“Kar in kara jin ance an ganki da Datti…”
Kashedin da Babanta yayi mata yana dawo mata yana kuma saka zuciyar ta dokawa a cikin kirjinta a lokacin da take tsaye tare da Dattin, yana mata murmushin shi da zaka hango kyallin shi har cikin idanuwan shi da wahala bata saka su yin ja, ko ita ta samu kyawu da hasken idanuwan shi tana so.
“Wahalar mu ta zo karshe Dije, na samo mana wanda zai aure ki ya sakomun ke bayan wata daya…anjima zai zo wajen ki, gobe sai yaje wajen Baba…”
Ya karasa maganar fara’ar shi na dan dishewa da wani tunani daya gifta mishi, lokaci daya kirjin shi ya dauki dumi, duhun kishi na lullube shi.
“Karki hada shimfida dashi Dije, karki rabamun kan ki da wani, zuciyata ba zata dauka ba.”
Kai ta gyada mishi a kunyace tana ganin kamar wannan bukatar tashi ce abu mafi sauki a duniyar ta. Su duka basa hango yanda ba kowanne iko bane yake a hannun su. Ko da ta koma gida shaukin kaunar Datti ce ta dinga dawainiya da ita har bayan isha’i, tana kirga kwanakin da zata suka rage kafin ta kasancewa karkashin shi a matsayin mata. Da aka aiko kiranta hijabi ta dauka ta saka tana kaucewa idanuwan Innar ta da ta kafe a kanta. Gaisawa kawai sukayi suna rasa abinda zasu ce ma juna, ita Dije ma yawo tunaninta yakeyi yana neman inda ta san mutumin da yake tsaye a gaban ta, duk da babu wadataccen haske a wajen kasancewar wata yayi nisa, hasken shi ya dishe.
“Baabuga sunana, dan gidan Sajo.”
Sai lokacin ta tuna, Baabuga ne, Baabugan da suke kirga ma yawan yara tun lokacin tana budurwa har ma bayan tayi aure in tazo gida, ba’a rasa wani a cikin yan uwan ta da zai ce.
“Matar Baabuga ta haihu…”
Dariya ta kanyi.
“Nifa harna bace lissafi tunda ya karo mata ta uku…”
Dan haihuwa a gidan Baabuga ta zama tamkar gasa ce a tsakanin matan shi da suka sakama kan su na ganin kowacce ta tsere ma ‘yar uwar ta a yawan yara. Wani idan yaji labarin su zai dauka wani abin duniyar Baabuga ya tara shisa suke gasar haihuwa don wata tafi wata samun dukiya idan shi Baabuga din ya kwanta dama, to babu wani kudin da yake da shi, asali ko gonar shi ta kanshi baida ita, sai dai wannan shekarar yayi aiki a karkashin wa’ansu su biya shi da amfanin gonar da yake ciyar da zuri’ar shi da ita. Yaran gidan Baabuga sun fi kowa dauda a yaran kauyen nasu gabaki daya,ga su kyawawa saboda Baabuga bashi da muni, an kuma ce baya auren mummuna, cikin talakawa yan uwan shi yake kurdawa ya zabo mai kyawun gaske.
Amman rashin suttura da kulawar gaske tasa yaran sunyi wani muni da talauci kadai kan samar, in ta ga giccin su idan zataje unguwa sai ta tsinci kanta da neman tsari daga talauci dan ba jarabta bace mai saukin dauka. A wani bangaren na zuciyarta kuma sai ta dinga hasaso kafafuwanta a cikin takalma Baabuga tana duba zabinka da yayi ma rayuwar shi da kuma yanda idan itace zata yisu, cikin zabukan harda zama da mata kwara daya don yaran da zasu haifa su sami wadatacciyar kulawa. Bata cika kyamatar zabukan mutane ba, saboda duk yanda ita basuyi mata ba, to tasan suna da nasu dalilin.
