarin nan then he must be arrested ASAP saboda babu yanda zaayi mu k’yale suspect a cikin case ya tafi scotfree until he’s proved innocent amma ni I’m doing this grace na k’yale ku ku tafi not because ina tsoron wani abu da zai faru but saboda naga darajarku tafi gaban hakan but my condition stands in kaga na shiga case d’in nan toh an kama shi ne” tun kafin ya kai k’arshe a maganar shi har ya nufi k’ofa.

Ganin haka ne Farhan ya mik’e yana cewa ” toh mun gode y’allab’ai, a tashi lafiya”. Ya k’arashe yana biyo shi a baya, da kallo ya raka su yana cewa ” yaran masu kud’in nan suna tunanin a koina zasuyi haukar su a bisu yanda suke so, ko yanzun ma banga damar kama shi bane ko da it will cost my job ne. Da shegun idanun shi a wajen, wa ma ya sani ko lodge ya kaita ya b’oye zai zo yanawa mutane barazana”. Daga haka ya fito shima yana rufe office d’in dama aiki zasuje, as he said in da dai ya amshi aikin can da ko na mai sun rage.

Suna shiga ya rufe Farhan da fad’a ” irinku ne ke zubarwa mutane mutunci, ji yanda kake kwantar da murya a gaban shi as if he’s the highest ranked staff a police ai ko IG bai isa ba wallahi har mu zai gayawa hukuma mu da mukeda military base a hannu mtsww”. Da mamaki yake kallon shi, yana mamakin girman kai da tsattauran ra’ayin Burhaan ji yanda yake wani daka masa tsawa a kai kamar wani ubanshi.

A d’an hasalen yace ” Saboda kuna da military base a hannu ne yasa ka salwantar da rayuwar baiwar Allah? well, kayi addua a ganta kawai if not duk girman Base d’in naku babu wanda ya isa ya k’waceka a hannun ‘yan Yerwa masu fad’a ajin da kake tak’ama kake rawa da bazar su”. Cewa yayi ” bana rawa da bazar kowa a Yerwa, ko aina ne I can stand for myself in amsa sunana confidently ba tare da na kuma rab’u da sunan su ba”.

Dariyar tura haushi yayi masa yana cewa ” mu kuma kaga dasu muke alfahari kuma kowani suna zamu amsa, zamu amsa ne because they stood for us from the very scratch bahaushe ma yace ‘kowani tsuntsu kukan gidan su yake yi’ so kaga bamu yi laifi ba “. Ya karashe da ajin shi shima, tsaki yayi bai tanka ba. Ba wai don baida amsar bashi ba but bai iya cacar baki ba, kai magana ma Farhan da Nadeefah suna cikin masu takura mai yayi magana suma bai tab’a basu amsar da yake so ba har yanzu.

Haka suka dinga zagaye a bus stops wai ko zasu ganta, sai dai babu ko mai kama da ita. And one good thing is yanda suka ma mance da sunyi musayar yawu, sai dai babu mai tanka ma wani cikin su unless idan ta kama.

Har to 11 babu alamarta hakan yasa Farhan ya basu shawarar komawa suma subi layin y’an jiran tsammani, a ran shi ya k’udure gobe da asuba zai kai maganar gaba ga media ko a samu hope. Dukda that’s so against the Yerwas, duk wani abu da ya shafe su basu son yana shiga media. ko mai suna yin shine in-house hakan ne ya sa babu wanda ya isa yace ga me suke ciki or how wealthy they are kai har a charity foundations d’in su.

They are not secretive but highly professionals and everything about then is confidential, duk da kasancewar Lele is a social media influencer amma bata tab’a posting abinda ya shafe a media ba. Kai barta da arts d’inta da products d’in ta, sai promoting brands d’in ta after that sai skin care tips da ta kan bada a lokuta nothing more.

