Shiga kawai ya yi ya tsaya, likitocin suka dubeshi. Wani Nurse ya dakatar da shi.
“Sorry Sir, ana kan aiki.”
Sanin dokar asibiti ne ya sanyashi fita ya tsaya a kofar dakin. Mintunan da basu fi ashirin ba, likitocin suka fito, ɗaya ya dubesu.
“Yauwa, ku kwantar da hankalinku. Ba wani rauni ya samu mai yawa ba. Mun bincika kwakwalwarsa ba ta ta6u ba. Alhamdulillah. Sai ƙafarsa da ya ɗan samu buguwa amman ba karaya bace. Yanzun dai ya farfaɗo kuna iya shiga ku ganshi.” Godiya Adam ya yi musu sannan ya bar wurin ya nufi ciki.
Idanun Fu’ad akan ƙofa, kansa daure da bandage. Fuskarsa ta yi wani ja ga tabon raunuka a gefen kuncinsa.
Idanunsa akan na Adam, kallon rashin sani yake mishi don har ga Allah bai gane wane ba.
Adam dubansa yake ba yabo ba fallasa. Yana kara tuna shi din jinin Salma ne.Ya karasa gareshi bayan ya tankwari zuciyarsa dakyar. Ya daure ya ce
“Ya jikin?”
Fu’ad ya gyada kai.
“Da sauki.” Ya yi daidai da shigowar ɗan sandan. Shima suka gaisa, ya yi mishi bayanin Adam matsayin mutumin da suka yi karo ya kawo shi asibiti. Fu’ad ya kara kallonsa da ɗan murmushi.
“Thank you.”
“You are welcome.” Ya fadi a gaggauce. Ya dubi agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Wannan sararsa ce, muddin ba ya son magana ko yana son barin wuri to zai shiga kallon agogo.
Ya sa hannu ya fiddo wayarsa.
“Ga wayarka, Mum ɗinka ta kira na sanarmata kana asibiti. Allah Ya kara lafiya.”
Daga nan ya sa kai ya fita tare da ɗan sandan. Sukai maganar motar Fu’ad ne, ɗan sandan ya koma ya sanar da Fu’ad batun motarsa a karshe ya fito Adam ya sallameshi. Adam bai bar asibitin ba sai da ya kara zuwa ya yi clearing dukkan wasu payments a karshe ya ba likitan lambarsa koda ace akwai abinda ake buƙata toh ya yi kiransa ta waya.
Yana shiga motarsa ya zauna yana kallon ta inda za ta ɓullo, haka kawai ya kasa barin asibitin, sai da ya tabbatar da shigowarsu tare da mijinta sannan ya ja motarsa a miliyan ya bar wurin. Ya san za’a rina, akan Fu’ad ta sha marinsa. Ta sha dukansa da aibatashi. Ba ta tsayawa anan sai ta haɗa da Ummansa. Mahaifinnasa ma ba kyaleshi yake ba, duk da cewar yana ganin irin yanda yaron ya raina uban, hakan kamar ba ya damunsa, sai ma kokarin saɓawa wanda duk ya taɓa yaron koda ba da gangan ba. Hannu yasa a aljihu da nufin ciro wayarsa ya ta6a cingam. A hankali ya dubi cingam din yana tuna diramarsa da ita sai ya yi murmushi. Fiddoshi ya yi daga ledarshi ya sanya a baka ya shiga tauna. Lumshe ido yake ba don cingam din ya kai dadin rabin wanda ya saba ci ba. Sai domin kawai ya fito daga hannun da ba zai iya wancakalarwa ba. Ina dalili? Bai sani ba.
Umma na tare da sauran iyayensa a tsakar gida suna aikace-aikacen biki kasancewar gobe ne daurin aure. Lokacin karfe takwas da wani abu na dare. Kallo daya za ka yiwa Umman ka san tana cikin wani irin farin ciki. Ba ta tattare da ko ɗigon damuwa. Yan uwanta sai nan nan suke da ita, kowa tausayinta yake ji. Wannan ya fiyemata komai.
