Skip to content
Part 20 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Kamar Mujahid ya san da wannan wasan da Binta ke shirin tsarawa, ranar ya dawo gida qarfe hudu na yamma koda yake cikinsa ne ya baci dole ya dawo gida saboda  ya sha magani ya kashe masa jiki.

Ya yi baccin sama da minti talatin kafin ya farka da sha’awar tauna wani abu a bakinsa, kasancewar tun safe ban da ruwan shayi babu komai a cikinsa.

Yana fitowa harabar gidansu ya ci karo da Nabila direban babanta ya sauke ta ya juya.

Wani irin zargi da neman ba’asi ya jibgo masa a zuciya tamkar zubowar gini, nan da nan ya ji wani bazawarin  kuzari ya zo masa da sauri ya qarasa ya tari Nabila yana yaqe.

“Nabila!”

Ya furta sunanta kawai, ya kasa dora wani abu bayan haka.

Nabila ta karanci dukkan yanayinsa, cikin wata irin karaya da sallamawa wanda ba ta iya yi wa kowa sai shi a duniya ta saki baki tana kallonsa, sai can ta nisa a sanyaye ta ce.

“Yaya Mujahid qalau?”

Ya fara waige-waige sannan ya juyo ya dube ta muryarsa qasa-qasa.

“Ke ya kamata na yi wa wannan tambayar, don zuwanki na ba-zata”.

Ita ma ta shiga waige-waige fuskarta da alamun shakka da tsoro, ba ta kai ga furta komai ba Mujahid ya yafice ta yana cewa.

“Kin ga zo mu je ki raka ni bakery din can na samo Shawarma sai mu tattauna a hanya.”

Bai ba ta damar wani zabin ba ya yi gaba, sai ta ji ba za ta iya yi masa musu ba, duk da ranta ya yi shakkar bin nasa, in Binta ta gansu fa? Me za ta zarga? Tabbas ranta zai sosu.

Haka dai ta bi shi a baya jikinta a sukuku tamkar ma ba tafiyarsu daya ba, har suka fice daga harabar gidan.

Suna fita ya dan dakata mata ta qaraso suka jera kafada da kafada.

Wani irin shauqi da Nabila ba ta taba jinsa ba ya silalo ya wafce ta, ya kai ta wata irin duniya wadda ta fi kowacce alfarma, ba don wani shegen waigi ya kawo wa alfarmar tata wawan naushi ba, da ta tuna wai tana cin wannan albarkacin ne sakamakon alfarmar za ta samar wa wanda ta ke so wata daban ba ita ba… an taba samun wata ko wani masoyi mai baqar qaddara irin tata kuwa?

Ta ji wani malalacin hawaye na son silmiyo mata, amma ta tura jarumtarta ta hadiye shi.

“Tun safe ban ci komai ba sai yanzu na ke son jefa wa uwar hanjina wani abu”.

Da wannan ya bude hirarsu.

Ta juya ta dube shi cikin kulawa, da haka ne ma ta lura ya dan fada, sai ta ji wani irin tausayinsa ya naushe ta, duk gabobinta tun daga zuciya zuwa gangar jiki suka mace.

Sai da ta gaji da kallonsa sannan ta kawar da kai a tausaye ba tare da ta iya cewa komai ba.

Ya dan juyo ya kalle ta saboda rashin tankawarta, bai karanci komai ba a fuskar tata, amma dai jikinsa ya yi sanyi, shi ma ya kawar da kai tare da qarfin halin kawo wata hirar.

“Allah ya sa dai kin iya tafiyar qafa, kin san da dan tazara.”

Ta dan juyo ta kalle shi tana dan murmushi, sai da ta kawar da kai sannan ta amsa.

“Idan ban iya tafiyar qasan ba ya ya za a yi tunda mun riga mun fito?”

Ya yi dariya ba tare da ya dube ta ba.

“Sai mu koma mu dauko mota ko babur.”

Ta gyada kai cikin kasa hankalinta fiye da biyu.

