Tun tasowarta, koya ta juya zata ga Daada a kusa da ita. A wautar tunani irin nata ko a mafarki bata taba hasaso nisa da Daada irin haka ba. Ace ba unguwa bace a tsakaninsu, ba gari bane ba, kasa ce kacokan a tsakaninsu. Awanni ne masu yawan gaske idan akace lissafasu za'ayi. Komai ba tajin dadin shi. Duniyarta tayi tsaye waje daya, tana zaune kawai sai taji hawaye na cika mata idanuwa. Duk da taji muryar Daada yafi a kirga yanzun, ta ganta a video calls din da Nawfal ya kirata yana hadasu. Ta tabbatar mata da cewar. . .
Dan Allah karki tarwatsa book dn nn da Wnn kaddarar
Dan Allah Kar ki muna haka badai Madina ba