Baabuga na cikin sahun farko na mutanen da take kasa yima uzuri. Amman tayiwa Datti da ya kawo mata shi, zata jure zama da Baabuga na kwanaki talatin, zata runtse idanuwanta daga ganin duk wani abu da bata so a tare da shi ta kalle shi a matsayin maslahar su kadai, ita da Datti, a matsayin hanya daya da suke da ita da zata sake hada su da juna.
“Na gane, gobe zaka sami Baba ko?”
Ta bukata cikin harshen fulatanci dan shima da shi ya yi mata magana, kai ya jinjina mata.
“Hakane…”
Numfashi ta sauke mai nauyi, ko Datti bai bukaci karta hada shimfida da Baabuga ba, ita da kanta tasan abune da ba zai yiwuwa ba.
“Allah ya nuna mana ya kuma sadamu da alkhairi, sai da safe.”
Ta karasa tana juyawa ta shige gida. Bata jima ba taji shigowar Baba, tana da yakinin ‘yan rahon shi da suka daukar ma kan su nauyin kula da duk wani motsin ta sun bishi sun labarta masa ta sake tsayawa da Julde, tunda da sanyin yamma ya zo, ko da Baba yasa aka kirata yana rufeta da fada tasan kwanan zancen, batare da tsoron komai ko wani dar a ranta ba ta kyale shi ya kai karshe har yana dorawa da,
“Idan ku baku da hankali mu muna da shi, saki uku wasa ne? Me kuka dauki rayuwar ne wai? Zan sami Dattin in masa kashedi shima…”
Nan ne ta dago da kai tana saukewa idanuwan kan fuskar Baba
“Ba sai kaje ba Baba, za’a zo a gaishe da kai gobe da yardar Allah…”
Har a fuskar shi ta ga mamaki.
“Waye?”
Ya bukata a a takaice,
“Baabuga ne dan gidan…”
Bata ma karasa ba ya katse ta da fadin,
“Baabuga? Baabuga dan gidan mai rasuwa Sajo?”
Kai ta daga masa a hankali, duk da maganar tashi tayi kama da yanayi da kanshi ne fiye da yanda tayi kama da yana mata tambaya.
“Baabuga ki ka ce Dije.”
Baban ya sake fada cikin jinjina nauyin maganar, saboda baiga dalilin da zaisa ta zabi Baabuga ba, takowacce fuska basu dace da juna ba, batafi karfin shi ba, amman gazawar shi a kula da iyali ba boyayyen abu bane a wajen mazauna kauyen nasu, zai masa adalci daya, iya karfin shi yake tsaye akan iyalin shi, aikin duk daya fado ma Baabuga yi yakeyi, iyalan shine suna da yawa, sunfi karfin abinda yake samu nesa ba kusa ba. Dije zata zama kamar karin nauyi a wajen Baabuga, nauyin da Baba bai hango zai iya dauka ba. Yana kaunar yar tashi kusan fiye da sauran yaran saboda nutsuwar ta.
“Me yasa Baabuga? Ko dan ina miki fadan tsayawa da Datti? Ko wani a gidan ya yi miki maganar rashin dadi akan batun mutuwar auren ki?”
Wannan karin muryar Baba a tausashe ta fito, kai Dije take girgiza masa, banda tausayi babu wani abu da yan gidan gabaki daya suka nuna mata akan batun mutuwar auren ta, babu kuma wanda ya sake mata zancen yaushe zatayi wani auren kamar yanda taji Baba na zargi a cikin tambayoyin shi. Dalilin ta ya sha bamban da duk wannan.
“Auren kisan wuta za kiyi Dije…”
Baba ya jefeta da wani yanayi mai nauyi a muryar shi da yasa wani abu da tasan ba hanjinta bane amman yana da tsayi ya tsinke a cikin cikinta.
“Kinsan girman munin abinda zakiyi a addinin ki kuwa? Baki san haramcin shi ba ko?”
Da sauri take girgiza ma Baba kai.
