Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

A guje ta fad’a gadonta ta na sanya wani kuka gwanin tausayi, ita kanta ba a son ranta take nacewa soyayyarsa ba. Har jin haushin kanta takeyi, amma kuma ta kasa yakice shi da tunaninshi daga kanta balle kuma nacin rab’ar duk inda yake. Ta dad’e ta na kukan har ta gaji ganin ba ma’agaji sai Allah, ta bawa kanta hak’uri ta share hawayenta.

Wanka ta sake ta shirya cikin kayan bacci masu taushi, har ta kwanta taji d’akin yayi mata fad’i da girma wayarta ta d’auka ta fito. Cikin sand’a ta nufi d’akin Hajjah dake zaune akan dadduma, ba wanda ya kalli wani cikinsu direct gadon ta d’ane tana danna wayarta har Hajjah ta kammala adduointa ta hau gadon bayan ta rage haske.

Tana kwantawa ta lallab’a jikinta ta shige kamar zata koma cikinta, Hajjah ce tayi musu addua ta shafesu kafin bacci yayi awon gaba dasu gabad’aya.

A ‘yan kwanakinnan an samu sauk’in k’ulafucin Lele aka Islaam daga Hajjah har ma Suleim sai dai natacciyar zuciyarta bata je hutu ko na rabin second ba, sai ma kara-kaunar shi da ta k’aru a sak’o da lungun zuciyarta. Ko bacci bata iyawa sai ta kalli hotunan shi da suka zama tamkar magani gareta,  kuma suke sake ingiza mai kantu a kan shi.

Dakatar da tafiyarta Abujan da tayi niyyar yi tayi, ganin watan ya kusa k’arewa kuma su Ummun suna gab da zuwa hakan ya sa ta bar shi sai in sunzo sai su tafi tare don shi really missed them bama ta tab’a dad’ewa a Kaduna kamar wannan karon ba ma.  A gefe kuma tana sake d’aura d’amarar addua a kan samun Burhaan d’in ba kamar yadda Hajjah ta bata shawara ba don ita cewa tayi ta nemi zab’in Allah kan tarayyansu ita kuma adduarta bai wuce Allah ya mallaka maka Burhaan ya sanya shine mijinta.

(Hmm lallai Lele a zamanin nan fa sai a na had’awa da neman zab’in Allah yoh yana sonki ma ya aureki ya ci ubanka balle ba sonka yake yi ba?, muje zuwa dai)

Tsaye take a toilet bayan idar da lalurar da ya kaita ne kamar ance ta lek’a window ta hango shigowar wata motar da ta sanya ta sakin ihu harda tsallen murna. Fitowa tayi ta na gyara zaman veil d’inta mai had’e da p-cap lilac color sanye take da palazzo pants wine color na kamfanin Victoria Beckham sai sleeves lilac na Armani k’afarta sanye da black crocs mai mugun kyau.

Sauka k’asa tayi tana washe baki ta isa ga motar, ko wainda ke ciki basu kaiga fitowa ba. Isarta ne yasa aka bud’e side d’in driver wani kyakkyawan saurayi mai tsananin kama da ita but ta fishi haske and he’s more masculine than her kana fuskarshi cikeda gemu, kana ganinshi kaga d’an gayu first class kuma namiji mai ji da lokacinshi abinson kowace mace sai dai in bata samu ba.

Rungume shi tayi ya na fitowa, hannu yasa ya tarbeta shima nan ta sakar mai kukan shagwab’a. Lallashinta yayi tayi kamar wata k’aramar yarinya har sanda tayi shiru kafin ta sake shi tana cewa “irin zuwan nan na bazata  Yayani?”

D’age gira yayi yace “Ai kin rusa surprise d’in girlie,,,wai ya akayi kika san nine?”

Ya k’arashe da dungure mata hanci , dariyarta mai kyau ta sake tace ” a jikina naji shigowarka,,,,abunka da jini.” ta k’arashe tana kashe masa ido d’aya. Dariya yayi don tsokanarta tana cikin abunda yake so tattare da ita she’s full of life and vibes , yace ” jini fa indeed,,,you know nazo nan inyi surprising d’inta you have no idea how bad I’ve missed her….”

