Tsaye take, jikinta sanye da farar riga doguwa kanta da mayafi fari. Ta yi kyau, fuskarta ɗauke da murmushi kamar koyaushe. Kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci mace ce mai kamala da haƙuri.
Ta mishi wani kwarjini da tun ranar da ya fara ganinta a rayuwarshi ya samu wajen zama a zuciyarshi.
“Aisha…”
Ya faɗi sunan na mishi wani iri akan laɓɓanshi.
“Karka bar yaranka… Kar tsoron fuskantar su yasa ka sake barin su a karo na biyu…”
Cike da rashin fahimta yake kallonta, sai dai kafin ya tambayeta me take nufi ta juya ta ɗauki hanyar da sai yanzun yake ganin tsayinta.
“Aisha…”
**
Buɗe idanuwanshi ya yi wata irin zufa na tsattsafo mishi. Numfashi yake mayarwa, mafarkin na dawo mishi, kalaman Aisha na zauna mishi.
Tun da Tayyab ya fita ɗazun, ya sake kaya ya ɗan ci abincin da ya kawo mishi, yana jingina kanshi da gadon ɗakin bacci na ɗaukarshi. Ko a mafarki kalaman Aisha cike suke da hikima.
Baisan me ya faru tsakanin shi da Hajiya Beeba ba, yadda akai ko wanne riƙo ne tai mishi ya sake shi, abinda ya fahimta a yanzun guda biyu ne. Na farko kulle kanshi a ɗakin nan, kukan da yake da damuwa ba zai canza komai ba, ba zai taɓa dawo mishi da Aisha ba balle Sajda.
Ba zai sa shekarun da ya rasa su dawo ba. Abu na biyu kuma. Allah ne ya sake ara mishi dama ya yi amfani da sauran ranakun da suka rage mishi wajen ganin yaranshi sun yafe mishi.
Bai da tabbas akan sake yarda da shi, don abu ne da yake ɗaukar lokaci. Hakan kuma abu ne da ba shi da tabbas akanshi, kamar yadda rayuwa za ta iya birkice maka ba tare da shawara ba haka mutuwa za ta iya maka sallama ko ba ka shirya ba.
Ba haka Aisha za ta so ya ji mutuwarta ba. Addu’ar shi ita za ta buƙata, abinda za ta so bai wuce kar ya daina ƙaunarta ta hanyar yi mata addu’a ba. Ya ƙaunaci yaranta dai-dai iyawarsa.
Miƙewa ya yi ya shiga banɗaki ya wanke fuskarshi ya fito, ruwa ya ɗauka ya sha. Aiki yake da shi babba a gabanshi. Zai kuma fara shi daga yanzun ne. Duk wani minti ɗaya da zai wuce yana tafiya ne da damar da yake da ita.
Ya kuma daina asarar sauran ranakun da yake da su. Zai yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Da wannan tunanin a zuciyarshi ya fito daga ɗakinshi.
****
Tunda ya fito daga gidan su Labeeb nasu ɓangaren ya yo kai tsaye. Cikin falo ya tsaya, goshin shi ya haɗa da bangon ɗakin yana lumshe idanuwanshi.
Babu abinda yake mishi yawo cikin zuciyarshi sai yadda ya sa hannunshi ya daki Labeeb, sai maganganun duk da ya faɗa mishi, bayan akwai ɓangare na zuciyarshi da ke kokwanto kan maganar Labeeb ɗin.
Ya gode wa Allah da zuciya ba ta sa ya ƙi yi wa Labeeb abinda ya dace ba a lokacin mutuwar Arif. Da har ƙarshen rayuwarshi ba zai yafe wa kanshi ba, yanzun hakan ji yake kamar zuciyarshi za ta faɗo saboda nauyin abinda ya yi.
A wani ɓangaren kuma zulfa da abinda ya faru da ita sun mishi wani irin tsaye. Ba zai iya ƙiyasta abin ba saboda munin shi ya yi yawa. Ko ya ya ji kalmar ta faru akan wata yakan wuni da abin. Balle kuma ƙanwarshi.
Sai dai yana da tabbacin ƙaunar Labeeb za ta iya dishe mata tabon da Mamdud yai mata a rayuwarta. Faɗin sunan Mamdud ya dawo mishi da haushin shi da baisan yadda zai yi da shi ba.
Sanin ba a hayyacin shi yai wa zulfa abinda yai mata ba bai hana zuciyar Dawud tafasa ba. Bai hana shi jin wani irin ƙunci ba. Dafa mishi kafaɗa ya ji an yi.
Zuciyarshi ta buɗe wani waje da ya jima da jan ƙofa har da sa mukulli ya rufe. Ko da hannuwa goma za su dafa shi zai gane wannan hannun. Hatta iskar da yake shaƙa sai da ta sake mishi.
