Skip to content
Part 59 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Ya juyo ya kalle ta ya kawar da kai, yana sane ya fada mata gaskiyar zuciyarsa, don ya fahimci lallai ta nade hannun zani za ta shigo rayuwarsa, to kafin ta shigo din dole ya tunatar da ita akwai fa wata da yake wa kwatankwancin son da yake mata.

“Ka fito fili ka fada min kawai ka daina sona, ba sai ka tsaya kana ta faman turance ni ba”

Ya nuna halin ko in kula,

“A haba dai, Binta ko bata min rai kika yi ai in na tashi hucewa cewa nake miki ina sonki, da zan iya daina sonki ai da tuni na daina, kuma so sai ya hana mutum fadar gaskiya? ko ba ki shata min layin mayar da ke Anti ba muna matsayinmu na masoya zan iya fada miki abinda na fada yanzu, ai ba na fasa fada wa Nabila ina sonki, ta san wannan kamar yadda ta san ina son ta”

Ta dan ji sanyi da maganganunsa, musamman da ta tuno da wani hange na masana halayyar dan adam, da suka ce, Namiji yana da wasu akwatuna a zuciyarsa na adana son mata barkatai, yayin da mace yawanci nata akwatin daya ne, namiji zai iya son mace sama da daya a lokaci guda, amma mace sai ta rasa wani son take iya karbar wani.

“Nabila na da ciki ne?”

Ta ji harshenta ya huce akan wannan tambayar.

Shi kuma ya amsa kai tsaye,

“Watansa uku, kin san ta da kara wai kunyar sanar da ke ta ke.”

Ta jima tana tattara kanta kafin ta kammala, Nabila na da ciki? Ta riga Nabila shiga zuciyar Mujahid amma komai ma tana riga ta? Tana so ta ji raunin zuciya amma sai ta dake, ta shiga bayyana murna a fili tana yi musu fatan alkhairi. 

Shi dai kallonta kawai yake don yana ganin kamar hannun agogonsa na neman komawa baya, tana son ba shi so kuma tana neman hanawa.

Can bisa rashin zato ya ji cikin rawar murya ta ce masa,

“Ina roqon wata alfarma.”

Ya juyo ya dube ta.

Bata yi qasa a gwiwa ba ta amsa,

“Mu koma gida yanzu, in yaso ka ba ni wata daya sai ka dawo ka gode wa Alhaji bisa aurena da na Nabila, na san yau zaka je masa ne bisa nata kadai”

Ya ji wasu kibiyoyin farin ciki na zagaye kansa a guje, sai dai yayi jarumtar boye su shi da zuciyarsa, yayi fuska bai tanka ba sai da ya je mazagaya sannan ta ga yayi kwana ya kama hanyar gida, da ba ta yi tsammanin zai yi mata alfarmar ba, har ta fara fargabar inda zata shiga ta yi rayuwa tunda komai a tare da Mujahid ma tana rasawa.

*****

Har kusan shadaya Nabila ba ta ga zuwan Mujahid gare ta don duba lafiyarta ba, ya dai kira ta har sau biyu a waya, daya da asuba daya kuma bayan ya dawo masallaci ya binciki lafiyarta, inda ta tabbatar masa yau ba ta tare da zazzabi kuma ba ta tare da jin amai, hasalima bacci ta ke ji yanzu.

Ya sha murmanrsa sannan ya bata rarrashin ta koma baccinta.

Da ta farka sai ta farka cikin kadaici, don yawancin lokuta ta kan farka ta tarar da shi kusa da ita yana ta faman kallon fuskarta yana murmushi, idan kuma ba zai iya jiranta ba, ya kan zo ya dinga diga mata ruwa a fuska, ya ce babu abinda ya fi yi masa qaye a tare da ita irin lallausa fatarta da ko kadan ruwa ba ya iya zama akanta, musamman ma fuskarta da ta fi ko ina santsi da qyalli, yau ta ji wani irin kadaici ya ishe ta da ba ta tarar da shi, da ta bi dakin da kallo kuma sai ta lura bai shigo cikin sa ba, ta ji ba dadi amma sai ta ji tana farin ciki idan aka ce ya sabunta zama lafiya da Binta ne.

Da sauri ta yi wanka ta shirya ta sauka qasa, a falon Binta ta tarar da Mujahid gaban teburin abinci yana kurbar tea cikin yanayin farin ciki, babu Binta a falon, tana shiga ya miqe tsaye domin girmamawa, yana yawan yi mata haka, tun tana jin kunya har ya zame mata jiki, don ya sha jaddada mata zai iya duk wani abu da zai sa ta ji a qoqolin ranta cewa yana sonta kuma yana girmama lamarinta.

Idanuwansu na kan juna har ta qarasa gareshi,

“Yaya Mujahid ka tashi lafiya?”

Bakinsa na rawa yana amsawa kuma lokaci guda ya ja mata kujera ta zauna,

“Lafiya na tashi Nabila, ki gafarce ni yanzu nake son kammala karyawa na je na ga lafiyarki.”