Ko da suka kawo gate kasa shiga yayi don ya san kwanan zancen, kwantar da sit suka yi. Within short time Farhan yayi dozing off dama shi kasa ne damuwa bata hanashi bacci. Shi ko idanuwan shi k’yar ya zura a hanya kamar ance mai zata dawo…

Kallon gefenta yayi tana ta sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen idanunta basu daina gudu ba, tausayin ta ne ya kamashi duk da bai san ta ba. Ruwa ya mik’a mata yana cewa ” kiyi hak’uri everything will be ok”. D’an kallon shi tayi da lumsassun idanuwanta, sai kuma ta maida ta runtse bayan ta shanye ruwan da ya mik’o mata. A hankali ta furta ‘thanks’ daga haka bata sake cewa komai ba, shi ma dama ba gwanin magana bane musamman ga bare.

Suna hanyar har aka kira ishai, a lokacin sun d’an fara isowa cikin Kaduna don har sun kusa Tungan rafin dinya. Sai suka ji fas!! k’arar fashewar tyre, tsayar da motar yayi yana addua kafin ya fita, duba motar yayi faci sukayi. Butt ya bud’e ko yana da spare tyre amma wayam babu, back seat ya bud’e ya sake dubawa ko a nan ya ajiye don ya kan ajiye a nan sai dai karatun d’aya ne babu.

Tsaye yayi yana hange sama da k’asa sai dai babu alamun bakanike ko mai sa iska, dawowa yayi yana bud’e motar ya shiga ciki yana furta ‘ hasbunallah’. D’an d’agowa tayi cikeda damuwa tace ” lafiya kuwa?” A hankali yace ” munyi faci ne” d’an zaro ido tayi, faci a dokar daji? “Subhanallah” ta furta da k’arfi muryarta yana exposing damuwar da take ciki.

Dafe kai yayi yana mai kwantar da kan a steering wheel, yana tunanin mafita. Toh ko dai barin motar zai yi a nan ne, in yaso sai yayi gaba ya samo mai gyara ko me?. Da sauri ya mik’e yana jin kamar idean shi tayi, toh amma ita wannan baiwar Allah fa? Barinta zaiyi ita d’aya a tsakiyar dajin nan or what?.

D’an dubarta yayi har lokacin yana dafe da kan shi yace ” ammmm,,,,,zan fita neman mai gyara, I’ll lock you in the car sai ki kwantar da kujerar kafin in dawo”. Ai da sauri a mugun tsorace tace ” ka bar ni a wace motar? Ai sai dai muje tare” ta k’arashe tana gyara zaman ta.

Cire hannunshi yayi yana kallonta, fita da ita daga motar matsala ne ko dan duba da kalar hanyar da suke. Armed robbers zasu iya zuwa or wasu miyagun kuma shi a halin nan is vulnerable, so zasu iya cutar dasu musamman ita da take mace. Don haka yace ” ba dad’ewa zanyi ba, masu gyara kawai zan nemo su d’an gyara mana tunda kin ga nan highway ne babu ta yanda zan iya jan motar a haka akwai risk”.

Shiru tayi tana tunani itama ta san fitar ta akwai risk amma hausawa fa sunce zama wuri d’aya tsautsayi, kuma mai ai da matsalar zaune gwara ta tsaye. Cewa tayi ” ka ja motar a hankali zuwa gaban may be a dace amma kaima fitar ka daga cikin motar ai is not advisable in kuma zaka fita then I’m following you ko me zai same mu ya same mu a tare”.

Ajiyar zuciya ya sauke kawai sai ya tada motar, tunda ya lura itama tana da kafiya ga kuma time ya tafi har 8 tayi da minti 18. Jan motar ya fara yi kamar mai koyan tuk’i, tafiya suke yi kamar basu yi suna wucen wurin suka hango gungun samari a zaune suna busa hayak’i. Addua dai sukeyi a zuciyar su, yayinda samarin suka tsura musu idanu. Suma kallonsu suke yi amma da yake su suna cikin mota ya sanya ba sa ganin su, runtse idanu yayi yana k’ara speed kad’an har suka wuce wajen.

Sai da suka iso gidan busa da wannan tafiyar, lokacin har tara ta gota kuma har time d’in basu ga mai gyara ba. Cigaba da jan motar yake yi kawai yana addua a ran shi tareda fatan kar a samu matsala, na accident ga motoci da suke gudu kamar ba a duniya zasu tsaya ba hakan ne ma ya sanya shi sauka a kan titi yake bin gefen titi.

