Ruwan da Julde yayi nufin hadiyewa ne yaji ya zarce yana bin wata kofar da ba hanyar shi ba, ya kuma toshe masa wucewar iska, abinda ya saka shi fara tari babu kakkautawa a lokaci daya yana kokarin ganin numfashin shi ya saitu, ruwan ya kara sha yana jan numfashi, tarin ya fara tsagaitawa amman kamar an zuba masa borkono cikin makoshin shi, bai daina juyo muryar Datti ba.
“Allah ya kiyayeni wallahi, da in haifo da irin Ado gwara na mutu banga kwaina a duniya ba… Me ake da lalatacce? Sai an magana ace kaddara, to ita kaddara bata san inda ya kamata ta fada bane? Kawai mutane sun kasa tarbiyar yara duk sun lalace an wani boye bayan kaddara.”
Yana juyo.
“Allah ya kyauta.”
Da Dije ta furta kamar ko da yaushe, yau ko kokarin fahimtar da shi batayi ba, da alamu itama akwai abinda yake tata zuciyar tun safe, ya kula komai da sanyi-sanyi takeyin shi.
“Daada bakya jin dadi ne?”
Ya tambaya, dan murmushin da ya karanci na karfin haline ta dora a fuskarta.
“Me ka gani? Lafiyata kalua.”
Bai matsa ba, yana dai alakanta abinda yake damunta din da Bukar. Saboda shi yazo yace mata yaga Hamman Bukar din jiya. Ya ga kuma dawowarta da yamma. Dan yana sauri zai fice da ya tsaya ya tambayeta inda taje, sai yayi mata sannu da zuwa kawai yana fita. Ita damuwa tayi da shirun Bukar, shi ran shine a bace shisa bai cika so ko zancen Bukar ana masa ba. Bayan wasu yan watanni yace, amman tashin farko sai da ya shekara harya kara wata daya akai kafin ya waiwaye su. Dawowa ta biyu a lissafe Julde yake, watan Bukar din goma sha biyar.
“Ka samu ‘yan uwan da suka maye maka gurbin mu ne halan?”
Tambayar farko daya fara yiwa Bukar kenan, sai yayi dariya, dariyar nan tashi da ko baka so sai zuciyarka tayi sanyi, musamman da yayi ta idanuwan shi cike da ban hakuri.
“Ko zan sake wasu ‘yan uwan ya zanyi da jinin dake yawo a jiki na? Kuna raina Hamma, wallahi kuna raina ko da banzo ba.”
Kwanaki bakwai Bukar yayi, sai yaga kamar awa bakwai ne.
“Saura ka shekara biyu wannan karan.”
Ya fadi cike da kashedi, dariyar dai Bukar ya sakeyi, daya tashi saiya tsallake kashedin da Julden yayi masa harya kara. Saiya barsu da tarin kewa da tunanin halin da yake ciki. Da yaga Hamman Bukar din yaso ya tsaya yayi magana da shi, saiya kasa. Akwai wani haushin shi da yake kasan zuciyar shi da ya kasa gogewa. Shine sanadin komai, shi ya kwadaitawa Bukar barin su. Shi gashi ya dawo yanzun, Bukar na can. Wannan laifin na Hamman Bukar ba Julde kadai yake ganin shi ba, harda Dije. Musamman bayan tayi amfani da barkar da ta tambayi Datti fita taje gidan Baabuga, ta samu Hamman shi zaune akan kujera suna hira da matar da take tunanin itace mahaifiyar shi cikin nishadi kamar a duniya kaf basu da wata matsala.
“Ina Bukar?”
Ta tambaya a madadin amsa gaisuwar da Hamman yayi mata, numfashi yaja yana fitarwa cikin yanayin da yake son nuna kamar ta takura masa, kamar ta saka shi sake maimaita mata amsar da ya riga ya fada mata ita a baya.
“A cikin Maiduguri nake karatu, Bukar na Borno, garuruwan sun bambanta…”
Wannan karin itace ta sauke numfashi, Bukar ya fada mata, yace mata makarantar su Hamman shi a cike take da dalibai sanda sukaje, yana cikin tarin wanda aka hada aka tura su Borno din, makarantar wani dan uwan Malamin, bayani yayi mata yanda zata fahimta. Amman kewar danta da takeyi ya shafe mata komai.
“Me yasa? Me yasa zaka ja shi ku tafi ka dinga baro shi?”
Ta karasa hawaye cike da idanuwan shi.
“Bangane yaja shi suka tafi ba? Bukar din yaro ne karami?”
Juyawa Hamma ya yi yana katse Innar tashi da.
“Inna mana…”
Dije ta numfasa da nufin datsa mata magana itama wata matashiyar budurwa da zai wahala takai tsarar Yelwa ta fito daga daki tana gaishe da ita cikin wata siririyar murya da yanayi da yasa jikinta mutuwa.