Ga zuciyarshi na wani irin dokawa. A hankali ya raba goshin shi da bangon ɗakin yana juyowa. Kamar wanda aka watsa wa wani abu ya ja da baya yana ture hannun Abba da ke jikinshi.
Numfashi yake ja yana fitar da shi da sauri-sauri saboda tun a asibiti zuciyarshi ke yaudararshi da sauyin da ke fuskar Abban.
“Dawud…”
Girgiza mishi kai Dawud ya yi, baya son yana kiran sunanshi da wannan yanayin. Baya son abinda ya sa zuciyarshi ji, baya son yadda yake shirin taso mishi da abubuwan da ya jima da haƙura da su.
“Don Allah ka ƙyaleni… Ka barni… Abubuwa basu jima da fara dai-daita a rayuwata ba… Kar ka dawo min da komai sabo.”
Da dukkan abinda ke zuciyar Abba yake so ya goge ciwukan da ke fuskar Dawud, ciwukan da uba ne kawai zai iya fahimtarsu ba tare da ganin alamar tabo ba. Yana son karɓar mishi nauyin da yake ganinshi ɗauke da shi shi kaɗai.
Tayyab ne ya shigo, ganin su tsaitsaye yasa shi kallon Dawud kafin ya kalli Abba.
“Tayyab…”
Abba ya kira, idanuwa Tayyab ya zuba mishi, yana jin yadda yake cikin yanayin nan, yadda kewar Ummi da Sajda ke damunshi babu abinda yake buƙata banda lallashi.
Ya gaji, ya gaji sosai da irin yadda rayuwa take ɗaukarsu tana jifa da su, ya gaji da yadda Dawud ne ke ɗaga su yana taya su jinyar ciwukansu a ko da yaushe ba tare da da ya damu da nashi ba.
Baisan lokacin da kuka ya ƙwace mishi ba, yana jin bai da wani amfani in har abu mai muni zai samu Zulfa ba tare da ya sani ba balle ai maganar ya kareta, da sauri Abba ya ƙarasa ya kama hannun Tayyab.
Kamar jira Tayyab yake, faɗawa ya yi jikin Abba yana sakin wani irin kuka mai taɓa zuciya, dam Abba ya riƙe shi yana son faɗa mishi har abada ba zai sake barin shi ya kubce ba.
“Abba fyaɗe akai wa Zulfa… Abinda nake ji… Nake ji kamar inje in ɗauke yarinyar da duk hakan ya faru da ita in ɓoye ta wani waje da zai mantar da ita… Akan ƙanwata Abba…”
Sosai Abba ya riƙe shi, shi ma kukan yake yi. Ba kanshi Tayyab zai ɗora laifin ba, sun yi iya ƙoƙarinsu, wani abin ya fi ƙarfinka ne. Shi da baya nan tare da su kuma baisan me zai ce ba.
In akwai abinda Dawud ya tsana bai wuce ya ga hawaye a fuskar ƙannen shi ba, kallon Tayyab da Abba yake, idanuwanshi kan Tayyab da ke rirriƙe Abba kamar zai koma cikinshi yana wani irin kuka.
Ya sani, ba tun yau ba yasan soyayyarshi kaɗai ta musu kaɗan, ba tun yanzun yasan suna buƙatar soyayyar da ta fi tashi ba. Ba sa nunawa ne kawai don kar ya damu.
Ƙirjinshi yake ji kamar an ɗora mishi dutse, bai gama kallon su Abba ba, Mami tai sallama, idanuwanshi ya janye daga kan su Abba zuwa inda su Mami suke.
“Abba???”
Zulfa ta kira cike da shakku bayyane a muryarta, cike da burika da dama, cike da son wani ya tabbatar mata da gaske Abban nasu ne, kai Abba ya ɗaga mata yana kasa magana saboda kukan da yake yi.
Hannunshi ɗaya ya miƙa mata, ƙafafuwan Zulfa har kyarma suke da dukkan jikinta kafin ta ƙarasa inda suke, gani take kafin ta je hannun Abban ya ɓace.
Bayan abubuwan da suka faru da su, bayan ‘yan kwanakin nan da suka yi su a hargitse, bayan ganin giccin asalin Abbansu ta san ƙarya take, duk wata tsana da take tunanin tana mishi ƙarya ce.
Bangwaye ne ta gina a zuciyarta don su kareta daga buƙatar mahaifinta da take a rayuwarta ta kuma san ya mata nisa. Soyayyarshi ce ta ƙarfi da yaji ta danne da ƙaryar ta tsane shi, da ƙaryar kamar yadda baya buƙatarta, ita ma ba ta buƙatarshi.
Sai yanzun ta gane hakan, ƙaunar Abba babu inda ta je daga zuciyarta. Tana nan daram, ta kuma taso mata jinta take ko ina, har ƙarshen rayuwarta ta san tana buƙatar kulawa da ƙaunar Abba.