Zuwan Adam ne ya tasheta suka shiga falon Gwaggo Kubra. Dubansa ta yi tana murmushi.
“Ya akai? Naga ka jima ba ka dawo ba.”
Nan ya labarta mata abinda ya faru ta yi ta salati. Ta kara da fadin
“Ya jikin nasa yanzu?”
Da mamakin yanda ta damu har haka ya ɗan taɓe baki.
“Da sauki, ba wani ciwon a zo a gani ya ji ba. Gudun ganganci yake.”
“Allah Ya ba shi lafiya to, Ya kiyaye tsautsayi.”
“Amman me ya kawosu nan?”
Fadin Adam da mamaki.
Umma ta yi murmushi.
“Mata da mijinta ai duk inda yace ta je, dolenta.”
“Ina twins?” Ya faɗi da don bagarar da zancen.
“Suna wurin babansu Yaya Hashim. Suna can gidansa. Ai yace yaransa ne na fidda rai.”
Murmushi mai kayatarwa Adam ya yi. Nan da nan ya tuno labarin Humaira. Ai kuwa ya ba Umman, me za ta yi ba dariya ba.
“Oh, to ko dai da ita za’ayi?”
Yana murmushin ya amsa.
“Yarinya ce fa, don bana jin za ta fi Amira. Idan ma ta fi to ba wani da yawa ba.”
Murmushin manya Umma tayi kawai.
“Allah dai Ya zaɓamaka ta gari.”
Ya amsa da Amin. Daga nan ya yi mata sallama ya fice zuwa masaukinsa.
*****
Kuka take yi tana shafar kan ɗan nata. Ya sa hannu a hankali ya sauke nata hannun.
“Please Mum, I’m ok.”
“Ta ya ya? Fu’ad ba ka jin magana, na hanaka gudu a titi. Kai ko yaya ranka ya ɗan ɓaci sai ka ɗau mota. Na hanaka amman ba ka ji.”
Sai a sannan ya kalli Hayat wanda tun tsayuwarsa ko kallon gefen da yake bai yi ba.
“Yanzun ma kin yi niyyar ƙara ɓatamin ne shiyasa kika taho da abinda zan gani na kuntata.”
Sarai Hayat ya gane, wannan abu na ci mishi tuwo a kwarya. Ya daure fuska tamau, wani kallo ya watsawa Salma sannan ya fita. Tana kiran sunansa amman ko juyowa bai yi ba. Fu’ad ya murmusa. Ya tubure akan lallai sai an sallameshi. Ganin dagaske yake Salma ta nufi wurin likita. Dakyar ya rubuta sallama bayan ya tabbatarmusu ko me ya biyo baya toh ba laifinsa bane.
Yana dan ɗingisawa haka suka fita, har sun kai baranda asibitin ya tsaya.
“Lafiya?” Cewar Salma.
“Ina son magana da Dr.”
Da mamaki tace.
“Me kuma kake ji? Ina ke ciwo yanzu?” Ta fadi a hargitse tana tattaɓa wurin raunukan. Ya ture hannunta cike da ƙosawa.
“Haba Mum, na faɗamaki naji sauƙi ko? Kawai magana nake son yi da shi.” Ba ta yi musu ba suka juya yana dafe bango har ofis din likita. Ganin da wani ciki sai da suka jira ya fito sannan suka shiga.
“Fatan ba wata matsalar bace?” Ya fadi yana gyara zaman farin gilashinsa.
“No, kawai dai ina son tambaya game da mutumin da ya kawoni hospt. Bai ce zai dawo ba ko wani abu?”
Dr ya jinjina kai.
“Gaskiya bamu yi maganar ba, saidai ya ajiye lambar wayarsa akan duk abinda ake da buƙata na sanar mishi.”