Tab’e baki tayi tace “I knew it you are not here for me but for her,,,,let the singles breeeth!” Harararta yayi yace ” I’m here for you both naa,,,, and I’m glad that I’ve met you in good condition…” Ta katse shi da ” you’ve see me dai not met me haka ake meeting mutane.” Ta k’are da yanayin kamar zata sa kuka, hannu ya kai zai kamota ta ruga tana dariya.

Juyawan da zatayi numfashinta ya tsaya cak, sakamakon ganin wanda ya fito daga d’ayan side d’in fuskarnan a d’aure kamar zaiyi aman wuta. Dafe k’irji tayi tana gaisheshi cikin ko in kula ya amsa ya kalli El-Sadeeq d’in murya a cushe yace ” Buddy ana nemana a clinic, I’ll have to go zan tafi da motar in yaso sai in turo ma wani.”

Girgiza kai yayi yace ” no need,,,,I’ll use hers sai mun had’u later.” ok yace kawai ya juyo zuwa driver’s side d’in ya shige ya ja motar. Kallonshi ElSadeeq yayi har yayi nisa shi da yaso a yau yayi surprising d’in shi ya nuna mishi wacce yake so da k’auna, don ko a mota da suna hanya labarin babe d’in da yake so yake tayi though he’s not even that interested in the whole gist kuma yasan yanda yake da banzan policyn shi na ba zaiyi dating ‘yar Yerwa ba balle ya iya aurenta ba.

Shi dai zai iya in fact next meeting zai kai maganar ga iyaye don bai son ayi taking time bai mallaki Suleim d’insa ba jan hannun Lele yayi suka hau sama.

Shiko Islaam tun a hanya hirar ta gundure shi don ba zai iya ce mai yayi shiru bane amma yanda bai sa baki ba shows it all, da yake ElSadeeq d’in ya san halin kayanshi yasa bai ko damuba. Tun da ya sauka yake burin sanya idanunshi akan ta hakan yasa ya karb’i driving d’in don yasan ba lallai ya kaishi Yerwa Complex ba, esp in ya san wurin mace zai je.

Shiko Islaam ai ko da yayi requesting ai ba zai k’i ba saboda ko ba komai zai ganta, don yana tsananin son ganin nata girman kanshi ne yake hanashi bawa zuciyar shi abunda yake so. Saidai ganin Lele da jin maganar shi ya sanya shi tunanin k’ila a cikin shirmammun k’awayenta ElSadeeq yake son wata hakan ne ma ya sanya shi jin haushi da rainawa Sadeeq d’in that’s why he said ana jiranshi a clinic cos he can’t stand seeing abunda ranshi zai b’aci yana tafe yayi tsaki yafi cikin ludayi a haka har yakai clinic d’in.

Su ko basu ma san yana yi ba don bayan shigarsu, direct Yerwa Closest suka yada zango anan ta baro yayan nata ganin yadda aka fara ba soyayya hak’k’inta basu ko kula da ita ba. Da yake ita ba mai damuwa bace sai kawai ta wuce sama ta fara aikin dake gabanta hakan ne ma yayi keeping d’in ta busy, sai kafin zuhr ya shigo, key ya amsa a hannunta kafin ya wuce gida.

Yau ba tayi closing da wuri ba duk da son hakan da tayi, sakamakon wata client d’in ta da tazo. Regular client ce don anan take komai da ya shafi gyaran jiki, lalle har ma da make up. Kuma bata yarda kowa ya tab’ata sai ita, tana cikin mata facial kira ya shigo wayarta bata d’aga ba sai da ta kammala kafin ta d’auki wayar sunan Safwaan da tayi saving da ‘Fav cousin ‘ da Emojis ne ya bayyana a screen d’in murmushi tayi tana dialing.

D’agawa yayi cikin muryanshi mai mugun taushi yace ” K’amshiii!! ” kaf Yerwa shi d’aya yake kiranta da sunan lumshe idanu tayi a d’an shagwab’e tace ” Fave nayi fushi fa, ka manta dani.” Tana jiyo sautin murmushin shi daga can side d’in yace “ni ina na isa in mantaki?, kina raina always “ya fad’a da iyakar gaskiyarshi.