“Ba auren kisan wuta zanyi ba Baba…”
Karya ta farko da ta gifta a tsakanin su tunda ta mallaki hankalin ta, ba’a sirri a gabanta ko laifi lokacin yarinta da yan matanci, don da Baba ya ce,
“Dije fadamun gaskiya kinji, me ya faru?”
Take zayyane masa komai, ko da kuwa harda ita a cikin laifin. Shisa idan ta fadi magana yake yarda kai tsaye, amman yau yanayinta da muryarta duk sun nuna rashin gaskiyar ta.
“Karki sa yazo wajena in dai ba son auren shi kike yi don ki zauna ba Dije, na rokeki karkiyi wannan kuskuren har ki raba zunubin shi dani…”
Wani abu ne tsaye a makoshin ta da ta kasa hadiyewa, abin da kuma bai hanata sake furta wata karyar ba da ita ce matakin farko na canza abinda suka tsara ita da Datti.
“Zaman aure zanyi Baba.”
Karyar da zata bibiyeta a gaba.
Karyar da zatayi dana sanin ta.
*****
Juma’atu babbar rana, juma’a hasken mako. Daren ta ma cike yake da albarka, abune da ko tsofaffi da aka haifa a musulunci suke kuma yin shi yanda suka taso suka ga anayi batare da neman ilimi ba sun san haka, kusan sune ma suka fara furta kalaman da basu san har a addinin da suke ikirarin bi ba kalaman su gaskiya ne, in da sun san darajar daren ranar da kuma ranar da ake so bawa ya raya da ibadun da zasu kara kusanta shi da Ubangiji, to da sun dage don ganin damar da suka samu ta kasancewa rayayyu kuma masu lafiya a darare da kuma ranakun juma’a mabanbanta bai wuce suna masu shagala ba.
Juma’a ce ta uku a wajen Dije, don hatta da lissafin awannin da suke cikin ranaku basa bace mata, yanda duk ta hango kuntata a gidan Baabuga ta wuce hasashen ta, bata saba ba, suna da yawa a nasu gidan, amman ba irin wannan yawan ba, kuma bakai kadai ake bari da aiki ba, taimakawa kawai zakayi, a zamanta gidan Datti kuwa ba kullum take abinci sau uku ba, fiye da rabin lokuttan ma a gidan Hammadi sukeyi tare da Abu, sai ta dibo nasu ta taho da shi, ko Abun tace mata karta dora girkin rana, ta saka abinci da ita. Abu da tayi kewa fiye da tunani.
Amman rashin son kazantar ta yasa sai ta share filin tsakar gidan na Baabuga sau biyu a rana duk da babu shafen sumunti, bandaki kuwa runtse ido kawai takeyi tana wanke iya inda zata tsugunna, tunda ta ina zaka fara wanke bandakin kasa? Wata irin jar kasa ce da lokaci yasa ta hade waje daya, ko kurar kirki bata tashi idan tana shara, amman ta bandakin batayi irin ta tsakar gidan ba. Bata kuma damuwa da zundenta da matan shi sukeyi, don ta kula kishi sukeyi da ita kamar babu gobe. Da sun san bata shigo domin ta zauna ba da sun sahirta mata, duka kwananta uku a gidan suka fara tashin hankalin sai ta karbi girki. Bata son hayaniyar shisa ta karba, kwana dai-dai sukeyi da take ganin kamar awa dai-dai ce, tuka tuwon gidan da kuma tarin wanke-wanke ba abu bane mai sauki.
Satin ta biyu akayi dace Abu ta zo ranar girkinta, ta sameta da dora wannan tukunyar tuwon gayyar, tana kallo har hawaye Abu ta dinga daukewa don karta gani, itama sai ta nuna mata bata gani din ba. Tayata tayi suka tuka suka kwasawa kowacce mace kason ta ita da bataliyar yaranta. Abun nata kallon ta, har kudi ta kwanto a habar zaninta tana ba Dijen da ta karba kawai tana ma Abu godiya. In ma ta tsaya gardama Abu baji zatayi ba, tunda bata san abinda suka shirya ba, haka bata san tana da kudin ta da Datti ya bata ba, masu yawan gaske kuwa.
