Sati biyu cif babu abinda ya sauya daga wannan, Mujahid na can kangon dakinsa da Binta ta sha kiyasta me ya qunsa, a gaban idonta dai ko kallon qofar dakinta bai taba yi ba bare ya gwada shiga. Iyakarsu da juna su hadu a tsakar gida ta wuce ya wuce babu mai ko dagawa juna yatsa bare a je batun gaisawa.
Duk abinda take buqata na daga dangin abinci ko kayan masarufi tana tararwa a kitchen ko store, ba ta taba gwada yin abinci da shi ba, shi ma kuma bai taba nema ba.
Wannan rayuwar fa ta yi mugun sanya Binta a uquba, ita da taso gidan mutane gidan shige da fice, an kawo ta wani mugun kurkuku an garqame, duk yawan danginta sai daidai ke zuwa, su ma sai wadanda zancen korar da Mujahid yayi wa Yaks ne bai je kunnensu ba. Ga ta ita ba ta da qawaye bare su dinga ziyartata suna dauke mata kewa, qawarta qanwarta kuma aminiyarta daya, wato Nabila, Mujahid ya sanya wuqar son kai da zalincin da su maza suka gada ya datse tsakaninsu, rabonta da Nabila tun ranar da aka kawo ta, sai sau daya da ta kira ta a waya.
Idan akwai abinda ya fi kurkuku, Binta ta radawa wannan rayuwar ta gidan Mujahid, kullum sai ya sha Allah ya isa ta fi cikin kwando tare da nuna Allah ita fa an zalince ta, an aura mata mutumin da bai san haqqin mace ba bai san komai ba sai zalinci.
Da tafiyar ta fara yawa sai ga ta fara rama ta fara kuka, alhalin da ta ci alwashin daga inda ta sa qafa ta shiga gidan Mujahid zata ajiye kuka a waje, sai dai shi ta bashi, to yanzu ta rakito abinta ta yafa, tunda shi ina ma ta gan shi bare ta ba shi kukan?
Satin farko dai na auren nasu ta fahimci ya kwashe shi yana wuni a kangon dakinsa babu abinda yake fitar da shi sai salloli, amma sati na biyu na shiga ta fahimci ya koma kan aikinsa, ya kan dawo gida da rana kamar yadda ya saba da, sannan ya kuma ficewa sai kuma yamma. Yanzun ma haka yake, in ya dawo iyakacinsa da ita sallama in ya tarar da ita a tsakar gida, inda zata amsa a ciki shi kuma ya kama qafar benensa ya haye, ba ta qara jin motsinsa sai tasa ta sauko shi.
Wa zata nuna wa wannan uqubar da take ciki ya kawo mata dauki? Wa zata fadawa ko da jaje ya taya ta? Kullum kukanta kenan har aka haure wata daya da bikin. Rannan dai da ta ga babu sarki sai Allah sai ta kira aminiyarta Nabila a waya,
“Wai Nabila laifin me na yi miki da kika share ni a rayuwa? Yanzu Nabila ko kowa ya guje ni ke yakamata ki guje ni?”
Nabila na dariya ta ce,
“Kai Anti abin har yayi zafi haka? Ni dai na san ana saurarawa amare su shaqata zuwa wani lokaci, wannan ne kawai dalilin kar ki dada kar ki rage, kuma ma dai cikin satin nan nake son zuwa musamman da neman shawarata kan maganar nan ne dai, Inna ta matsa…”
Binta ta boye tsakin da ya bijiro mata bisa dalilin kiranta amarya da Nabila ta yi, da saurin murya ta ce,
“Ba wani batun cikin sati Nabila, kawai gobe ki zo, yaya zaku kawo ni wani kurkuku ku juya baya babu mai zuwa ya ce bari dai ya je ya gano wannan fursunan.”
Dariya kawai Nabila ta yi don ta san kwanan zancen, Mujahid yayi mata jirwaye da kamar wanka a wata wayar da suka yi.
Binta ta ce,
“Ina Hajiya?”
Nabila ta amsa,
“Inna na nan lafiya, duk da dai ta dan sha ciwo, ba ki zo dubiya ba sai Yaya Mujahid ne ya zo”
Binta ta ji wani takaici da tsanar Mujahid ta qara naushinta, ta yi qoqarin ta hadiye kuma ta kasa,
“To mugun ba sai ya fada min ba? Kodayake ai laifinki ne, har ya fi ni matsayi a wajenki ne da zaki fada masa ni na kasa sani?”
Nabila ta ji ciwon zagin tamkar wani ubanta aka zaga, amma babu yadda ta iya, fadan da ya fi qarfinka dole ne ka mayar da shi wasa, tana dariyar yaqe ta amsa,
“Wallahi shi ma ba ni na fada masa ba, a can gidanku ya ji, su Hajiya ai da su aka yi ta sintirin asibiti…”
Binta ta ce,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ciwon me zafi ne haka?”
Nabila ta amsa,
“Ciwon suganta ne dai, kin san ta da karya doka”.
Binta ta amsa,
“Ayya! Yakamata na zo na duba ta, ki gaishe ta don Allah.”
Binta ta yi maganar ne cikin rashin yarda da kai, don ba ta san ta yadda zata kwashi fitar ba, in dai ana maganar dole sai ta tambayi wancan Sarkin gabar.
Tana jiyo Nabila cikin dariya tana ce mata,
“Kar ki damu, tana nan tana ta sa miki albarka kin yi zamanki a dakinki ba ki yi ta barbadaddun yaran yanzu masu fita tun kafin su rutsa sati da aure ba.”
Binta ta dan yi nishi kawai, cikin ranta tana fadin,
“Ai barar Dankali ma samun dama ne, kuma duk wanda ya sami rana shanya zai yi.”
