Duk labarun tashin hankalin da yake ji basu taya shi shiryawa zuciyar shi wannan da yake so wani ya girgiza shi yace masa mummunar mafarki ne yakeyi ba, ko a tarihi ba zai tuna kunnuwan shi sun tsinkayo mishi wani yana bada labari kwatankwacin abinda yake gani yanzun ba. A tsaye yake akan kafafuwan shi, har yanzun yana da tabbacin akan kafafuwan shi yake tsaye saboda yana jin sunyi sanyi. Duniyar da yake tsaye akanta ne ta birkice dashi tana nuna masa iyakarsa. Kamar awanni ba kasa da dakika ba haka yaji tsakanin rufe idanuwan shi da yayi ya sake. . .
Aiki ja
Hmmmmm. Babbar magana.
Wai