Binta dai ta ji zuciyarta na faman cin wuta amma ba ta san sila ba, ta rasa abinda zata rarumo ya kashe mata wutar,sai kawai ta sami kanta cikin hawaye da duban Mujahid,
“Haqqinka ne, Nabila ce take da haqqin ka dinga bin safiya kana gaishe ta kana jin lafiyarta, mai haqqin kuma an sheqar da shi ya bi titi ko?”
Ya ji zuciyarsa na taka rawar burgewa ita kadai, Kishi! Binta ke kishinsa? Da kishin gaske ne da yayi abinda ya fi rawa amma ya san kishin cutar da shi ne kawai, so take kar ya rabi kowa ya ji sanyi.
Wannan ya sa ya kalleta kawai sannan ya kawar da kai ya share bai tanka mata ba.
Daidai lokacin suka iso Bankin, yana qoqarin neman wajen ajiye Motar yana sauraronta tana gasa masa magana,
“Ni dama ba zama na zo yi gidanka ba wallahi, kana iya sallamata ka auro Nabila… ka ba ni takardata kawai.”
Tana rufe baki ya amsa mata cikin bata fuska,
“Au wai da fatar baki zaki nemi sakin ne? ai na zaci zaki neme shi da aiki ne kamar yadda kika tsara, ga matakin farko nan kin aza.”
Yana nuna mata Bankin, bai jira cewarta ba ya dora,
“Kin zabi fita aikin da zaki dinga barin gidan aure dan na taba fada miki ba na son matata ta yi aiki? To ai kawai ki cigaba da gwadawa, ni ba ke zaki dinga zaba min abinda zan yi ba, sonki daban rayuwata daban kin ji.”
Cikin mugun takaici ta dinga goge hawaye, shi kuma ya ya cilla kai can gefe nuna basarwa da nuna shi fa ko a jikinsa. Ta dinga satar kallonsa tana ganinsa a wani danta’adda mai quntatawa mutane ya sanya su a bala’I ba tare da ya ji komai a ransa ba, ya ce shi masoyi ne amma bai san komai na kyautatawa wanda ake son ba.
Ta gaji da ciwon rai ta goge hawayenta ta kama murfin mota tana qoqarin fita ba tare da ta ce masa komai ba.
A cunkushe cikin gadara ta ji yana ce mata,
“Wani lokacin in kin yi abu don ki quntata min, sam ba kya lura da cewa kanki kike cutarwa, dubi dai yanzu, kin wani qinqimo cingam kin manna a baki kina ta faman cakwal-cakwal kuma wai zaki shiga cikin mutane da sigar matar aure, don Allah in kin bar wajen ni za’a zaga ko ke?”
Da takaici ya qara shan kan Binta kawai sai ta qara saurin taunar Cingam dinta ba tare da ta saurare shi ba.
Ya dan daga murya,
“In kin gama sai ki kira ni na mayar da ke inda na dauko ki, in kuma ba ki da lambata kina iya karba, don na san wanda ba ka qauna goge lambarsa kake, ni ma da nake qaunarki da babu abinda zan yi da lambarki tuni na goge ta.”
Nan ma dai babu amsa, har ma ta fara tafiya abinta.
Ya bi ta da kallo cikin dariya ba tare da ta sani ba, sannan ya daki sitiyari ya ja motarsa yana cewa,
“Ki yi haukanki ki gama, kuma muna tare.”
Ya dinga tsammanin kiranta tun bayan mintuna talatin da kai ta, amma shiru kake ji har lokacin zuwansa gida cin abinci rana yayi. Yana son zuwa ya dubo ta a can Bankin amma yana tsoron bayar da kai, don haka ya cigaba da cijewa.
Ya dawo gida da dokin ya ga ko ta dawo amma sai ya tarar da gidan a rufe yadda ya bar shi, don haka duk gwiwarsa ta yi sanyi, haka ya shiga sukuku yana harkokinsa yana tunaninta. Duk yadda ya raya zai cirewa kansa damuwa da wannan ta’addacin da ta kinkimo masa na zuwa aiki da wuni cikin qarti, yau daya sai ya ji zuciyarsa na neman ta fashe don ma yana yayyabe ta da ambaton ubangiji ne, yana tsammanin da qila fashewar zata yi.
Can sama-sama ya dinga jiyo qararrawar gidan na amo, qirjinsa na bugawa da zaton Binta ce ta dawo ko a motar haya ko kuma ta kira dan iska Yaks ya dauko ta, ya tsaya ya dinga hadiye kala-kalar fishinsa sannan ya bude qofar, kawai sai yayi arba da Nabila tana tsaye cike da dokin ta ga Anti Binta, ya hango hakan a idonta da kuma yadda ta yi turus da ta ganshi.
