Ba don wani ya fada mata cewar don an haifeta a marake, ta girma, tayi aure anan zata kare sauran ranakun ta a cikin kauyen ba. Kawai a jikinta take jin cewa anan din za'a binneta wata rana, ko da zata bar Marake sai dai tayi tafiyar da sunan ziyara, ba wai bari na gabaki daya ba. Duk wani abu da yake da muhimmanci a wajenta a ganinta ya fara ne daga Marake, ya fara daga tsatsonta. Ta gilashin motar take kallon titi, take ganin bishiyoyin da suketa wucewa suna kara tazarar da take tsakaninta da Marake.Shikenan? Da. . .
Masha Allah Muna gdy
Inaji a jikina chan zata hadu da bukar da yelwa mafari Zai hade wuri daya muje zuwa
In luv of dis but
Kudos lubna👍👍👍
Kudos lubna 👍