Sun d’an sake wasu tafiyar mai tsayi sai ga wata mota nan da take tahowa ta d’ayan hannun, tsayar da motar a kayi drivern ya lek’o da kan shi yana cewa ” ka juya malam muyi yanke, gaba can an tare mutane ba lafiya”.

Da sauri ta dafe k’irji yau taga banu shi ko cewa yayi ” ai ni nan da kake gani na faci nayi ba zan iya yanke ba tunda ka san hanyar ba kyau ta cika ba”. Da k’arfi yayi magana duk dan yaji ai ko da sauri ya juya motar izuwa hannun da suke kun san hanyar wurin one-way ne. Ya tsaida motar a bayan tasu yana fitowa zuwa inda suke.

Yana k’arasowa ne yace ” ba ka da spare tyre ne?” kai ya gyad’a masa yana extending hannunshi sukayi musabaha yana cewa ” wallahi ban san banda ita ba ma sai yanzu”. Cewa yayi ” ayyah Allah sarki, inada tyre bari in d’auko sai a saka ga madam an d’auko ai ba zai yiwu a tafi a haka ba”. Ya k’arashe da tsokana kallon gefenta yayi yana murmushin yak’e, bai ko kula da hakan ba har ya juya zuwa motar shi.

Cikin abinda bai fi 30 mins ba suka kwance tyrer suka sanya wata, har lokacin babu motar da ta wuce da alamun sun samu labarin tare hanyar da akayi ne. Har kuma aka sa tayar aka gama tana ciki bata fito ba. Godiya yayi masa sosai shiko cewa yayi ” haba ai yiwa kai ne, ni na san wa zai taimaka min a sanda zan buk’aci taimakon yanzu dai kazo mu tafi kar aikin ya biyo ta kan mu”.

Murmushi yayi yana cewa ” ba ku gaisa da madam ba ai ” cewa yayi ” muje kam mu gaisa kar tace ban da kirki”. Glass d’inta yayi knocking ta sauke tana cewa ” har kun gama? Sannunku da k’ok’ari”. Yace ” sannu madam ya gida ya harkoki, yau dai kema kin ga halinda hanyar k’asar take ciki sai a cigaba da ma oga uzuri”.

D’an zare idanu tayi a ranta tana cewa ‘ wannan akwai magana waiii farfesa’ a fili kam tace ” wallahi kam Allah dai ya cigaba da tsarewa mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi”. Fuska a washe yace ” Ameen ai babu komai ” sai kuma ya kalli gefen d’ayan yana cewa ” sunana Abbas” shi kuma yace ” Mus’ab ” kallon shi tayi sai yanzu ta san sunan ya kalleta yana cewa ” Madam fa? Ko Mrs Mus’ab ya wadatar?”.

D’an murmushi tayi tana cewa ” Nadeefah” shima kallonta yayi kawai bai ce uffan ba, ganin yanda mutumin ya sake dasu kamar an san juna. Exchanging contacts sukayi da juna kafin kowa ya nufi motar bayan Musab ya sake jaddada godiyarshi mai tarin yawa a gare shi, yana shirin tada mota sai ga wani daga hanyar Kaduna-Abujan ya k’araso gabansu yana cewa ” hanyar is safe, Sojoji sun zo yanzu haka” daga haka yayi gaba ko jin amsar su bai yi ba don yafi tunanin abinda suka guje mawa kenan ya sa suka tsaya a hanyar.

Sai kawai kowa ya ja motar shi suna hawa hanya sosai, a dai-dai jangwan ne aka tsare su a check point lokacin hanyar ma babu mutane sosai. Sai da aka gama bincike kafin aka basu damar wucewa, tun daga nan basu sake tsayawa ba har sai da suka fito ta makera suka shigo Kaduna proper. Lokacin 11: 22 har tayi kallon side d’in ta yayi yana cewa ” wani unguwa kika nufa sai in sauke ki?”.