“Abinda duk kike so ki bayar a siyo miki Dije, ba iya cin abincin gidan nan zakiyi ba.”
Bata kuwa iya ci din, idan ranar girkinta ne da safe ta dama koko, takan fito da kofi ta diba ta shiga dakin ta inda take da tulin sikari da farar alawa, wata ran ta dauke ta tana gutsura tana kurbar kokon, yan kananan yaran kan bata tausayi, nasu kokon saita diba a wani bokiti ta zuba musu sukari, ko ba ranar girkin ta ba da yake ance kuruci dangin hauka, yaro kuma babu ruwan shi da mahaifiyar shi bata san ka in dai kana kyautata mishi, da sun faki idon iyayen nasu sai taga sun fado dakin ta wai ta saka musu sikari ko ta basu farar alawar ta, bata taba hana su ba, har kudi tana dauka ta basu su siyo yar alawa.
Badon kowa takeyi ba sai dan kuruciyar yaran, da kuma yanda take jin ko kishi ya hadata da wata ba zata iyama yaranta mugunta ba, don shi da na kowane, watakila ma a cikin yaran kishiyar ne wani Allah zai nufa da samun arzikin da zatayi fatan ya ture yan ubanci gefe ya tallafi ‘yan uwan shi. A wajen matan Baabuga ba haka abin yake ba, gani sukeyi kamar yaudara ce da kissa irin ta mata, don ta fisu samun fada a wajen miji. A dan zamanta matan duk sun canza, yan sutturun su da sukan siya da kudaden sana’o’in hannun da suke yi, can na kasan akwati suke fiddowa kowacce na caske gayun da basu sabayi ba.
Matan Baabuga da halayen sune nishadin da takan samu a kuntataccen gidan shi duk idan wani uzuri ya fito da ita tsakar gida. Shikuwa duk daren duniya sai yayo mata kunshin tsire da rogo mai yawan gaske ya mika mata daki, shi take ci da dare ta rage har safe ta kara ci, wani lokaci da fura da tasha nono yake hado mata, tana kuma jin dadi, har rana ba zata wuni da yunwa ba tana jiran dawowar shi. Yawan hidimar yasa ta fahimci da kudaden Dattin ta akeyin su, shisa da wani irin nishadi take cin naman. A ranar kwananta kuwa in Baabuga ta shigo, kasa take sauka tabar mishi gadon karfen da aka kai mata.
Wajen ma yayi mata kada don gadon da sauran tarkacen ta duk ya cike dan dakin da bashi da girma. In kuwa taji ya maida kofa ya rufe tare da bugun zuciyar ta yake yin haka, bai taba bi takanta ba, sai minsharinta da zai tayata hira har wayewar gari. Wannan juma’ar kuwa itace ta karshe da zatayi a gidan shi, ita ce kuma wadda tazo mata a baibai. Ita din bata da wani jiki, duk da tana da madaidaicin tsayi, amman siririya ce da in tayi wani aikin zaka iya mamaki saboda yanayinta bai nuna alamar karfi ba. Karfin da dagaske bata da shi lokacin da tun shigowar Baabuga dakin ya mayar da kofa ya rufe ya zauna akan gado madadin kwanciya kai tsaye kamar yanda ya saba ya fara kashe mata jiki.
“Kwana uku ya rage miki da zama a gidan nan Dije, ina bukatar dukiyar da Datti yai mun alkawari dan ita kadai ce damar da nake da ita na tsayuwa akan nawa kafafun, tun tasowa ta a karkashin wasu nake…”
Yake fadi kamar mai bata labarin da bata ga alakarta da shi ba, bata kuma son ji.
“Ko ban ciyar dake ba, na baki makwanci, na kuma taimake ku, ki taimaka mun nima, ki taimaka mun Dije in dandana abinda nake ta hasashe tun shigowar ki gidan nan.”
