Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Ranar Birthday by Abba Abubakar Yakubu

Aisha Abdulhamid ɗaya daga cikin ƙawayen Ruƙayya ita ce ke gabatar da taron wato MC, kuma yarinya ce da Allah ya yi wa azancin harshe da iya tsara magana, tana karatunta ne a kwalejin koyar da aikin watsa shirye shiryen talabijin da rediyo ta NTA da ke Jos, inda ta ke koyon aikin jarida.

Fara ce doguwa mai dan madaidaici jiki, da kyan diri. Tana sanye ne da doguwar riga, baka, sakakkiya, da aka yi wa adon farin zare da ja a gaban rigar, ta kuma ɗaure kanta da babban farin gyale da aka zarga shi ya zama kamar hijabi, takalminta mai tsinin dunduniya ya ƙara mata tsayi. Tubarkallah!
Bayan an buɗe taro da addu’a, sai aka gabatar da ƙirjin buki, Ruƙayya Abdallah, domin ta gabatar da taƙaitaccen tarihinta da kuma maƙasudin shirya wannan liyafa da wani baƙon salo da ba a saba da shi ba.
A natse cikin murya mai cike da ladabi da ƙasƙan da kai Ruƙayya ta ba da tarihin rayuwarta, tun daga makarantar farko da ta fara a gaban mahaifiyarta, da makarantar asuba, inda suke zuwa da sauran ‘yan uwanta, har zuwa makarantar Islamiyya da boko ta suka yi a matakin firamare wacce ake yi wa laƙabi da Tanbihus Sunnah da kuma sakandire da ta yi a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta G.S.S Gyel, inda ta yi ƙaramar sakandire, daga bisani kuma ta koma Hikima Academy, har ta kammala da sakamako mai kyau. “Yanzu haka kuma ina daga cikin rukunin daliban farko da suke nazari kan sabuwar fasahar kula da lafiyar dabbobi, wanda shi ne irin sa na farko da wata makaranta a duk fadin Nijeriya ke koyar da irin wannan kwas. Kuma nan ba da dadewa ba cikin yardar Allah ina sa ran kammala ƙaramar Diploma ta, tare da fatan ubangiji ya ba ni damar dorawa zuwa babbar Diploma.”

“Allahu Akbar!”

Ɗakin taron ya ruɗe da kabbara, domin jin daɗin yadda wannan matashiya ta samu nasarori a rayuwarta, duk da ƙanƙantar shekarunta, da ƙalubalen karatu da take fuskanta, amma ta tunkari wannan hidima ta ganin ba ita kaɗai ta samu RAYUWA MAI ALBARKA ba har ma da sauran ‘yan uwanta mata.

“Ya zama tilas a gare ni in yi godiya ta musamman da jinjinawa ga iyayena, musamman mahaifiyata, waɗanda suka tsaya tsayin daka, domin tabbatar da ganin rayuwata da ta sauran ‘yan uwana ba ta lalace ba, kuma mun samu ilimi da tarbiyyar addini yadda ya kamata.” Sai kawai aka ga ta durkusa kan gwiwoyinta cikin murya mai alamun shassheƙar kuka, tana cewa. “Ummi, na gode da irin tarbiyyar da ki ke mana, ba ki bari ruɗin rayuwa da lalatattun ƙawaye ko samari sun ja hankalin mu ga saɓawa Allah da kaucewa tarbiyyar addini ba. Da fatan za ki yafe mana kurakuran da muka yi miki, saboda ƙuruciya da rashin sanin ciwon kai. Ubangiji Allah ya sa mu tare da ke a Aljannatul Firdausi, ya kuma ja mana kwananki!”

Waɗannan kalamai na sanyaya zuciya ya sa wasu da dama zubar da ƙwalla, musamman ita mahaifiyar Ruƙayya, Hajiya Sa’adatu, wacce ta taso ta kama hannun ‘yarta kuma ‘yar lelenta ta miƙar da ita daga inda take durƙushe. Ɗakin taro ya yi tsit kamar ruwa ya ci makaɗi, sai dai sautin masu shassheƙar kuka da ake ɗan ji ƙasa ƙasa. Jim kaɗan bayan an ɗan samu natsuwa, Ruƙayya da sauran baƙi sun dawo hayyacin su, ta cigaba da bayanin dalilanta na shirya wannan liyafa, domin amfani da wannan rana wajen faɗakar da ‘yan mata yadda ya dace a shirya bukin murnar zagayowar ranar haihuwa, cikin tsafta da mutunci. Ta kuma yi alkawarin idan Allah ya ja kwananta ya sa tana da sukuni za ta cigaba da shirya irin wannan taro, tare da yi wa jama’a godiya da irin haɗin kai da goyon baya da suka bata na halartar wannan liyafa, da sauran ƙawaye da suka tallafa mata.

Daga bisani kuma sai aka shiga fagen wa’azi da nasihohi game da ƙalubalen da ke gaban matasan mata a ɓangaren ilimi, tarbiyya da zaɓen miji nagari.

*****

Labarin wannan liyafa ta Birthday da Ruƙayya ta gudanar ya karaɗe garin Ɓukur har ma zuwa cikin Jos, inda ya zama jigon wa’azin malamai da nasihohi a makarantun ‘yan mata da samari. Domin jan hankali da ƙarfafa gwiwa ga Musulmi su riƙa tsaftacce ayyukan su don su dace da koyarwar addinin Musulunci. Ita kuwa jarumar, sai addu’o’i take sha da sa albarka daga bakin iyaye da ‘yan uwa. Wannan buri nata ya cika, cikin izinin Allah.

Sai dai kuma wata sabuwar barazana da ta tunkaro ta shi ne, kwararowar masoya, samarin ustazai da malamai, sai fitowa suke yi suna bayyana sha’awar aurenta. Ita kuma tana dakatar da su, cikin hikima, tare da sanar da su tana da wanda take so kuma za su yi aure, ba da daɗewa ba.

Muna yi mata fatan alheri a rayuwar ta, da fatan samun ɗaukaka da ƙarin basira da hazaƙa. Tare da fatan sauran ýan mata za su yi koyi da salon rayuwar Ruƙayya, wajen tsaftace rayuwa da riƙo da tarbiyyar iyaye, don samun albarkar rayuwa, da tsira a duniya da lahira!
ƘARSHE

<< Ranar Birthday 3

1 thought on “Ranar Birthday 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×