A hankali tace ” in kaje junction d’in complex ka sauke ni zan samu taxin da zai kaini gida naga kaima jiranka a keyi a gida”. Da yake tun d’azu ake kiranshi yana cewa yana hanya ya kusa, tana kyautata zaton matar shi ce ke kira. Bai kalleta ba yace ” to twelve d’in ne zaki tafi gida? Just tell me unguwar taku saboda in san ta inda zan shiga ko a cikin barnawan kike?”.

Girgiza kai tayi kafin tace ” Can cikin millennium city ne Yerwa layout naga dare yayi”, cewa yayi ” nima sabon kawo na nufa yanzu haka “. Daga haka bai sake magana ba, tafiya kawai yake yi. Da suka shigo millennium city ita ta dinga guiding d’in shi har suka iso Yerwan, Tun daga nesa ya gane cewa unguwar ta manya ce bai ma tab’a zuwa wurin ba yana dai jin ana fad’inta ashe kam ganinta yafi jinta.

A gate d’in shiga ne security suka tsayar da su don baa barin shiga sai d’an Yerwa musamman da dare, rana kam su kan bari in suna jin abin arziki in ba saji kuma sai dai ka kira wanda kazo wajen shi ya kira a barka ka shiga.

Daga saman suka ce ” oga turn back!” Kallonta yayi duk ta galabaita ganin ta kusa da gida ne ma ya d’an yi cheering d’inta kad’an yace ” ya zaa yi kenan?”. A hankali tace ” barin musu magana” turo kai tayi itama da d’an sauti duk da muryarta ya dishe saboda kuka da kuma gajiya tace ” its Nadeefah Yerwa let us in “. Amsa aka basu ” you might be dump or stupid, Nadeefah doesn’t stay late outside you should go back” cewa tayi ” you can come and check for yourself”.

Tsaki akayi wanda yake saman yace ” don’t let me repeat myself” ta bayan shi aka ce ” open up let’s see” ok sir ya furta don wanda yayi maganar superior d’in su ne a wurin. Saukowa suka fara yi kafin ya sauko ya kira na bakin gate yana basu umarnin bud’ewa, bin umarnin sukayi kuwa da sauri ya shigar da motar ciki suka maida suka rufe.

Dai-dai lokacin suka iso wurin, torch mai mugun haske suka dalle musu fuska. Da sauri suka k’ame oga Khamis yace ” sorry ma, we didn’t know it was you ” gyad’a kai tayi kawai tana cewa ” issokay Khamis you were just doing your job are we free to go?” Ta tambaya a gajiye.

Cewa yayi ” sure ma, good night ma” wuce su yayi yana jinjina tsarin wajen, directing d’in shi ta cigaba da yi har suka iso street d’in da Hajjah take Garwa Zannah close. A gate suka tarda motar Burhaan dake parke har lokacin, honk yayi a dai-dai gate d’in gidan.

Honk d’in da ya jefa mutanen dake ciki a cikin fargaba, dukan su suna zaune ne a filin gidan. Har Hajjah duk yanda yaran suka so ta koma ciki kuwa k’i tayi, jin hon ya sa suka tsaya cak ana jiran aga wanda zai shigo duk da sun fi bada cewa Burhaan ne suna son ganin shi dawa zasu shigo.

A waje ko da sauri Farhan ya bud’e idanu yana kallon gate d’in, ganin bak’uwar mota ya sanya shi kallon Burhaan yana cewa ” ga wata mota can zata shiga ciki ko ita ce ta dawo?”. Sai lokacin ya kalli gate d’in dukda yaji hon d’in amma bai d’aga kai ya kalli direction d’in su ba, yana waigawa motar tana shigewa tada tashi yayi yana mara musu baya.

Daga ganin yanayin mutanen dake tsaye ya fahimci damuwar rashinta ne yayi musu yawa, don haka ya matso da motar har kusan harabar inda suke. Ai kafin ya gyara parking ta b’alle murfin ta fita, da sauri ta nufi hajjah tana rungumeta tana sanya kuka da k’arfi a dai-dai time d’in ya iso wurin kuma a lokacin Burhaan da Farhan suka k’araso su ma.

<< Nisfu Deeniy 9Nisfu Deeniy 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×