“Lafiya lau.”
Ta amsa tana kallon fuskar budurwar da ba zata tunata a cikin yaran Baabuga ba. Sannan yanayin kyawun jikinta, da tufafinta kamar ba daga Marake take ba, a madadin shigar su ta fulani da ta mamaye fiye da rabin kauyen. Ba zatace ga asalin sunan kayan jikin yarinyar ba, kuma ba riga da zani bane ba, shigarta tayi kama da ta ‘yan binni, tsirarin ‘yan binnin da kan shigo Marake lokaci zuwa lokaci, kuma a cikin harshen Hausa tayi mata magana, gangariyar Hausar da babu alamun sirkin fulatanci a cikinta.
“Zaizo Daada, zai zo da yardar Allah.”
Hamma ya fadi, nauyin da zuciyarta yayi bai sa ta iya amsa shi ba, juyawa kawai tayi, kafarta daya ta taka soron gidan tajuyo muryar Innar shi na fadin.
“Mero haka zaki wuni baki saka ma cikinki komai ba? Ko irin abincin namu ne baiyi miki ba?”
Kalmomin karshe na tabbatar da hasashen tunaninta. Matashiyar da aka kira da Mero ba ‘yar gidan bace ba, bakuwa ce. Ko da bata fada ba, a iya sunan ta tsaya Dije zata gane bakuwa ce. Bukar bai taba ambaton Mero a cikin jerin ‘yan uwan shi ba.
Fita Dije tayi tunanin Bukar na danne mata na Mero.
Mero da bata hango kaddara sake hada hanyar su ba.
Balle kuma ta hango yanda zata zama silar faruwar komai.
Tana da yakinin idan wani abu ya samu Bukar zataji a jikinta, kaunar da take masa na da wannan girman. Amman bata da sukuni, tun jiya bata da wani sukuni, zuciyarta batayi mata dadi. Idan har yazo zata gwada, ko ba zaiji ba zata gwada ce masa ya zauna a kusa da ita. Ya hakura da karatun haka, idan da hali ya karasa a Marake tunda suma makarantun yanzun sun fara wadatarsu, ko wani gari da yake kusa dasu. In da idan ta matsa Datti ba zai amfani da nisan a matsayin uzurin shi na hanata zuwa wajen Bukar ba.
Ranakun duk da zaka ga yaran sun ci abinci a gidanta akwai wata magana da suke sonyi da Datti, yau ma haka ta kasance, Julde a kwanon Datti ya saka hannun shi bayan isha’i, suna cin abincin Datti na bashi labarin da bata cika son ji a bakin shi ba. Labaran da suke cike da laifukan wasu, laifukan da suma basu fi karfin Allah ya jarabce su da irin su ko fiye da haka ba, bata saka musu baki ba, bata ma daga kai ta kalle su ba duk da tana zaune akan tabarma daya da su
“Baba ina son zuwa Ikko har cikin raina. Dan Allah me yasa baka so kabar ni?”
Duk yanda Julde yake matsawa da yin nisa da Marake bai taba daga hankalin Dije ba, saboda tasan Datti, ta san Datti ba zai taba barin shi ba. Kusan yama fita son ganin su a kusa da shi. Don a lokuttan da Julde yake zuwa Kano harya dawo baka raba bakin Datti da mita akan yanda bayason wannan tafiye-tafiyen, mitar da zaka karanci babu komai a cikinta sai tsantsar kewar dan nashi da yayi a kusa da shi. Amman yau amsar da Datti ya bashi ta sa wani abu kadawa a cikinta da ya wuce ace hanta ce.
“Kayi aure tukunna, ka zama cikakken mutun inda yafi Ikko ma idan kana son zuwa sai kaje…”
Yaga yara a Marake da yawa da suke tafiya kudu da sunan neman sana’a, yaran Hausawa da na Fulani da baiga me yasa zasu bar tushen su da sunan neman kudi ba. Nomar suke gujema? Ko kiwon? Sana’oi gasu nan kala-kala a cikin yankin nasu da idan ka kama daya da gaske zai wahala kaqi samun abinda zaka rufawa kanka da iyalinka asiri. Gasu nan suna dawo da wata irin shiga sunyi watsi da al’adunsu, sun dauki na wasu can sun yafa. Randa yaga Baballe ya dawo da wani wando da wata yaloluwar riga, ya kama kugu ya tsuke, harya dawo gida yana bambami shi kadai da tsine irin wannan dabi’a daya kwaso yana cikakken bafullatani.
Idan ya tsaya iya shiga ma da sauki, wasu sanadin lalacewar su kenan.