“To na iya tafiyar kar ka damu.”

Ya dan yi jim yana maqaqin tausayi da shiga haqqi, don haka suka dan yi shiru sosai babu wanda ya tanka, sai can Nabilan ta tsinka shirun.

“Me ya hana ka cin abinci tun safe?”

Ya kasa juyowa ya dube ta don yanzu tausayin ya yi masa rubdugu, ashe kulawarta ba za ta wuce kukan da ya yi mata na rashin cin abinci tun safe ba, ashe tana tune ba za ta manta ko ta zuba akwandon shara ba.

A raunane ya kada kai ya amsa mata.

“Ba na jin dadi ne, cikina ya dan hargitse, shi ne dalilin dawowa ta aiki na dan sami hutu, yanzu na tashi daga bacci na farka da yunwa.”

Wasu tawagar tausayi suka sake dirar mata a qirji, ta dinga jin ina ma ita ce mara lafiyar ba shi ba? Sai ta matsa wa fuskarta boye damuwa, duk da muryarta ta kasa boyewar.

“Oh! Sannu ko, Allah ya sa kaffara ce Yaya Mujahid.”

Da qyar ya iya tanka mata da, “Amin”. Don ya haqiqance wannan damuwa da kulawar ba a matsayin wa ya ke karba daga gare ta ba.

Ba ta tsaya a nan ba, sai da ta sake ce masa.

“Da ka sani aiko ni ka yi kawai na siyo maka, bai kamata ka qara gajiyar da kanka da wannan doguwar tafiyar ba.”

Ya daure ya yi murmushi bayan ya ji dolencin kawar da wannan kulawar da bai kamata ta tsiro a alaqarsu ba. Binta ya ke so,irin son da ba a juya baya don haka bai kamata ya dinga barin Nabila tana yi masa abin da ‘ya’yan tausayinta za su dinga kawo masa hari ba. Da muryarsa babu yabo babu fallasa ya ce.

“Kai haba kamar ni na aiki santaleliyar budurwa kamarki? Ai dukan sai ya yi yawa, ga wancan yaqin da na ba ki na yaqo min masoyiya, zai zama da hadama in na mayar da ke baiwa fiye da haka.”

Ta jima ba ta tanka ba, don ya yarfa mata zafi fiye da kullum, bai san tunda ya jona mata sonsa ya mayar da ita fiye da baiwa ba.

Da ya gaji da shirun sai ya soko zancen da ya ke jin ya fi kamatarsu.

“Na san kun yi waya da Binta yau ko?”

Kai tsaye ta kada kai idonta na kallon miqaqqiyar hanyar da suke bi.

“Ta kira ni jiya da yamma.”

Cikin tsananin zaquwa ya tambaye ta.

“Ita ta gayyato ki yau ko?”

Kada kai kawai Nabila ta yi ba don yana kallonta ba ma ba zai san amsar ba. Bai gamsu ba don haka har yanzu a zaqe ya jefo mata wata tambayar.

“Kiran da ta yi miki yana da alaqa da ni? Fada min don Allah.”

Ba musu Nabila ta kwashe labari ta ba shi, sannan ta qarqare da magana cikin raunin murya.

“Na zabi fada maka ne don ina da hasashen za ka yi wata dabarar ka kubuta, kawai hankalina ba zai kwanta ba idan ban ga ka samu cikar burinka ba.”

Duk qoqarin Mujahid da basarwarsa lamarin da sadaukarwa Nabila sun dake shi da kyau, sai dukan qwallon kansa kawai ya ke ya kasa cewa komai, muhimman abin nazarisu ne, Binta da gaske ta ke sai ta rabu da shi ko ta wanne hali, sannan hanyar da zai bi don hana ta cika burinta akwai Nabila a hanyar wadda duk wani yunqurinsa na qoqarin kasancewa da Binta ta’addanci ne a fuskarta da zuciyarta, duk da ta fansar wa sonsa da qaunar Antinta Binta.