Ba ta ko gane me yake nufi ba tace ” uhmm naji dai, ya kake?” Ajiyar zuciya ya sauke yace “ina lafiya, kewarki kawai nakeyi na shigo Yerwa complex zanci abinci sai naga floor d’in ku da wuta bakuyi closing bane?”

Cikin murnan ta samu mai maidata gida tace “Wallahi nice fa in gaya maka aikin ne ya kaini dare and my car is with Ya Sadeeq, ka wuce ne?”

Amsa ya bata da “Nope, my order is not even ready in na gama zan hawo floor d’in naku sai in maidake gida.” Cikeda nishad’i tace ” thanks fave, you are a darling.” bata jira shi ba ta katse wayar tana komawa kan aikinta suna tab’a hira da client d’in nata. A side d’in Safwaan kuwa jin zancen nata yayi har a tsakiyar kanshi a hankali ya furta “Da sannu zan tabbatar da hakan a gareki.”

She’s almost done with the job sanda ya hawo floor d’in, kiranta yayi nan ta shaida mai ya jirata a office d’in ta tana aiki amma ba zata jima ba. Hakan yasa shi shiga ya zauna k’are ma office d’in nata kallo yayi ‘ everything about her is classy, stylish and unique, she has a good fashion sense.’ wanda yake k’ara sashi narkewa a sonta cos yana son mace ‘yar k’walisa, ma’abociyar gayu da kula da kai. Yana sak’e-sak’en shi ta shigo office d’in tana shagwab’e fuska, murmushi tayi tace,

“I’m sorry i keep you waiting! ” Girgiza kai yayi ya na lumshe idanunshi da ya tsura mata yana mai yabawa halitta da kuma yanayin ta bata da girman kai da kai kanta wani waje kamar sauran ‘yan matan Yerwa and she’s so respectful despite the fact she’s jovial and friendly tana bawa hatta masu aikinsu girma da daraja ta kasancewarsu y’an adam,  cewa yayi  “Don’t mention ai ban dad’e ba hope kin dai gama?”

Gyad’a masa kai tayi tana had’a kayanta da zata tafi dasu, sai da ta had’a komai kan ta taso tana cewa ” shall we?” yep ya furta a hankali yana mik’ewa tana gaba yana biye da ita kulle koina tayi ta kashe light kana ta mik’awa securityn floor d’in key da kud’i tana cewa ” Baba Sule dare ya kawo jiki aje a huta sai kuma gobe in mai kowa ya kaimu.”

“Allah ya tashe mu lafiya Hajiya, nagode sosai Allah ya k’ara bud’i Alhaji a tashi lafiya ” Ameen suka amsa gabad’aya suna sauka yayinda Baban ya bisu da kallo har k’asan ran shi yaran familyn suna birge shi basuda matsala ga jin k’ai da tausayin talakawa, haka nan hannunsu a bud’e yake. Ko yanzu da Safwaan zai shiga ciki sai da ya ganshi, yanzu ma ga Lele da nata addua yayi  musu yana rufe floor floor d’in gabad’aya kafin ya sauko zuwa gida.

Suna tafe a hanya sai shiriritarsu sukeyi yana bata labarin wani picnic da yaje, kasancewar a gajiye take bata wani biye masa ba har ya shiga gidan Hajjahn. Fitowa tayi don bata da burin da ya wuce tayi wanka ta kwanta don a can tayi sallah, ganin yanda take ta hamma da yatsina fuska which make her quite adorable and cute yasa ya d’auki jakarta a hannu d’aya d’ayan hannunshi kuma ya rik’o hannunta suka nufi parlorn.

Da sallama duka a bakinsu a take k’irjinta ya buga sakamakon k’amshin da taji da kuma wa’inda suka amsa sallamar, Burhaan ne da ElSadeeq dake zaune sun sanya Hajjah a tsakiya.