“Ai shisa kaga na yiwa Magaji aure kafin in bari ya tafi kudun nan tunda ya nace, kasan yaran nan ka haife sune baka haifi halin su ba, nan sai kaga ya bijere mun akan zuwa kudun nan.”
Baban Magaji ya fadi wani lokaci da suke tattauna yanda burin yawancin matasan shiyar ya karkata da barin tsatsonsu da sunan neman kudi. Da farko maganar bata wani zauna ma Datti ba, saida aka wayi gari dan gidan Malam Shitu ya tattara kaya yayi gaba, an neme shi an rasa, sai daga baya labari ya bazu cewar ya gudu kudu ne don neman kudin da mahaifin ya nuna baya so. Abin ya tsorata shi duk da bai fada ba, amman kasa runtsawa yayi, inda duk zai rufe idanuwan shi saiya hango Julde a matsayin dan gidan Malam Shitu. Sai kuma ya hango irin matakin da zai dauka.
Randa duk Julde zai zabi duniya a saman ra’ayin shi zai tsine masa ne yabar sallama shi yabar shi da duniyar. Hukuncin daya hango kwara daya da zai iya kenan, amman kafin hakan ya faru yana da hanyoyin da zaibi duk lokacin da Julden ya sake bijiro masa da zancen zuwa Ikko. Sai dai dariyar da Julde ya kwashe da ita da irin amsar daya bashi ta saka shi murmusawa.
“To aini ban shirya ba Baba, kabari in fita neman kudin in tara sai ayi Magana.”
Murmushin dai Datti ya sakeyi.
“A zancen auren naka ne sai ka fita ka tara kudi? Baka san dan gidan waye kai ba? Ka manta kaf Marake babu ‘yar wanda zaka nema in dai don kudine ka kasa samu?”
Dariyar dai Julde ya sakeyi, aure, shine zaiyi aure? Kamar hakan na nufin rayuwa da tilon mace na wani lokaci koda yana da nufin karo wata. Ko da zai kara ba zai iya wuce mata hudu ba, da su kadai zai iya rayuwa. Sauran matan da zasu wuce su shiga idon shi fa? Yayi yaya? Anya aure na cikin jerin abinda yake hasasowa kan shi nan kusa kuwa? Ko zaiyi aure ba yanzun ba.
“Anya aure yanzun?”
Maganar da yayi nufin furtawa iya zuciyar shi ta kubce masa.
“Sa’anninka nawa ne har an ajiye musu yara? Ai ka isa auren.”
Datti ya fadi.
“In kaga kafarka a Ikko to da aurenka.”
Numfashi Julde yaja, har ran shi da zuwa Ikko yake kwana da shi yake tashi. Da tunanin tarin matan da yaji labarin su, kalar rayuwar da yake son jin yanda take. Kallon shi Datti yakeyi yana ganin yanda yake juyayin maganar auren a ran shi, kamar baya so. Da farko da yayi masa zancen hanya ce da zai gusar masa da tunanin yin nisa da gida. Amman yanzun da wani tunanin yazo masa sai yaji baya bukar amincewar Julde, saboda gatane zai masa. Sauki da nutsuwar sune duka. Idan yace yanzun da yaga su Yelwa sai wani sashi a zuciyar shi ya yanke ya fada can wani waje a cikin kirjin shi da tunanin sunyi girman da za’a iya musu aure kowanne lokaci.
Musamman Saratu, sai irin mazan da zasu aura su rike masa yaran da yake ji har a ruhin shi ya saka shi jin wani irin firgici na daban. Anya a cikin matasan da yake gani a Marake akwai wanda ya cancanci ya dauke su ya bawa? Sai yanzun yaga wanda ya kamata ya dauka ya ba Saratu, ga Julde a gaban shi.
“Ka auri Saratu.”
Datti yayi maganar cikin umarnin da kafin ya amsa Dije ta riga shi da fadin.
“Yau kuma yan zolayar taka ne suka motsa.”
Muryarta ta fito da tsantsar tsoron da maganganun shi suka jefata ciki. Saboda taji da gaske yake, taji babu alamar wasa a muryar shi ko kadan. Maganar tace bata tunanin auren yaran dukkan su bata taso ba, tunda sun kawo lokacin da za’a fara hakan. Amman Saratu? Akwai mata da yawa a kauyen banda ita, akwai matan da zata so gani da Julde banda Saratu da bata da nagartar da kowacce uwa zata so danta ya rayuwa da su. Daga jikin Hammadi ta fito, a hannun Abu ta taso amman ko daya a cikin tarin halayen su bata biyo ba.
Tana zaune da Datti don ta samu damar barin shi ta sake zabarshi, shi din zabinta ne a karo na farko da na biyu, saboda data nuna bata son shi a na farkon Baba ba zai taba mata dole ba, in dai akan maganar aure ne shawara itace abinda zai shiga tsakaninka da Baba, sauran zabin naka ne. Idan aka bata takarda da biro duk zata kwana ta yini tana zayyana duk wani dalili da auren Datti ya zame mata kuskure, duk wasu halayen shi da soyayyar da take masa ta rufe mata ido ta sake dawo masa a karo na biyu.