Fiye ma da su Tayyab, don su maza ne, ba sa buƙatar Abba a rayuwarsu kamar ita. Hannun da ya miƙo mata na tuna mata lokutan da duk take tunanin ta manta su.
Sa’adda ta sha faɗuwa hannun Abba take kamawa ta miƙe, yadda da gudu take rugowa ta kama hannunshi ya ɗaukota daga makaranta, yadda in tana kukan hannunshin dai ke share mata hawayenta.
Yadda hannun nan da ya miƙo mata yake wuni aikace-aikace da rubutu don rayuwarta ta samu inganci, yadda hannun nan da ya miƙo mata ke haɗuwa da ɗan uwanshi wajen yi mata addu’a tun kafin ta diro duniya.
Hannunta na karkarwa ta miƙa shi cikin na Abba, ƙaunarshi na ƙara lulluɓe ta, kewarshi da ta yi na shekaru na dawo mata.
“Ab.. Abba…”
Ta faɗi a daburce kuka na ƙwace mata, janta Abba ya yi jikinshi yana haɗa su da Tayyab ya riƙe. Ƙaunarsu, kewarsu da girman abinda ya rasa na rayuwarsu na sa shi jin kamar zuciyarshi za ta fashe.
Yanayin yadda yake karantar wahalar da suka sha na saka shi jin wani irin ƙunci na daban. Mami kam kukan da suke yi ne ya sa ta kuka sosai. Yadda take ganin ƙaunar da ke tsakanin su, da yadda wasu matan babu zuciya a ƙirjin su.
Yadda za su shiga rayuwar mutum da iyalanshi su tarwatsata saboda son zuciya ba tare da tunanin mutuwa ba balle tsoron Allah na ba ta mamaki.
Har cikin kunnuwanshi Dawud ke jin yadda zuciyarshi ke bugawa. Su Zulfa ke riƙe da Abba amma shi yake ji musu tsoro, shi yake jin tsoron yadda suka yi saurin yarda Abbansu ne wannan.
Yadda suka yi saurin buɗe mishi zuciyarsu, baya ganin komai sai yadda hannuwan Abba da suke rungume da su Zulfa suka ɗibo kayayyakin su suka watsar a waje. Zuciyarshi na ƙara yi mishi nauyi.
Yana jin yadda baisan ta inda zai fara ba in Abba ya dagula mishi komai, baisan yadda zai maida su Zulfa dai-dai ba in har ya sake juyewa zuwa mutumin nan da ba Abbansu ba.
Wani tsalle zuciyarshi tai har cikin ƙirjinshi ganin yadda Abba ya sauke idanuwanshi cikin nashi, yadda yake tuna mishi abubuwa da ya jima da son mantawa.
Zuciyarshi ce ta rabu gida biyu kowanne ɓangare na kokawa da ɗayan wajen ganin ya yi rinjaye. Ɓangare ɗaya mutumin da ya maye gurbin Abbansu ne da abinda yai musu. Da ranar da ya watsar da su a karo na farko da suka fi buƙatarshi a rayuwarsu.
Ɗayan ɓangaren kuma Abba yake gani, Abbanshi da kalar ƙaunarshi a gare su. Yana kallon yadda ya saki su Zulfa, tsaye suka yi kowannen su a gefenshi suna kallon Dawud da idanuwansu da ya canza launi saboda kukan da suka yi.
Hannu Abba ya miƙa wa Dawud, da sauri ya matsa yana haɗe jikinshi da bangon wajen, juyawa ya yi ya ga babu inda zai sake matsawa in ba cikin bangon zai shige ba.
Juyowa yayi yana sake girgiza wa Abba kai.
“Dawud… Ka yafe min… Zan gane in yarda da ni zai maka wahala… Nauyin ku zai min wuyar ɗauka… Don Allah ka yafe min…”
Abba ya ƙarasa hawaye na zubar mishi, zuciyarshi na mishi ƙuna da yadda yake kallon ɗanshi na kokawa da sake ƙaunarshi, yadda yake tsoron ya zo kusa da shi.
“Don Allah ka ƙyale mu… Ba ka ganin ka taɓa rayuwarmu ta wajaje mai ciwo? Ba ka ganin mun cancanci mu samu farinciki?
Me yasa za ka dawo yanzun? Bayan mun haƙura… Ka kalle su… Ka kalli yadda ƙaunarka na mintina ta gigita su… Ya kake so in yi da su in ka sake tafiya?”
Dawud ya faɗi muryarshi a dishe. Yana jin kamar numfashin shi zai ɗauke saboda tashin hankali. Girgiza mishi kai Abba yake yana son gaya mishi babu inda zai je. Wannan karon mutuwa ce kawai za ta raba su.
Da kanshi ya taka ya ƙarasa inda Dawud yake, duk yadda Dawud ke ƙoƙarin shigewa cikin bangon, ganin da gaske Abba so yake ya ƙaraso ya taɓa shi yasa shi saka hannuwanshi duka biyun yana ture Abba da su.