Zuciyarta har cikin idanuwanta da suka ciko da hawayen tashin hankali take jin bugunta, musamman da Baabugan ya mike yana nufota. Takasance cikin mutanen da tashin hankali yake kwacewa sautin murya, hawaye ne dai ke zubar mata tana kuma matsawa baya, yanda ya riko damtsen hannun ta tasan bata da karfin da zata gwada da nashi.
“Allah ya isa tsakani na da kai Baabuga, har abada ba zan yafe maka ba, Allah ya isa tsakani na da kai.”
Sune kalaman da ta furta cikin kuka da safe da zai bar dakin, amman ko bi takanta baiyi ba. Kuka tayi shi kamar ranta zai fita tun daren har wayewar gari, bokatan ruwa biyu ta ja a rijiyar da take can karshen gidan tana wanke jikinta, amman bata daina jin Baabuga a wajajen da bai kamata ba a jikinta, a wajajen da ba hurumin shi bane ba. Wuni tayi kuka, ta sake kwana tana yin shi, dan ledar daya shigo mata da ita ko kallon ta batayi ba har wani daren. Ta cine saboda tazo sallar ishayi ta dinga ganin wani duhu-duhu da bashi da alaka da dare, karta halaka kanta bayan wayewar garin zata zo mata da wani haske na daban.
*****
Ta san fara’ar da ta kasa boyuwa a kan fuskarta ce abu na farko daya fara tona mata asiri a wajen yan gidan su.
“Bakiji maganata ba ko Dije? Allah ya kyauta, Allah ya kuma yafe mana gabaki daya.”
Baba ya fadi bayan ta zo mishi da takardar saki har uku da Baabuga yayi mata. Baban kuma yaga dalili kwanaki hudu bayan haka, yaga da sa hannun Baabuga akayi komai, gonar da ya siya ba Baba kadai ta sanarwa da Baabuga yayi auren yarjejeniya da Dijen Datti. Cikin kankanin lokaci zancen auren kisan wutar da Dije tayi ya karade kauyen Marake. Har mamaki ta dingayi, yanda mutane zasu dauki abinda bai shafe su ba suyi ta cece kuce akan shi. Ita yaki take da zuciyarta, kamar yanda suka tsara da Datti, sai ta gama iddar ta ne zai zo. Kewar shi ke nukurkusar ta, ko da ba suyi wata magana mai yawa ba suga juna.
Amman a kasan zuciyarta tana jin zata iya daukar wannan dan takaitaccen lokacin, tayi kewar shi, tayi kewar Julde, dan Abu ita kadai tazo mata wannan Karin.
“Fada ya kamata inyi miki idan da gaske na dauke ki yar uwa, amman banda wannan zuciyar, in da baki kaso auren nan ba ina gab da zuwa in kashe miki shi.”
Abu ta karasa tana rungume Dijen kafin ta saketa tana share hawayen, suna kuka yin dariya gabaki daya. Ko kowa yaji haushin abinda tayi Abu ta wanke mata komai tas, kafin ma kwanaki su karasa cika ta koma gidan Dattin ta. Ta koma kusa da mutanen da take ji fiye da wasu a cikin yan uwanta. Innar ta bamai yawan magana bace bayan.
“Allah ya kyauta.”
Bata sake furta komai ba, itama Dijen bata yi wani yunkuri na kare kanta ba, sun sani, meye abin boye-boye. Auren kisan wuta tayi, zabinta ne, a cikin su babu wanda yasan soyayya balle tayi kokarin fahimtar da su, dul yayyaenta mata babu wadda ta auri kamar Datti. Takardar da Baabuga ya bata sai ta wanke mata abinda ya yi saura na shi da take ji a jikinta, shisa ko tunaninta bai kara giftawa ta daren ba. Kwana take tana tashi da farin cikin yanda ranar take kara kusantata da cikar burinta na komawa gidan Datti. Hankalin ta ya dauke, bata bi takan jikinta balle ta kula da sauyin da ya yi.