Ta kada kafada,

“Kar ka damu, duk ranar da baka sami sarari ba ni zan zo na ga lafiyarku. Ina Anti Binta?”

Ya nuna mata qofar dakin bacci, 

“Ban san me ta ke yi ba tun dazu ta bar ni ni kadai”.

Kallonsa kawai Nabila ta ke, komai nasa ya canja, sai wani qayataccen annuri ne ke tashi daga fuskarsa.

Ya hura mata iska a idonta daga inda yake, zai yi magana ta riga shi,

“Na ji dadi yau ina ganinka cikin farin ciki fiye da ko yaushe”.

Ya kada kai cikin qarin jin dadi,

“Ko? Ai kin san kullum in na kwanta farkawa nake da qarin soyayyarki, dole fuskata da yanayina zasu dinga nuna canjin da suke samu na cigaba…”.

Lokacin Binta na tsaye gaban gado da mamakin ganin kayan lefenta a kan gado, wanda tuni Mujahid ya kwashe, ashe ba siyarwar yayi ba wani wajen ya sakaya su? Ita kadai ta dinga dariya, shi komai nasa daban ne, yadda yake neman so daban haka ma yadda yake sarrafa shi idan ya samu.

Ta na jiyo su tun farkon shigowar Nabila, bakam ta yi tana daukar darasi, wato Mujahid dan taratsin soyayya ne, in yana darasi shiru take masa ashe abin na mai da martani ne? Nabila ta iya ita tana zaune?

Ta miqe da sauri ta doshi falo kar su fasa mata zuciya, don ta jiyo Nabila ta kashe murya tana ce masa,

“To ni me yasa tawa fuskar ba ta nuna wa? Don Allah ba ka gani a idona kullum da sababbi son ka nake tashi?”

Yana cikin shauqi ya amsa mata,

“Ina gani mana, ko kadan ma ba kya ragewa Babyna don ta zo ta samu, cinye du kike zama…”

Nabila ba ta kai ga amsa masa ba Binta ta fito, duk suka kintsa kansu ba tare da cire walwalar fuskarsu ba, sai dai maimakon juna Binta suke fuskanta, Nabila har da miqewa tsaye,

“Anti Binta barka da fitowa.”

Binta ta daure ita ma ta basar tana nuna murna,

“Barka Nabila ai yanzu nake shirin hawa sama da qorafina.”

Nabila ta dan yi tunani, sai ta tuna jiya Mujahid ya fada wa Binta tana da ciki, da sauri ta maze ta cewa Binta,

“Ayya Anti, ki manta kawai.”

Dariya Binta ta yi, tana jin raguwar zafin qirji saboda Mujahid ya sa ma ta ido, qwayar idonsa na tura mata saqonni dubunnan soyayyarsa.

Har lokacin da Nabila ta fara bayani ya mai da ganinsa kanta, itama da gani kallon da yake mata daga fadar so ya tono shi,

“Komai tare da ke muhimmi ne Anti, yi miki irin wannan albishir din ma muhimmi ne, kyakkyawan lokaci irin wannan nake jira don na ba ki albishir din, yau na ga daga ke har Yaya Mujahid fuskokin ku kyalli suke, ina son irin wannan lokacin.”

Binta ta tsare Mujahid da ido,

‘Me ka fada mata?”

Yana murmushi ya dauke ido daga kan Nabila ya mayar kanta,

“Na jaddada mata ina sonki, kuma ta taya ni murnar kin yarda zaki rayu da ni, faqat! Abinda na ce kenan ko Nabila?”

Ya sake maida ganinsa ga Nabila.

Duk da yanzu ta ji zancen da farin cikinta ta goyawa masoyinta baya, ta daga hannu tana dariya ta ce,

“Shikenan fa Anti, kar ki dada kar ki rage, kuma hakan ya isa ya wadatar gidanmu zai yi albarka zagaye da so da Amana, ina sonku duka, ban taba ganin wasu mutanen kirki kamar ku ba.”

Binta ta ji hawaye na cika mata ido tana hadiye shi, Mujahid kuma na cika da farin cikin in an rantse a Nabila ba a shan kunya, sonta na qara samun muhalli a zuciyarsa, alfaharin zamowarta iyalinsa kuma na sa shi jin qasaita,

Can ya jiyo muryar Binta na magana cikin raunin murya da kada kai,

“Na yarda da kai Yaya Mujahid, Nabila ta cancanci irin soyayyar da kake mata, zan sake baka goyon bayan sonta, zan kuma taya ka kyautata mata…”

Nabila na nuna alamun jayayya Mujahid na amsawa Binta,

“Kamar yadda ta ba ni goyon baya a taki soyayyar kuma ta taimake ni na samu, kai wa ya kai ni sa’a? na yi murna da na aboci mutanen da ke daraja muradan abokan zamansu.

daya bayan daya suka dinga duban juna, sai kuma suka fashe da dariya.

KARSHE

<< Rigar Siliki 58

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×