Sai a sannan Salma ta tuna wautarta, hankalinta na ga ɗanta tilo har ba ta tuna da ta nemi wanda ya kawoshi asibiti ba balle ta yi tunanin yin godiya gareshi.
“Can I get it?”
“Sure.” Fadin Dr. Ya fiddo lambar Fu’ad ya dauka a wayarsa. Sannan ya yi godiya suka fito.
Hayat na zaune ya hangesu. Ba ya iya fushi da yaron, koda ya yi na dan lokaci ne, tausayinsa ya ji ganin yanda yake tafiya yana ɗingisawa. Idan ma ba ka gane ba sai ka dauka dingishin na ƴan gayun zamani ne.
Hangoshi da ya yi a mazaunin direba ne ya sanya shi zama a baya. Har suka je gida bai ce musu uffan ba. Yana ji suna batun karɓo motarsa a washegari nan ma bai da niyyar magana ya sharesu.
*****
Washegari da safe ya ji ana taɓa yatsun ƙafarsa, ya janye gami da jan tsaki don har yanzun kafar na mishi zafi. Ba’a daddara ya ji an kara riƙota, ya kuwa yi wata ƴar ƙara gami da miƙewa zaune a fusace.
“What the…Haidar?”
Ya zarce da fadin sunanshi, madadin wannan fusatar, sai mamaki ya cika taf a fuskarsa.
Siriri ne mai madaidaicin tsawo. Daga farin fata ya rine ya koma baƙi kamar na ƴan Sudan, ya tara gashi a kan. Leɓɓansa baƙiƙirin sakamakon shan sigari, domin duk son Fu’ad da sigari bai kai shi ba. Shi bai ƙi ya zuƙe kwali a wuni guda ba.
“Yaushe ka iso? Isowar ma nan garin ba Kano ba?”
Haidar ya yi dariya ya zauna.
“Burina na shayar da kai mamaki. Wannan duka plan din Mum ne. Ita ta tsara na yi maka hakan.”
Ya fadamasa abinda zai iya don ba zai iya fitowa ya mishi bayanin ainahin abinda Salma ke so game da zuwansa Yobe ba. Sanin da ta yi maganarsa nada matukar tasiri akan Fu’ad hakan yasa ta nemi ya zo ko don ya lallaɓashi su je dangin Hayat. Umarnin Boka take so ta cika, ta shagalar da shi daga barin tunanin dangin Mahaifinsa ta hanyar daukemishi hankali akan na Hayat da yin duk kokarinta.
Yamutse fuska Fu’ad ya yi kawai bai ce uffan ba. Yana gani Haidar ya zaro sigari ya kunna ya shiga busawa. Hannu ya miƙa masa domin ya ba shi, ba musu ya miƙa. Nan kuma suka shiga hira har Fu’ad ke labarta mishi batun Hanan sabuwar babyn da ya yi. Hira sosai ta ɓarke har sai da Salma ta katsesu. Ta shigo ta ci uban ado da wata rantsetsiyar shadda pink wacce ta sha aiki.
“Welcome Haidar. My son, Ina fatan ka yi murna da wannan surprise din?”
Ya yi murmushi gami da ɗan ɗaga gira.
“Yes, thank you.”
Har ranta ta ji dadi.
“Ko zan sami rakiya idan kun yi breakfast? Kaima sai ka kara jin daɗin jikinnaka.”
Kafin Fu’ad ya amsa Haidar ya cafe.
“Sure, why not? Tashi ka yi wanka mu yi breakfast, mu wuce.”