Kamar wanda ya samu taɓin hankali Dawud ke ture Abba yana faɗin,
“Ka ƙyaleni! Na ce ka ƙyaleni ko? Kana ina sa’adda nake buƙatar ka taya ni kula da su? Sai yanzun za ka dawo? Sai yanzun? Da kaina na zo kiranka Ummi na buƙatarka ka ƙi ka zo… Shi ne kawai abinda take so… Ko ba ta rasu da aurenta ba ta ganka!”
Kama hannuwan Dawud Abba ya yi, maganganun da yake yi na ƙara gudun kukanshi, amma sam ya ƙi, fisge hannunshi ya yi yana sake ture Abban baya da dukkan ƙarfin shi. Hawaye masu zafi ne ke zubo wa Dawud.
“Ka sake ni! Da hannunka ka kore mu… Da hannunka ka watso mana kayanmu… Ka ce ba ka son ganin mu… Me yasa sai yanzun? Kana ina Ummi ta bar mu? Kana ina ta bar min jariri da bansan yadda zan yi da shi ba?”
Takowa Abba ya yi yana ƙara nufo Dawud ɗin, su dukkansu kuka suke, su dukkansu abubuwan da suka faru da rayuwarsu ke dawo musu da wani irin ciwo.
Sake hankaɗe shi Dawud ya yi.
“Me ya sa ba za ka ƙyaleni ba… Ni kaɗai na kula da su… Ban mutu ba… Ni kaɗai na rufe Ummi… Ba ka nan! Bana iya bacci saboda ina tsoron ko ya na rufe idona da daddare wani abu zai same su.
Duk sa’adda na kalli Khateeb in na shiga ɗaki sai na yi kuka saboda bai san menene mahaifi ba… Baisan ya kalar Ummi take ba. Kar ka ce min sai yanzun kake son dawowa rayuwarmu… In su sun yarda da kai ni bazan iya ba! Sajda ba ta da buri da ya wuce ta zama yarinyar da za ka yi alfahari da ita… Ta zama wata ko za ka dawo rayuwarmu. Sai yanzun? Ka koma inda ka fito ba ma buƙatar ka…”
Kuka Abba yake har numfashin shi ke shirin ɗaukewa, sai dai ba zai taɓa barin su ba, ko ya kalaman Dawud za su yi mishi ciwo ba zai barshi ba, sake zuwa ya yi ya kama hannuwan Dawud da ke wani irin kuka da tun rasuwar Ummi rabon da ya yi irin shi.
Yau Abba ya famo mishi da komai, duk ciwukan shi da bai yi jinya ba saboda ba shi da lokacin yin hakan sai dai ya ɓoye su suka fito fili suna mishi zugi. Kamar Abba na zuba mishi gishiri a jikinsu haka yake ji.
Kiciniyar ƙwacewa Dawud yake yi sai dai wannan karon bai da wani ƙarfin kirki, don haka ya durƙushe a ƙasa gaban Abba yana sakin wani irin gunjin kuka. Da gudu Tayyab da Zulfa suka ƙaraso wajen shi suna zama.
Kama hannuwanshi suka yi suna kuka suma, maganganun shi sun fama musu ciwukan da suka ji. Girmanshi da ƙaunarshi na ƙaruwa a zuciyoyin su. Dawud shi kaɗai ya basu kulawar mutum uku.
Ya basu ta Ummi, ya basu ta abba, sannan ya basu ta ‘ya’yanshi. Sosai suke ganin girman abinda yai musu ba tare da nuna gajiyawa ba, suna jin ƙaunarshi, duk da kukan da yake bai hana shi kama su jikinshi yana ƙoƙarin lallashin su ba.
Duk da wannan karon ya fi su buƙatar lallashin, a jikinshi suka kwantar da kansu suna kuka. Zama Abba ya yi ya sa hannuwa yana tallabar fuskar Dawud da ke son ƙwacewa amma Abba ya riƙe ta dam.
“Babu inda zan je… Ka yarda Dawud… Bazan taɓa gyara kuskurena ba… Wallahi ba zai gyaru ba….bazan taɓa gane halin da na saka ciki ba… Sai dai na maka alƙawari daga yau har ƙarshen rayuwata… Bazan sake barinka ka ɗauki komai kai kaɗai ba…”
Kallon shi Dawud yake yi, zuciyarshi ta fi ƙarfinshi a wannan karon, din yana jin yadda take buɗewa da ƙaunar Abba da Allah ya halicce shi da ita, bayan Ummi Abba ne mutum na biyu da zuciyarshi ta rayu da shi.
Za kuma ta mutu da shi. Baisan abinda zai ce ba.
“Ruwa… Ruwa zan sha…”
Dawud ya faɗi, da sauri Abba ya miƙe ya nufi kitchen yana fitowa da ruwa da kofi, kallon shi Dawud yake yana zuba mishi ruwan har ya kusa cika kofin ya miƙo mishi.
