Rufa-Ido
Na ce ki tsaya gare ni komai rana,
Kin ce ai ga dare maraice kura.
In ya zo sai ki ɓuya bayan haske,
Wai za mu haɗe cikin mafarkai ƙarara.
In bayi sun shiru jiki ya kwanta,
Ni talatainin dare nake wa hira.
Na ce ki tsaya gare ni komai rana,
Kin ce ai ga dare maraice kura.
In ya zo sai ki ɓuya bayan haske,
Wai za mu haɗe cikin mafarkai ƙarara.
In bayi sun shiru jiki ya kwanta,
Ni talatainin dare nake wa hira.