Yayi murmushi ya juya cikin gida yana cewa,
“Za ki zo amma dazu da muka yi waya ba ki fada min ba?”
Ta bi bayansa jikinta a sanyaye tana cewa,
“Ni da zan zo wajen Antina Yaya Mujahid, ba fa wajenka zan zo ba.”
Yayi dariya,
“Madalla, sai ki shigo ai.”
Suna shiga cikin gidan ta yi turus da ta ga qofofi a kulle, ta ga kuma Mujahid ya bude Kitchen ya dauko mata doguwar stool ya ajiye mata a nan.
“Ki zauna.”
Ta yi Saroro tana bin gidan da kallo,
“Ina Antin?”
Yayi dariya yana dosar Bene,
‘Anti ta je unguwa, kin ga dayake ba ta da kirki ta san cewa zaki zo amma ba ta kira ki ta sanar da ke cewa yau tana da fita ba, abinda ba zan taba iya yi miki kenan ba.”
Tana dariyar qarfin hali ta ce,
“Ka ji Yaya Mujahid, ni ko me zaka ce ma ba ta yi min laifi ba.”
“Ai nima ba cewa na yi ta yi ba.”
Don dai kawai Mujahid ya wuce ya bar ta ne, da gaskiyar magana ba ma zata zauna ba, duk da a tsakar gida ne sai da ta ji tamkar akan qaya ta ke. Ko babu zargin komai a tsakaninta da Mujahid, sam ba zata sake ta zo gidan babu matar gidan ba, bare sun riga sun shata layin da ba zasu iya goge wa kansu ba.
Can jimawa ya leqo, kafin yayi magana ta dan daga murya ta riga shi,
‘Yaya mujahid zan koma.”
Ya ce,
“Wai da ruwa zan kawo miki ki sha, sai mu je mu dauko ta, can Bankin da take neman aiki ta je tantancewa.”
Nabila ta dan ji sanyi a ranta, amma dai kadan. Ba ta son bin Mujahid dauko Binta, ga shi kuma ta sallami direban gidansu, a sanyaye ta ce,
“Ba sai na sha ruwa ba Yaya mujahid.”
Ya ce,
ya bude mata qofar mota yana cewa,
“Ko wanne kika zaba dai ai motar tawa zaki shigo mu tafi, in ba zaki bini mu dauko Binta ba ni zan kai ki gida, in na je dauko ta kuma zan fada mata yadda muka yi da ke.”
“To muje kawai.”
Ta fada jikinta a sanyaye.
Sai ta bashi tausayi ya dinga satar kallonta lokaci lokaci har suka je. Ita dai Allah ya yi ta mai matuqar sauqin kai, duk wani abu mai damun rai ko mai yakushin abokin mu’amalarta ba ta tare da shi. Wadannan gwala-gwalan halayen nata suna da tasiri wajen bata girma a duniyarsa, yake mata fatan samun abokin zama wanda ya san darajar halayen ba irinsa mai girmama so fiye da kyawun hali ba.
“Ina Yaks?”
Ya jefo mata wannan tambayar katsahan lokacin da ya ga Yaks ya gifta a guje cikin motarsa, yana ta faman hada hanya da Mota, matan da ya dauko da gani ka san ba kintsattsu ba ne.
Ita Nabila ba ta gan su ba har sun wuce, wannan dalilin ne ya sa ta amsa masa da iyakar gaskiyarta,
“Yana nan har yanzu muna tare, kuma da alama dole shi zan aura, don shi kadai na san halinsa a wadanda ke son aurena, Abdul da Nasiru dukkansu rayuwar waje suke yi har yanzu, in za’a sami qazanta tare da su ina tsammanin zasu fi yaks.”
Ya juyo ya dube ta cikin tausayawa, ya qara gudun motarsa ba tare da ya tanka mata ba, har ya riski Yaks a danja, ya tsaya gefensa na hagu, don da alama Yaks dama zai yi, yayin da shi kuma zai miqe, Mujahid ya nuna wa Nabila yaks, aka yi katari daidai lokacin yaks na tafawa da Budurwar da ke gefensa.
