Idan yace baya so ya daina abinda yakeyi zaiyi karya, ba don kowa ba sai don Dije, sai dan yanayin da yake gani shimfide a cikin idanuwanta duk lokacin da Datti ya bude baki ya bishi da kalaman da suka zame masa jiki yanzun."Allah ya isa"Wannan sune masu sauki a cikin kalaman Datti da suke fitowa daya bayan daya kamar ya jingine alakar da take tsakanin shi da Julde, yayi katanga da duk wata soyayya da ta taba giftawa a tsakaninsu. Idan Julde ya rufe idanuwan shi yana tuna lokuttan da suke zaune karkashin inuwa daya da Datti. . .