LITTAFI NA BIYU
Binta ta yi qoqarin boye dukkan damuwarta a birnin zuciyarta, har ta gama kwasar gaisuwa a wajen Hajiya Inna kakar Nabila.
Dattijuwar mace wadda tsufa ya gama yi wa sallama, amma kirkinta sabo fil, ga kamala da yawan fara’a da alama duk halayen kirkinta Nabila ta kwaso.
Tana ganin Binta dayake ta san amincin da ke tsakaninsu da Nabila, ta hau kawo mata kukanta,
“Kin ga qanwarki ba kya yi mata fada ko Binta?’
Yaqe kawai Binta ta yi, don ba ta da abinda ya fi shi, fishin da ta kwaso da shi cikin gida gaba. . .