Nabila ta kawar da kai da sauri lokacin da kanta ta ji yayi wani irin nauyi, zuciyarta na runtsewa da jin sassaucin zata iya maneji da Yaks. Danja ta basu hannu duk suka wuce ba tare da wani a cikinsu ya sake tankawa ba, Buqatar Mujahid dai ta biya, ko banza ya san wannan dalilin zai iya raba Nabila da yaks, Yayin da Nabila ta yi shiru cikin zuciyarta tana ta saqa dalilin da zasu wanke mata yaks a ganin da ta yi masa yau, ta dinga kwatanta yarinyar da ya tafa da ita a matsayin wata Qanwarsa, sai ta dinga jin sanyi da kintace, don yanzu ita fa ba ta da mafita.
Yana neman wajen tsayar da motar ya ga Binta ta doso shi, yadda ya hango ta fuskar nan kamar ta shanu sai da ya ji wani kadawar ciki, yayi kasa da murya ba tare da ya dubi Nabila ba ya ce,
“Ga Antin naki nan fa ta qaraso”
Nabila na waiwayawa sai ta hango Binta, cikin sauri ta balle murfin motar ta fito.
Sai da Binta ta kusa kifawa don razana da ta yi da ganin Nabila ta fito daga motar Mujahid, qirjinta yayi wani irin qunci nan da nan ta ji tana neman amaye kayan cikinta.
Yaqe kawai ta sakarwa Nabila suka rungume juna.
Cikin shagwaba Nabila ta ce,
“Anti shi ne kika shanya ni, alhalin kin ce na dako sammako”
Binta ta dinga tattare wasu tarkace da ba ta san sunansu ba daga maqogwaronta ta ja hannun Nabila suka doshi motar Mujahid tana cewa,
“Sorry My dear, wallahi tallahi na manta ne”
Nabila ta bude mata qofar mota kusa da Mujahid, sannan ta zagaya ta shiga baya tana cewa,
“Na yi miki wannan shaidar Anti, na san in dai kina sane ba za ki taba yi min abinda zan ji babu dadi ba.”
Nabila ba ta kula da Mujahid ba sai Binta, da Nabila ta gama magana tabe baki yayi a hankali ya ce,
“Kayya!”
Binta ta qara rasa qarfin gwiwa, da ta yi qoqarin ta yi magana sai ta kasa.
Sai da Mujahid ya hau titi sosai sannan a qasaice ya ce mata,
“Malama ina fatan komai ya tafi yadda yakamata.”
Ta dinga kokawa da fishi kafin ta dan ci kariminsa ta ce,
“Alhamdulillahi, akwai alamun nasara. Tun sha biyu na gama amma ina shafa lambar taka sai na tarar kuwa ashe na goge ta, dole na zauna dakonka kawai.”
Ya san dan ta tura masa haushi ta fadi haka, don haka tana rufe baki ya rama,
“Allah kuma ya taimake ki ba zaki kwana a wajen ba, Nabila ta zo ta ji gundurar zama ba kya nan na ce ta zo na kawo ta wajenki.”
Ta yi qasa da murya yadda Nabila ba zata jiyo ta ba,
“Ayya ta kwafsa min, kwana a nan ai Aljannar duniya ne akan kwana a wancan kurkukun mai kama da gwantanamu”
Shi bai rage muryar ba ya amsa,
“Dadin abin babu wanda aka kafe da qusa a cikinsa.”
Dole Binta ta yi shiru saboda jin numfashinta ya fara shaqewa. Wannan azzalumin mutumin sonsa na gaibu ne, bai qi ya kashe ta ya huta ba.
Kawai sai ta mayar da hankalinta ga Nabila tana ta jan ta da hira, kuma cikin hirar take samu ta jefa masa baqar magana.
Hakan ya sanya Nabila mugun muzanta, ba ta san cewa gidan nasu har yanzu girgidi yake ba, da babu dalilin da zai sanya ta shiga tsakiyarsu Binta na cin fuskarsa haka.
Shirun da yayi sai ya dinga bata tausayi ta ga kamar kawai Binta ta qunshe shi a gida ne tana ta faman cutarsa.
Bai sake tanka musu ba har ya kai su qofar gida, kamar a kan qaya suke dukkansu suka yi waje, amma sai ya sa baki ya kira Nabila.
Qafarta na hardewa ta koma wajensa ta tsaya, muryarta na rawa ta ce,
“Ga ni Yaya Mujahid”.
Ya ce,
“Qarfe nawa zaki tafi na zo na mayar da ke? Ko ki jira ni kawai in na taso daga aiki zan mayar da ke”.
Nabila ta yi qoqarin ta yi magana da qyar,
“Direba zai dawo ya mayar da ni.”
Ya tashi motar,
“Ki yi masa waya ki dakatar da shi, akwai maganar da nake son yi da ke a hanya.”
Girgiza masa kai kawai ta ke amma ya qi saurararta, yana daga mata hannu ya ja mota ya tafi.