Karɓa ya yi ya sha, sai da ya kusan shanye ruwan tukunna Abba ya karɓi kofin ya ajiye. Buɗe baki Dawud ya yi.
“Abba…”
Ya faɗi yana jin sunan na sake rayuwa a zuciyarshi, hawaye ne suka ƙwace wa abba, hannu Dawud ya kai yana taɓa fuskar Abba, yana jin babu abinda ya canza mishi a jikinta duk shekarun nan.
Sosai kuka ya ƙwace mishi, rashin Ummi da Sajda na dawo mishi sabo saboda yadda zuciyarshi ta ji ta samu wanda zai lallashe shi, da sauri Abba ya matsa ya sa hannu yana goge wa Dawud fuskarshi.
Kuka Dawud yake yana faɗin,
“Don Allah Abba kar ka sake barin mu… Kar ka sake barin mu…”
Kai Abba yake ɗaga mishi, ɗaga shi su Zulfa su ka yi, da sauri ya ƙarasa yana kwantar da kanshi a jikin Abba kamar ƙaramin yaro yana sakin wani kukan, kanshi Abba ya ɗora a bayan Dawud.
Zulfa da Tayyab suna dora nasu jikin kowacce kafaɗa ta Abba. Kuka kawai suke yi, abinda ya faru da su suke amayarwa yau. Ƙaunar da ke tsakanin su na fifita musu ciwukan da ke musu zafi.
***
Ya rasa abinda ya kamata ya ji, ya rasa tunanin da ya kamata ya tsaida zuciyarshi akai. Maganganun Zulfa sun warware mishi wani abu da yake ƙulle da zuciyarshi.
Burin shi da ya gama tarwatsewa akan Mamdud yake jin ya dawo. Inda yake zaton Mamdud ya tsallaka da babu dawowa har abada ya canza mishi.
A ƙasan duk yanayin da yake ji akwai farin ciki na nasara. Zai auri Zulfa, za ta dawo ƙarƙashin kulawarsa gaba ɗaya, zai daina tashi da fargabar wanda duk ta aura zai iya mata gori akan ƙaddarar da bata da laifi a ciki.
Yadda ya zaci fitowar gaskiyar cikin Zulfa daban da yadda ya faru. Komai ya zo cikin sauƙi. Wata irin dokawa zuciyar shi ta yi.
“Tee…”
Ya furta a fili, yasan yadda ta tsani ƙarya a rayuwarta, yasan yadda take son ya gaya mata gaskiya ko ya za ta yi mata ciwo, sai dai a cikin al’amarin da ya faru bai da wani zaɓi da ya wuce yi mata ƙaryar.
Sauke numfashi ya yi mai nauyin gaske, yana tunanin laifukan da ya yi mata cikin satikan nan, da ƙyar ya samu ya ture tunaninta gefen zuciyarshi. Ba yanzun ba tukunna.
Gani yake asibitin ya ƙara mishi tsayi yau, da tunani barkatai a zuciyarshi ya ƙarasa Harmony yai parking ɗin motarshi. Sai da ƙafafuwan shi suka fara taka cikin asibitin tukunna zuciyarshi tai wani irin matsewa.
Babu abinda yake so ya gani sai Mamdud ɗin, ya ga da gaske ya tashi, Allah kaɗai yasan yanayin da zuciyarshi take ciki akan Mamdud a kwanakin nan, dauriya kawai yake yi saboda su Asad na buƙatar hakan daga gare shi.
Har ƙasan zuciyarshi yasan ba zai iya jure rashin wani ɗan uwan ba. Yana kuma son magana da su Asad, a bakinshi suka ji ƙaryar cikin Zulfa , a bakinshi ya kamata su ji gaskiyar komai.
Zuciyarshi na dokawa da ƙarfin gaske ya sha kwanar da za ta kaishi ɗakin da Mamdud yake. Ko sallama bai yi ba ya tura ɗakin. Su duka biyun suka juyo suna sauke idanuwansu akanshi.
Wani sanyi-sanyi ya ji ganin farin cikin da ke shimfiɗe kan fuskokin su, abinda ya kwana biyu bai gani ba, baisan yadda yai kewar ganin su cikin walwala ba sai yanzun. Ƙarasawa ya yi cikin ɗakin yana tura ƙofar.
Ya maida hankalin shi kan Mamdud…an cire mai robar abincin da ke hancin shi, haka babu ƙarin ruwa a jikinshi, yanayin fuskarshi ya ɗan canza fiye da kullum da yake ganin kamar bai da jini a jikinshi.
“Ku ka ce min ya farka?”
Labeeb ya faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi.
Kai suka ɗaga mishi, Asad na amsa shi da
“Ya farka…magunguna ne basu sake shi ba. Bacci ya koma…doctor ya ce ko yaushe zai iya tashi.”