Tun Magrib suke gidan anan suka ci abincin dare in da sai tsiya takewa Burhaan d’in akan yaushe rabon da ta ganshi, shikuma sai b’ata fuska yakeyi don a da yana zuwa amma tun abunda ya faru tsakaninshi da Lele sai ya d’auke k’afarshi daga gidan.

Shigowar su akan hannunsu dake sarke idanunshi ya sauka, ko kad’an bai ji komai a ran shi ba tunda ai ba yau suka fara rik’e hannun juna ba shi addua yake ma su daidaita kansu can su suka sani amsa sallamar yayi yana kauda kanshi . Washe baki ElSadeeq yayi yana cewa ”  Yanzu nake maganarki sweetheart.”

Cuso baki tayi tace ” kuma ka barni hakanan ba mota a hannuna if not for Ya Safwaan da sai dai fa in nemi uber,,,,,uhmm Hajjah ta I’ve missed you” ta k’arashe zancen tana shigewa jikin Hajjah ta side d’in da ElSadeeq d’in yake, shafa kanta Hajjah tayi tace ” ai na hanaki overtime d’in nan Lele, sai kinje kinyi overtime d’inki kizo kiyita min raki ki tashi kije ki watsa ruwa zakiji dad’in jikinki sai ki kwanta.”

Tura baki tayi tana mai gaishe da su Islaam da Sadeeq d’in amsawa sukayi kafin ta mik’e “Ni dai na shiga ciki sai da safenku,,,,Yaya Safwaan thanks for the ride you are so sweet.”

Ta k’arashe da karb’an jakar ta dake hannunshi tana jifanshi da murmushi, murmushin shima yayi mata yana d’aga mata hannu. Wucesu tayi suna cigaba da maganar da sukeyi wanka tayi da alwala shafai da wutri tayi tana idarwa ta baje kan gado idanunta suna rufewa cike da bacci.

A parlor kam ko da ta wuce basu wani zauna ba haramar tafiya sukayi, banda ElSadeeq da anan zai zauna a BQ. Tare suka fita su duka sai da ya rakasu gaban motocinsu sun d’an jima suna magana kafin kowannensu ya shige cikin motar shi suka ja  zuwa gida bai koma ciki ba sai ya wuce d’akin da yake.

Hajjah tsayawa tayi maids d’in ta suka gyara koina kafin ta wuce cikin d’akin sanda ta shigo bacci ya d’an fara kwashe Lele, zama tayi kusa da ita tace ” bacci kikeyi ne?”. Bud’e idanu tayi cikeda shagwab’a ta zauna tana tura baki tace ” uhmm”, cewa tayi ” sau nawa nake miki kashedi akan barin Safwaan ya na shisshige miki ne?” ware idanu tayi tace ” like for real Hajjah? àwágə̀nân kúràngə̀nà, Álà nàngàrò ( we are cousins, for God’s sake).”

Harararta tayi tace “Na sani ba sai kin maimaita min ba, amma kasancewar ku cousins ba shi ke nufin ku muharramai bane ko ba komai yanda kike fatan zama matar Yayanshi a gobe ai bai kamata kina barin kuna ko wane irin wasa ba ko dan kar shi ya zargi wani abu tsakaninku.”

Shiru tayi bata tanka ba don a bahagon tunaninta bata ga aibun abunda tayi ba, hannunta fa kawai ya rik’e amma kuma jin Hajjahn tace mata ‘matar Burhaan a gobe’ yasa ba zatai mata musu ba.

Besides, bata shiryawa rikicin Hajjah da daren nan ba tace ” toh Hajjah zan kiyaye in shaa Allah ” Tashi tayi tana cewa “da dai yafi miki, sai da safe”. Amsa ta bata da “Allah ya kaimu lafiya ” Ameen ta amsa tana fita bayan ta kashe mata wuta, dafe kanta tayi tace ” Hajjah rigima, abunda fa ya shigo da ita kenan Allah ya tsare mana ke Hajjah.” Tana mai jan bargo tayi kwanciyarta a take bacci ya d’auketa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nisfu Deeniy 2Nisfu Deeniy 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×