Haka bata zaben abinci, wanda duk taci zama yake, sai dai ko gyada wani ya ambata sai taji kamar ranta zai fita yabi ya nemo gyada duk inda take sannan ya dawo, bata samun nutsuwa, kudi ta cire ta aika gidan Asibi yayarta da yake tana siyarwa sai ta soyo mata kwano daya mai gishi ta zo ta adana tana diba kadan kadan, kamar nama haka takan ji gyadar. Bata kuma damu da rashin ganin al’adarta ba a watan farko, domin ta canza mata watanni biyu da suka gabata, ta kara kwanaki shidda kan lokacin ta, ta kuma kara kwanaki goma ana gaba. Wannan ma ta dauka hakan ne, kafin ya dai-daita tunda batasan dalilin shi na hargitsewar ba.
Har wani yammaci da Innar A’i kamar yanda suke kiran abokiyar zaman mahaifiyar su, duk da A’in ta rasu tana shekara uku. Kuma ba ita bace yarta ta farko, lakabin sunan yaki barinta ta kalli Dijen da take zaune tsakar gida tana tsintar wake, sosai take duban hasken da tayi, fatarta tayi wani luf ta jefeta da tambayar da ta razana duka ruhinta.
“Dije yaushe rabon ki da ganin al’adar ki?”
A razanen ta dago da bayanannen tsoro a fuskarta, tana neman nutsuwar da zata rage gudun da zuciyarta takeyi cike da kai kawo a cikin kirjinta.
“Wancen watan da wanda ya gabata kafin shi duka nayi karin kwanaki, ta rikice mun.”
Dan murmushi Innar A’i ta yi.
“To wannan rikicin kam mai motsi ne Dije.”
Ai batasan tasan ta mike ba sai da taji salatin Innar A’i, da kuma karar faduwar kwaryar waken da take kan jikinta tana fitar da me kyan tana zubawa a wata, ba’a kai da kwashewa ba aka sake yin ruwan sama irin na bazatar nan, duk sai wani yayi duhu cikin waken.
“Ni jikar Takko da Allareeni…”
Cewar Innar A’i tana dorawa da,
“Me yake damun ki Dije? Ciki ne fa, rabo mai girma amman kamar wani mugun abu?”
Ganin hawayen da suka wanke fuskar Dije. A wajen ta ba ciki bane, a wajenta ba rabo bane, a wajenta mugun abune a jikinta da zai nisantata da Datti na tsayin watanni tara da doriya a maimakon uku rak kamar yanda suka tsara.
“Baabuga ya cuceni”
Maganar zuci ta subuce mata, wasu hawaye sababbi na zubo mata.
“Wallahi Dije zan kwade ki da mari idan baki nutsu da wannan haukan ba, ko dan kinga an sa miki ido? Babu wanda yai miki maganar wautar da kika aikata?”
Nan tabar Innar A’in tana bambami da yake in dai wajen tarbiya ne a gidan kowa na da damar hukunta dan kowa kamar yanda zai ma nashi. Daki ta shige tana samun waje ta zauna dabas, yanayin ta zaisa kayi tunanin karshen duniyarta ne ya zo. Kuka take da yake fitowa daga zuciyarta, me zata ce ma Datti? Ta karya alkawarin da ta daukar mishi? Ta so binne daren su da Baabuga a matsayin tarihin da ba za’a taba tonowa ba, ba’aje ko ina ba asirinta yana son tonuwa kowa yagani. A yanda azabar son Datti ke nukurkusar ta ba zata iya fuskantar shi ba, kamar yanda ko ba tada niyyar komawa gidan shi ba zata taba hada iri da Baabuga ba
Zabi daya take da shi.
Zabin da shine kuskuren ta na biyu.
*****
Idan littafi na yayi muku dadi, ku taimakeni ta hanyar bude account da Bakandamiya don hakanne kadai zai baku damar yin like na shafin duk da zan saka da kuma yin comment ko da na fatan alkhairi ne. Hakan zaisa website din Bakandamiya su biyani.
Nice