Numfashi Labeeb ya sauke yana janyo kujera ya zauna ya fuskanci su Asad, yanayin fuskarshi ya sa Anees faɗin,
“Yaya lafiya dai ko?”
“Bani ruwa in sha Asad.”
Labeeb ya buƙata ba tare da ya amsa tambayar da Anees ɗin yai mishi ba. Ruwan ya bashi ya sha sosai tukunna ya kalle su.
“Bansan ta inda zan fara ba… Ina son faɗa muku wani abu, ku dukkan ku. Zee Zee ba ta kusa kuma…”
A ɗan tsorace Asad ya ce,
“Menene? Na kira Ishaq ma na faɗa mishi Yaya Mamdud ya tashi. Kasan Zee ban faɗa mata ba tukunna. Ya ce in sun samu jirgi yau za su taho ma… Saboda ba ta da nutsuwa tunda suka tafi.”
Sai da ya ɗan yi jim kafin ya ce,
“Bari ta zo ɗin… Maganar za ta iya jira.”
Nazarin fuskarshi suke yi, yana jinsu, hakan ya sa shi kauda kai gefe yana nutsar da hankalin shi akan Mamdud. Sau ɗaya yake son yai maganar nan yadda zai wuce ta har abada.
Dukkan ƙarfin gwiwar da ya rage mishi ne zai yi amfani da shi ya faɗa musu abinda zai faɗa musu. Yasan babu abinda zai rage da zai yi amfani dashi wajen faɗa wa Zainab in ta zo , kuma ya fi so ta ji daga bakin shi.
“Kasan muna nan dai in kana son magana ko?”
Anees ya faɗi muryarshi cike da damuwa. Murmushi Labeeb ya yi,
“Anees ni zan kula da ku… Not the other way.”
Langaɓe fuska Anees ya yi.
“Na sani, muma muna son kula da kai wasu lokutan ai.”
“Kar ka damu… Komai zai yi dai-dai.”
“Allah Ya sa haka.”
Suka amsa da amin. Wani irin shiru ya ziyarci ɗakin. Kowa da tunanin da yake yi a zuciyarshi. Motsi Labeeb ya ga Mamdud ya yi, jan kujerar shi ya yi kusa da gadon sosai yana kallon Mamdud ɗin, sake motsawa ya yi.
Idanuwanshi yake jin sun mishi wani irin nauyi kamar buɗe su ɗin zai mishi wahala, ga kanshi kamar an zuba ruwa ciki haka yake ji, da dukkan ƙarfin da yake ji a jikinshi ya buɗe idanuwanshi a hankali.
Sai dai dishi-dishi yake gani, ga hasken da ke shiga har cikin kanshi, ko ina na jikinshi yake ji a ƙuƙƙulle, magana yake ji cikin kunnenshi amma ya kasa fahimtar abinda aka ce.
Sake runtse idanuwanshi yayi ya buɗe su, a hankali komai yake dawo mishi da wani irin yanayi. Hatsari ya yi…Arif ne ya rasu! Wani irin matsewa zuciyarshi ta yi waje ɗaya.
“Mamdud kana jina…”
Sai lokacin ya fahimci abinda Labeeb ɗin yake cewa. Sai dai yana juyo da kanshi maimakon ya ga Labeeb ɗin likita ya gani. Tambayoyi yake wa Mamdud amma sam harshen shi ya mishi nauyi cikin bakin shi.
“In kana gane me nake cewa ka ɗaga kanka.”
Likitan ya faɗi, ɗaga mishi kai Mamdud ya yi, ‘yan dube dubenshi ya yi tukunna ya ce in dai zai iya ya sha ko da yoghurt ne. Tukunna ya fita, gefen gadon Labeeb ya zauna.
Sai yanzun gaba ɗaya gajiyar dake tattare da shi kan Mamdud ɗin take danne shi, dukkan tsoronshi yake dawo mishi. Muryarshi ɗauke da wani yanayi ya ce
“Ya Rabb… Na ɗauka… Na ɗauka rasa ka zan yi kaima.”
Idanuwanshi Mamdud ya tsayar akan Labeeb ɗin, yana karantar gaskiyar abinda ya faɗa akan fuskarshi, bai san kalar zuciyarshi ba, ba wannan yanayin ya kamata ya gani ba.
Bayan duk abinda yai mishi, tsanarshi ita ya kamata ya fara gani cikin idanuwan Labeeb ɗin, ko ya manta shi ya kashe Arif ne.
“Ni na kashe shi… Ni na kashe Arif…”
Mamdud ya faɗi yana jin yadda muryarshi ke fita kamar ba tashi ba. Da tashin hankali Labeeb yake kallonshi.
“Kanka ya bugu da yawa… Ka daina magana sai ka ƙara hutawa.”
Yanayin shi Mamdud ya kalla, da hannunshi da ƙafarshi, wani murmushin takaici yayi, bai shirya wa mutuwa ba ya sani, saboda haka ba zai yi fatan zuwanta da wuri ba.