Fu’ad ya yi fuska gami da kauda kai, sai da Salma ta kara sa baki gami da narkewa kamar za ta yi kuka. Sai ta ɗan ba shi tausayi, ya mike bayan ya ja tsaki yana ɗan ɗingishi wanda idan ba ka sani ba sai ka dauka na gayu ne. Banɗaki ya faɗa ya yi wanka, jim kadan ya fito. Wasu sabbin kaya ya gani shadda farare ƙal saman gado. Wata ƴar murmushi ya yi na rainin wayo, ya karasa ga wardrobe dinsa. Haidar ba ya ɗakin ya fice tuni. Yana cikin shafar mai yana tuno da mutumin da bai san sunansa ba. Shaf ya mance bai yi kiransa a waya ba balle ya kara mishi godiya. Idan da wani zai ce yana da wannan kirkin zai iya musantawa akan ba hakan bane. Sai dai abin mamaki yau shi ne ke son kiran wani da ya yi mishi taimako don yin godiya gareshi.
“Wow!” Ya faɗi yana ɗan ta6e baki da murmushi.
“Da akai me?” Ya kai duba ga Haidar, sak irin kayan da ke saman gadon su ne a jikinsa. Duk da tarin sumar da ke kansa haka ya dage ya sanya hula. Fu’ad ya yi ta dariya, yau ga Haidar da manyan kaya. Abu ne da bai ta6a gani ba. Haidar ya kai mishi naushi sai ya tuna da rauninsa ya fasa gami da dunkule hannun suka dara. Ko kallon kayan bai ƙara yi ba, a cewarsa bai ga dalilin don zai yi rakiya sai ya sanya wasu manyan kaya ba. Rigarsa ya sanya light blue mai karamin hannu sa dogon wandon jeans baƙi. Ya gyara sumar kansa wanda da kaɗan ta fi ta Haidar. Ya gama fesa turarukansa ya fito don tuni Haidar ya bar ɗakin.
Salma ta dubeshi kamar ta yi magana sai ta fasa, ba ta son ja in ja da shi har ya ji cewar ya fasa. Ta kara shigewa ɗaka ta zizara kwallinta idona idonku. Ba ma ga Fu’ad kadai zai yi tasiri ba har akan dangin mijinta. A lallai sai ta siye zuƙatansu da kyauta da kyautatawa. Da haka ta sakarwa kanta murmushi ta fito. Raunin kan Fu’ad wanda ke nannaɗe da Bandage na ƙara sanyata nishaɗi, ko ba komai wannan ma hujja ce ta rashin zuwa wajensu akan lokaci.
*****
“Indo dai? Ke din ce?” Fadin Inno tana duban Humaira baki a hangame. Humaira na dariya ta sanya hannu ta rufe bakinta. Inno ta yi mata daƙuwa ana dariya.
“Yarannaki ni kaina ban ganesu ba.” Fadin Mama tana murmushi.
“Yo ina fa? Ji dai wannan Rukayyar kamar wata Aljana, kwalliyar ma banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Ni jiyan nan da naga Nuriyyah sai da gabana ya fadi don a farko tsoro diyarnan ta bani. Sai da na kira sunanta ta amsa na hangi tabon sallar goshinta na gane mutum ce dai a gabana.”
Dariya sosai Inno ta ba su. Kiran da aka shigo aka yiwa Inno da Maryam ne ya sanya su ficewa.
Gidan kowa ya ci kwalliya kasancewar ranar daurin aure ce, da daddare ne za’a je Dinnerparty. Fuskar kowa cike da annuri. Dankwalinta ta dauka tana duban Jamila.
“Lah, bari naje na roki mai kwalliya ta yimin ɗauri.”
“Sai ki tafi ke kadai, ba ruwana ba zan je waccan matar ta cigaba da hararata ba.”
Jin haka Humaira ta juyo tana mai riƙe ƙugu.
“Wace mata?”
“Wannan kawar Anti Nuriyyah ɗin nan. Ya ma sunanta?” Ta tsaya tunani.
Can ta tuna.
“Oh, Ameena.”
Zama sosai Humaira tayi.
“Ke ashe kin lura kema? Ai wallahi ta bi a hankali ko nayi mata rashin kirki ma. Haushi take bani Tun sadda ta gwada ba ta sonmu wai mu yan ƙauye ne.”
