Alhaji Ibrahim karimin mutum ne wanda ya iya mu’amala da mutane, kamar yadda ya iya tarairayar mace da nuna mata soyayya, macen ma irin Binta wadda idan sonta ya shirya fada wa zuciya ba ya yi mata ta wasa.
Cikin qanqanin lokaci ya sami fada a zuciyar Binta, ko ba ta ji sonsa dari bisa dari ba, ta ji dari bisa darin babu laifi idan ta aure shi. In ba ta sami komai da komai da ta ke so a mijin aure ba, to tabbas ba shi da komai na abin da ta ke qi, don haka kai tsaye. . .