Har suka kai wajen da suka nufa babu wanda ya sake tanka wa wani ya yi masa qunshin ya yi mata nata na dole tunda ta ce ba za ta ci komai ba.

Sun kamo hanyar fitowa suka hango motar Yaks a can gefen titi ya faka idonsa akansu, fuskar nan tasa tamkar mai jegon haihuwar fari, ta hango kwatarniyar ruwan zafi shaqe da ruwan zafin.

Lokaci daya duk su biyun suka yi turus kamar kuma sun hada baki sai suka rage dan saurin da suke kowa jikinsa ya mutu, musamman Nabila wadda da ma zuciyarta a raunane ta ke, kamar qiris ta ke jira ta narke.

Ba ta shirya ba ta ji bakinta na ambaton “Innalillahi.”

Da sauri Mujahid ya kalle ta kafin ya yi magana ta sake ambata.

“Wai me ye laifina ne da zan rasa me liqe min sai wannan? Gizo-gizon?”

Ba ta san maganar ta fito fili ba, da alama hankalinta na son yi mata nisa.

Mujahid ya dauke kansa daga kallonta zuwa kallon Yaks wani mugun takaicinsa da  tsanarsa ta qara rufe shi, da ma tun ranar da ya riqe masa Binta ya sumbatar masa ya ji babu dan Adam din da ya tsana sama da shi.

Da sauri ya yafici Nabila suka koma ciki, kai tsaye ya ja su kujerun masu cin abinci a nan suka zauna, fuskarsa a bace fiye ma da Nabilan.

Tsawon lokaci yana faman huci da karkade-karkaden takalmi gami da cije lebe, sannan ya juyo ya fuskance ta yana gyaran murya.

“Me ki ka fahimta akan tsarin da Binta ta shirya miki jiya da ta kira ki a waya? Yau din nan nake son in fuskance ta mu fara bugawa.”

Saqare kawai Nabila ta yi tana kallonsa, don gabadaya ba ta gane inda ya dosa ba.

Fahimtar hakan ya sa shi murza yatsu cikin zafin nama ya zabura ya miqe tsaye, sannan ya dogare hannayensa kan tebur yana fuskantarta kai tsaye yanayinsa na nuna alamar iyakar gaskiyarsa zai fada.

“Nabila!”

Ta dago ido kawai tana kallonsa ba tare da ta tanka ba.

Bai damu ba ya zarce da maganarsa.

“Binta da ki ke ganinta RIGAR SILIKI ta fi ta mutunci da tausaya wa wanda ya rabe ta, tabbas mace ce mai kirki, amma a kan ra’ayinta komai ma yi take, kuma kowa ma saba masata ke.”

Ya dan tsagaita ya shaqi numfashi ta hanyar hadiye yawu saboda maqogwaronsa wanda ya cushe da tsabar takaici. Ya dan dubi Nabila a kaikaice.

“Me ki ka fahimta game da shirin da Binta ta tsara miki jiya?”

Nabila ta yi tsuru tana kallonsa  kawai, sai can ta sunkuyar da kai qasa tana wasa da yatsun hannunta.

Abin da bai sani ba, kuma ba za ta iya fada masa ba shi ne, idan yana zaune kusa da ita, idanuwanta na kallon nasa suna shaqar iska iri daya, sam kwanyarta ba ta da sukunin wani nazari ko lissafi kamar yadda ba ta iya tankwabe duk wani ra’ayi ko iko nasa.

Ya ja qafa ya sake gyara zama cikin alamun fushi da son nutsuwa dole.

“A yau Binta ta so ta soke wani kaso na nagartar kyan hali da kyan dabi’u wadanda na sha rantsuwa a kan tana da su, kin ga za ta janyo min kaffara…”

Cikin sauri Nabila ta dago ta kalle shi da alamun rashin fahimta, jikinta da bakinta duk suna rawa ta ce masa.