Amma a fili sai ta cewa Nabila,
“Ki ce kenan in kika yi aure sai kin shekara ba ki fita ba, don na san sai ta zuge mijin.”
Nabila na dariya,
“To ga ni nan dai, ni in an yi maganar auren ma wallahi gabana faduwa yake, Inna na son matsa min na zabi mijin da zan mutu ina nadama, ni bana son kowa yanzu wallahi, ba qaramin taimakon rai ba ne a bar zuciyata ta huta kuma ta yi addu’a.”
Binta ta ji tausayin Nabila ya soke ta, ko da yake tausayin kanta ma ya fado mata zuciya, cikin raunin murya ta ce,
“Gaskiyarki, don wallahi da wani auren gara a kai ni tsakiyar bahar maliya a gina min gida a can a ajiye a dawo gida.”
Nabila mai hankali tana bude baki sai ta amsa mata da cewa,
“Ni ba haka nake nufi ba Anti, ni in dai an riga an aura min miji, ko shi ne ba ya sona ba wai ni ce ba na sonsa ba, gaskiya zan yi qoqari na bi shi, don aure ba wasa ba ne, bautar Allah ne da zaka sami sakamako daidai abinda ka aikata.”
Binta ta so ta share saboda jin haushi, amma ta gaza sai da ta ce,
“Ayya! Da ma ke ce Ko wanne Gauta mana, sunan wani shirin siyasa da na taba ji a gidan wani radiyo a kano, na ga har kin fi shirin iya siyasa”
Sai kawai Nabila ta yi dariya, ta ce,
“Wallahi tallahi ina fada miki iyakar gaskiyata ne Anti, ba gashi nan ina shirin in zabi wanda ba na so in aura ba, bisa farin cikin Innata ba farin cikin kaina ba, ba na sonsa ko kadan amma ki zuba ido ki gani ba zan kasa yi masa biyayya ba…”
A fusace Binta ta tare ta,
“In kin aure shi don Allah ki dinga zama yana yankar naman jikinki, ni kin ga zaki zo goben ko ba zaki zo ba, in kuma Mujahid ya shiga tsakaninmu kawai ki fito fili ki fada min.”
Nabila ta kame baki,
“Zan zo Anti, zan zo dan ki janye zargin da kika yi min.”
Binta na qoqarin sauke waya ta ce,
“To ina zuba idon ganinki, qarfe tara na safiya”
Tana jiyo Nabila na dariya da ihun qin lamintar doka wannan sammakon.
Binta ta sauke waya tana dariya, haka kawai Allah ya jarrabe ta da son Nabila, wannan ne dalilin da ke qara mata tsanar Mujahid don yana qoqarin gindaya hijabi tsakaninta da ita.
Ta lula cikin tunani da son warware matsalolinta, babbar cikinsu ita ce son rabuwa da Mujahid, qananan ciki kuma shi ne hanyoyin da zata bi su rabun, da kuma yadda zata kubuta daga wannan tsinanne kadaicin na gidansa me cin rai, haba kadaici sai ka ce na azabar lahira, kana zaune da mutumin da bai san komai ba sai gaba, bayan kai ba sonsa kake ba, kuma ya qi bata damar hanyoyin da zata nemi saki saboda tsabar zalinci, in dai ba so yake kawai ta fito ta ci kwalarsa ta nemi sakin shi kuma ya ji dadin laqaba mata hauka ba.
Nan da nan Yaks ya fado mata a rai, sai ga shi ta kira wayarsa,
“Wai kai ya maganar aikina ne?”
Da azama ya ce,
“Wallahi Binta an samu, na yi ta kiranki yanzun nan na sami wayarki Busy, sun kira ki Interbiew gobe-gobe…”
Binta ta ji wani matsanancin farin ciki ya fado mata zuciya, ta dinga tsalle tana shewa, Yaks na ta yi mata dariya, ta ce,
“Wanne Bankin?”
Ya amsa mata,
“Wanda dai kika so.”
Ta sake shewa,
“Allah na gode maka, zaman kadaici ya qare min, gobe kawai sai ka shigo ka kai ni…”
Ya tare ta cikin razana,
“Ki rufa min asiri don Allah Binta, Yaya Mujahid fa ina shakkar in kansa daya, duk da kin ce kin warware masa cewa shiri ne muka yi, har yau fa q0
Qbai dena gaba da ni ba”
Ta zagi Mujahid cikin zuciyarta amma a fili sai ta ce,
“Kai ka cika tsoro wallahi, to an ji na kawo kaina.”
“Yauwa da dai ya fi.”
Suka yi sallama suka ajiye waya.
Binta ta zauna musamman ta fara lissafin ta fuskar ma da zata tari mujahid ta yi masa zancen, sam ba ta zaci haka da wannan muguwar gabar zaman gidansa zai zo ba, da tun farko ta bijirewa tariyar sai ta fara aikin, in ya so babu abinda zata nema a wajensa, duk inda ta so zuwa zata iya zarcewa daga wajen aikinta ba tare da ta matsawa kanta tambayar wani qato ba.
Bisa wannan dogon lissafin da gwajin tambayar har kuka ta yiwa kanta, ta kuma qara jin tsanar wannan tsinannen auren wanda ba shi da ribar komai sai asarar koya mata gaba da dan uwanta musulmi.
Tana cikin atisayen yadda zata yi magana da Mujahid qarfe biyun rana ta buga, sai ta yi daidai da tsayawar Motarsa a qofar gida.
Cikin dakan zuciya ta yi zarya ta taho bakin qofar falonta ta tsaya tana dakon ya shigo tsakar gida ta datse shi a nan. Komai na jikinta bari yake, sai ka ce mazinacin da yake tsaye jiran sakamakon gwajin cutar HIV