Runtse idanuwanshi ya yi yana jin zuciyarshi na ƙuna, tana tafasa, babu abinda ke dawo mishi sai muryar Arif. Babu abinda yake gani a zuciyarshi sai fuskar Arif ɗin.
Tsayawa kawai zai yi, juyawa kawai zai yi ya saurari Arif ɗin amma bai yi hakan ba. Har a zuciyarshi da niyyar ya barsu har abada yake tafiya. Ashe da gasken barin Arif ɗin zai yi. Yana ji hawaye masu ɗumin gaske suna zubo mishi ta gefen idanuwanshi.
“Juyowa…juyowa kawai zan yi in ji shi na ƙi… Saboda me ban juyo ba? Saboda me na ƙi jin kiran da yai min?”
Mamdud ke faɗi yana jin wani irin ɗaci, hawaye masu zafi na zubo mishi, bai taɓa haihuwa ba, amma akan Arif yana jin kamar ya rasa ɗanshi ne, raɗaɗin hakan ba zai taɓa misaltuwa ba.
Asad da Anees da har yanzun basu san yadda akai Arif ya rasu ba, don har yanzun akwai alamar tambaya akan sanadin rasuwar Arif ɗin, sun san ko sun ji ba zai canza komai ba, ba zai dawo da Arif ba.
Sun ƙyale Labeeb ɗin ne ya soma magana da Mamdud ba don ba sa son yin hakan ba, sai don sun ga damuwar da yake ciki ta fi tasu. Sosai Mamdud ya kalle su. Da ƙyar yake magana ya ce,
“Asad ni na kashe shi…da na juya da bai tsallako titi ba…”
“Karku saurare shi Anees…kanshi ya bugu da yawa…”
Labeeb ya faɗi, koya ya ƙifta idanuwanshi sai ya ga yadda motar nan tai sama da Arif na dawo mishi kamar yanzun abin ya faru, bayan ya samu da ƙyar ya kauda shi gefe.
“Ba abinda ya samu kaina… Ka fi kowa sanin gaskiya nake faɗa.”
Murya can ƙasa Asad ya ce,
“Yaya me yake faɗi haka?”
“Shirme…”
Labeeb ya amsa shi, kallon su Mamdud yake yi, sosai hawaye ke zubar mishi. Kukan mutuwar Arif yake, don a wajenshi sabuwa ce. Ɗan ɗaga kafaɗa Anees ya yi.
“Mu duka muka rasa shi Yaya Mamdud… Ɗora laifin mutuwarshi akanka ba zai dawo da shi ba. Har yanzun nakan ji kamar kiranshi zai shigo wayata duk idan lokacin wayarmu ya yi.
In bacci ya ɗauke ni nakan farka da jin kamar yana cikin rayuwarmu sai na tuna zuciyata ke ciwo sosai…”
Ya ƙarasa maganar yana runtsa idanuwanshi don yadda yake ji kamar an zuba mishi gishiri a raunukan da ya yi ne. Idanuwan Asad cike da hawaye yake faɗin,
“Dukkan memories na Arif da nake da shi sun kulle a wani waje da na kasa nemo su… Babu wanda yake zuwa min sai wanda nake ƙoƙarin mantawa da duk numfashin da na ja.
Bana jin a duniya akwai abinda zai taɓa kai binne wanda kake ƙauna wahala… Abinda zai kai rashi irin wannan zafi. Yaya Mamdud kasan me ke tare hawayena in suka zo zuba?”
Asad ya ƙarasa yana kafe idanuwanshi kan Mamdud da ke wani irin kuka. Kafin ya ci gaba da cewa,
“Tunanin Allah ya bar mana kai… Tunanin da gawa biyu zan binne a rana ɗaya… Tunanin Allah ya bar mu da rashin Arif kawai… Don Allah karka sa mu wani ciwon fiye da wanda kake ciki… Don Allah Yaya ka ce ya daina kukan nan…”
Asaad ya karasa muryarshi na karyewa, yana jin yadda yake kokawa da numfashin shi. Sai dai abinda yai tsaye a wuyan Labeeb da maganganun da suka yi ya hana kalma ko ɗaya fito mishi. Sakkowa ya yi daga kan gadon yana ƙarasowa inda Asad yake.
Rungume shi ya yi, don baisan abinda ya kamata ya ce mishi ba, yana son raba ciwon da suke ji tare da shi, don yasan ba zai taɓa iya cike musu ramin da Arif ya bari ba. Sai dai zai iya taya su jinyar ramin har su saba da shi.
Sosai Asad ya riƙe Labeeb ɗin yana jin kamar ya koma cikin shi ko zai ɗan samu sauƙin abinda yake ji. Ƙarfin hali kawai yake yi. Bayanshi ya ji Anees ya dafa, hakan ya sa shi kallon Anees da ya ce mishi
“Ba zamu taɓa komawa dai-dai ba…za mu koyi zama da rashin da muka yi…”
“Are you sure?”