“Idan haka ne na yi wauta da na sanar da kai yadda muka yi, ni na fada maka ne don zaton hakan zai maka amfanin sanin takun da za ka yi, ban fada domin na rage qimar Binta a idonka ba Wallahi.”

Da sauri ya girgiza kai ba tare da fuskarsa ta sauya ba.

“Yadda Binta ke da muhimmanci a duniyata haka ki ke da shi a cikinta, ya ya zan kasa jin ciwo idan Binta ta so ta ci da da guminki? Na san Binta da kyau, qarya ta ke miki,idan ta ce miki za ta aure ni don kin auri Yaks,. Oho! dama qiyayyar da ta ke min doronta don kina qin Yaks ne?”

Har yanzu Nabila kallonsa ta ke, ta kasa magana.

Shi kuma ya murza hannu ya ci gaba da cewa.

“Ita ya kamata ta amsa wannan tambayar, yayin da ke za ki yi mata tambayar.”

Nabila ta yi qarfin halin yunqurawa da qyar za ta yi magana, amma sai ya tare ta ta hanyar dakatar da ita da hannu.

“Ji nan Nabila, na gayyato ki cikin wanzar da soyayyata da Binta ba don in salwantar da rayuwarki ba, idan ina da ‘ya ko qanwa wallahi ba zan aura mata Yaks ba, hakazalika ta silata mace mai kirki irinki ba zan yarda ta fada hannun Yaks ba.”

Yanzu hatta bugun zuciyar Nabila ya sauya, ba ita kanta da ta ke jin kamar wata Nabilan aka sauya ba, komai qanqantar kulawa daga Mujahid ba qaramin rami ta ke haqa mata a zuci ba, balle irin wannan. Tana da muhimmanci a duniyarsa, yana kishin aurar da ita ga Yaks saboda rashin cancantarsa, wannan kulawa ce da ke tasowa qarqashin so na haqiqa, don haka ta ji farin ciki na neman ya kashe ta.

Bai fahinci halin da ta shiga ba don illahirinsa a birkice ya ke.

Ya dube ta sosai ya fara magana cikin kwantar da hankali da taushn murya,

“Nabila, ki kwantar da hankalinki, ki daina damuwa don Yaks ya zo yana sonki. Binta kawai za a tursasa ta auri wani namiji bisa dole, amma wallahi ban da ke. Zan sa ki a addu’a don haka ki ji yaqini cikin ranki, duk namijin da za ki aura sai kina sonsa dari bisa dari.”

Cikin azama ya miqe gami da buga tebur.

“Taso mu tafi.”

Tuni wasu sanyayan hawaye suka kawo wa idanuwan Nabila ziyara, hawayen daga zuciyarta suke kutsowa kai tsaye suna fadada zuciyarta, suna sama mata  sarari da farin ciki. Duk takura da takaicin da ta ji a yau gabadaya suka gushe, ji ta ke a ranta tunda wanda ta ke qauna fisabilillahi zai mata addu’ar ta auri wanda ta ke so, to albarkacin son da take masa saboda Allah, Ubangiji zai sama mata mafita.

Tana ta faman goge hawayenta cikin murmushi tana binsa a baya, yayin da ya ke tafiya da azama suka fice daga gurin.

Suna shiga harabar gidan Mujahid ya ga motar Yaks tsaye tana hutawa, Mujahid ya dan rage sauri ba tare da ya juyo ya dubi Nabila ba ya ce mata.

“Abin da na ke so da ke shi ne, kar ki nuna wa Binta kin janye daga abin da ta zaba miki, duk yadda ta tsara ki tafi a haka, ki bar ni zan ji da ita.”

Kada kai kawai ta dinga yi tamkar qadangaruwa.

“Zan yi waya da ke yau da dare ko gobe, na gode.”

Ya sake fada a gaggauce, sannan ya zarce da sauri ya bar ta.

Dole ita ma ta rabo kanta da shauqin binsa da kallo, lokacin da ya qule hanyar da za ta sada shi da dakinsa.

<< Rigar Siliki 19Rigar Siliki 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.