“Ba zolayar shi nake ba, da gaske nakeyi aure zan hada su da Saratu.”
Datti ya sake tabbatar musu.
“Baba bana son ta.”
Julde yayi maganar kan shi tsaye, duk da idan ance masa meye so din ma bai sani ba. Idan ta gifta hakika yana so ya tabata, idan tayi masa magana yana son jinta a jikinshi, yana son rabarta yaji bambancin da take dashi da sauran matan daya raba. Amman bai hango su karkashin inuwa daya a matsayin ma’aurata ba. Tun kafin ya rabi mace yasan akwai abubuwan da ya fiso a jikinta. Saratu bata da wannan abubuwan, idan ya kalleta bayajin komai daya wuce sha’awar da yanzun yasan ta wani dan lokaci ce.
“Ungo nan.”
Datti yace yana masa dakuwa.
“Kai har soyayya ka sani?”
Hannun shi Julde ya tsame daga cikin abincin da yake ci.
“Akan zuwa Ikko ne ai ko? Na hakura…”
Ya karasa yana mikewa yaje ya dauki buta ya wanke hannun shi yasa kai ya fice daga gidan.
“Kina jin shi?”
Datti ya fadi yana murmushi, saboda har ran shi yasan cewa wannan auren babu wanda ya isa ya hana ayi shi.
“Tunda baya so ai sai abar shi.”
Dije ta fadi cikin sanyin murya tunda itama baso takeyi ba, dalilinta kuma ba zai taba zama dalili a idon Datti da Saratu bata laifi ba.
“Ai ba sai yana so ba, bashi da hankalin da yasan abinda yake so da wanda baya so. Ko ke bansan ina son ki ba lokacin da Hamma yazo mun da zancen auren ki.”
Kallon shi tayi cikin ido, shigowar Yelwa na hanata amsawa.
“Yelwa…”
Datti ya kira yana sata fadada murmushinta.
“Ya kike ganin idan aka hada auren Hamman ki da Addar ki?”
Karasawa tayi tana zama kan tabarmar cike da zumudi.
“Dan Allah da gaske kake Baba? Hamma zai auri Adda?”
Dariya Datti ya yi.
“Eh mana.”
Wani irin tsalle tayi, ihun murnarta na karade gidan gabaki daya.
“Yaushe? Yaushe za’ayi musu auren? Hamma bai fadamun ba.”
Mikewa Dije tayi tsam tana shigewa daki, Datti baibi takanta ba, saboda yasan bata son Saratu, bata taba fada da bakinta ba, amman yanayin mu’amalarta da Saratun ya nuna haka. Ya nuna yanda bata son yarinyar. Ba kuma ya bukatar amincewarta, ita dinma a karkashin shi take balle kuma su Julde.
“Je ki kiramun ita tukunna.”
Mikewar kuwa tayi tana fita suka dawo da Saratu da tun a hanya take tambayarta mene ne amman taki bata amsa har suka shigo gidan, ita kadai ta zauna ta kalli Yelwa da murmushin da yake fuskarta don ita ta kasa zama, da alama zumudi na cinta.
“Baba ka fada mata.”
Cewar Yelwa tana saka Datti yin dariya sosai.
“Idan na zabar miki miji zaki yarda da zabi na?”
Julde ya gilma ta cikin idanuwanta, sawayen shi na bayyana a cikin zuciyarta har numfashinta na mata barazana da ta hada kalmar miji, mijinta ta hango babu hoton shi a wannan hadin. Lumshe idanuwanta tayi tana aunawa, soyayyar Datti da ta taso da ita ko ta Julde data tsinta akan hanya. Tana jin wani abu da yake karyewa a cikin kirjinta.
“Baba kasan ba zanki zabinka ba, wanda duk ka zabarmun ina so.”
Amsarta ta sanyaya zuciyarshi, ta saka wata kauna da yake mata tasowa ta shimfidu har a cikin idanuwan da yake dubanta dasu.
“Kaga ‘yarka…”
Da Hammadi kan fada baiyi karya ba. Girman da ta bashi na taba har ruhinshi.
“Zan hadaki aure da Julde…”
Maganar ta dirar mata, a zaune take, amman sai ta sakejin kamar ta kara zama, zama daban da wanda tayi tun shigowarta gidan. Zama da sanin wahalarta ta kare.
“Don ina da yakinin ba zai cutar mun dake ba.”
Datti ya fadi da tabbacin da bashi da shi.
Yayi kalaman da zaiyi dana sanin su a gaba.