Asad ya buƙata, ɗaga mishi kai Anees ya yi, ba don shi ma baya buƙatar lallashin ba, sai dai Asad ya fi shi rauni sosai, ko tasowar su abinda zai taɓa Asad ɗin bai da wahala.
Sakin Labeeb Asad ya yi.
“Yaya Mamdud ya fi ni buƙata…”
Matsawa suka yi su duka biyun jikin gadon Mamdud ɗin, Labeeb ya koma inda yake zaune gefen gadon. Hannunshi mai lafiyar Asad ya riƙo, aikam kamar jira Mamdud yake ya dumtse hannun Asad ɗin gam.
Kuka yake yana faɗin,
“Ku yafe min…don Allah ku yafe min… Wallahi bazan iya rasa ku ba kuma…”
Labeeb kaɗai yasan dalilin da ya sa Mamdud ke faɗin hakan. Zai yi ƙarya kuma idan ya ce kukan da yake yi baya ci mishi rai, in ya ce damuwar da yake gani kan fuskar mamdud ba ta ƙona mishi zuciya.
“Saboda me za mu barka? Ka taɓa ganin ƙannai sun bar yayansu?”
Anees ya tambaya. Kai Asad ya ɗaga da faɗin,
“Kuma kai ne ma kwance kan gadon asibiti Yaya mamdud…”
Kallon su ya yi cike da ƙunar rai, kafin ya kalli Labeeb da ya girgiza mishi kai don ya gane tambayarshi yake ko sun san abinda yake faruwa. Sosai hawayen Mamdud suke ƙara zuba.
Ganin shirmen da yake shirin yi ne ya sa Labeeb saurin faɗin,
“Lokacin sallah ya yi… Mamdud me za ka ci? Doctor ya ce ka ci wani abu.”
Miƙewa su Asad suka yi suna nufar toilet don su yi alwala.
“Me yasa?”
Mamdud ya bukata
“Me yasa me?”
“Me yasa za ka tashe su bayan kasan gaskiya zan faɗa musu? Rashin Arif kaɗai ya ishe ni dauka… Me yasa za ka hana ni sauke dayan nauyin? Me ma ya sa baka tsane ni ba bayan duk abinda na yi maka?
Baka da zuciya ne a ƙirjinka? Ko ba ka san butulci ba? Baka san shi nai maka ba?”
Miƙewa Labeeb ya yi.
“Me za ka ci?”
Ya sake buƙata kamar Mamdud bai yi magana ba. Kau da kai ya yi hawayen takaici na sake zubar mishi, har su Asad suka fito suna fita daga ɗakin. Sam zafin da yake ji cikin jikinshi ya hana shi jin na ciwukan shi.
Wani abu da ke tsaye a wuyan Labeeb ya ƙi wuce mishi. Banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala. A nan ɗakin yai tashi sallar, ga hannuwanshi ya ɗaga sama sai dai a karo na farko ya rasa me zai roƙa. Ya rasa abinda ya dace ya fara roƙa.
“Allah Kai kake kyauta ga duk wanda Ka so, Allah ka ba wa Mamdud yara. Allah ka jarabce shi ta hanya daban banda wannan. Allah ka bashi yara masu albarka.”
Ya maimaita addu’ar ta kai sau biyar tukunna ya shafa yana miƙewa. Gefen gadon Mamdud ya koma ya zauna.
“Ka ji me doctor ya ce … Me za ka ci?”
Shiru ya yi ya ƙyale Labeeb ɗin ba don baya jin shi ba, sai don abinci na ƙarshen abinda yake zuciyarshi yanzun. Jin ya yi shiru ya sa Labeeb sauke numfashi
“Zan je gida in dawo… Zan roƙeka da ka riƙe gaskiya na ɗan wani lokaci kawai. Ba don ni ba ko kai, don su Asad…please kar ka ce komai.”
Yana rufe bakinshi su Asad na shigowa da sallamarsu, miƙewa Labeeb ɗin ya yi yana kallon su da faɗin,
“Zan je gida in dawo… Ku yi mishi magana ƙila ya saurareku ya ci wani abu.”
Kai suka jinjina mishi, bai sake cewa komai ba ya nufi ƙofa ya buɗe yana fita, zuciyarshi cike da rauni. Ko da ya buɗe motarshi ya shiga ya nufi hanyar gida wani irin dokawa zuciyarshi take kamar za ta fito daga cikin ƙirjinshi. Baisan ta yadda zai fara fuskantar Ateefa ba, baisan ta ina zai fara ba.
Sai dai yasan da duk mintinan da suke wucewa da ƙarin ɓata lokacin da yake yi, ba zai ci gaba da guje wa matsalar nan ba, gara ta sani kawai sai yasan yadda zai fara ba ta haƙuri.