Ta ƙarashe tana mai kwafa.
“Ki rufamana asiri, kin dai san Mama ba za ta kyalemu ba.”
Ba tare da ta ce uffan ba ta miƙe ta fita. Jamila na kira sai dai ko sauraronta ba ta yi ba.
A dakin Nuriyyah ta tarar da su gaba daya, Nuriyyah na zaune ta yi shiru don yau gaba daya jikinta ya yi sanyi irin wanda aka sani ga budurwar da za’a daurawa aure.
Tun shigarta Ameena ke watsamata banzan kallo. Ta dauke kai ta zauna gefen Nuriyyah.
“Kanwata, ya akai? Kin yi kyau?” Ta fadi a sanyaye, ba ta da kanwa mace, wannan ta sanya yara ke burgeta musamman mata.
“Ba komai, daurin dankwali nake so a yimin.”
“Mtsww!” Suka ji an ja tsaki, kowa ya dubeta. Ameena ce.
“Ke kuma ke da wa?” Faɗin Rayyanatu cousin din Nuriyyah.
“Wanda ya tsargu.” Ta amsa da gatse. Aka sa dariya.
“Kai Hidaya! Handsome fa ya kwafsamin. Haka na bi shi har wurin mota sai dai abin takaici, na sha kunya.” Cewar Khadija. Ta miƙawa Hidaya hannu suka cafe suna dariya. Da gayya Khadija ta dubi Humaira.
“Humaira ya sunan wannan haɗaɗɗen da na ganku tare ma?”
“Aikin banza, kowa dai ya yi zagi a kasuwa ya san da wa yake. Sannan idan fitsari abin banza ne kaza ma ta yi mana!” Daga haka ta mike ta bar ɗakin fuu, Ameena kenan, duk aka bi ta da kallo ai kuwa nan aka ɗago bakin zaren, aka kwashe da dariya.
“Ba kya jin magana wallahi.” Fadin Nuriyyah tana duban Khadija. Wadanda basu gane ba suka hau tambaya, dama abinda Khadijah ke jira kenan. Ta shiga labartamusu yanda Ameena ta kwashe da Handsome har da yanda suka fahimci tana jin haushin Humaira. Abin ya bada mamaki da dariya.
Humaira mai kaifin basira da wayo, nan da nan ta ɗago bakin zaren. Ashe dama duk wannan daure fuskar da biyu Ameenar ke yi. Ta yi shiru, duk da yarinya ce ta gane wato kishi ake da ita. Ita ƴar yarinya da yanzun ta soma ƙirgar dangi?
“Hum um!” Ta furta a fili, miƙewa ta yi, ta ma bar batun daurin dankwalin. Koda Nuriyyah ta kira cewa tayi a barshi. Da zumuɗi ta karasa ɗakinsu ta fesawa Jamila. Suka shiga kyakyata dariya gami da cafkewa.
“Ba ta da wayo, za ta san ta ta6o tsuliyar dodo. Cabdin! Allah Yasa yau ma na hadu da ɗan Biyutiful.”
Jamila wasu lokutan bata da magana hakan ta sanya ta kallonta kawai ba tare da sanin me take nufi ba.
*****
A daidai kofar gidan suka tsaya, jama’a sun soma taruwa kowannensu ya sha shadda. Ƙamshi kawai ke tashi ta ko’ina. A hankali ya maida gilas ya zuge sama. Ya dubeta ta gilas.
“Mum, za ki sauka ko muyi gaba da ke kin fasa?”
Ta harareshi.
“Ni na fadi hakan? Iyakar rakiyar da zan samu kenan?”
Ya ja guntun tsaki.
“Please Mum, ba haka mukai ba. Kar ki takuramin.”
Ba ta musa ba ta sauka, cikin isa take taku har ta wuce dandazon jama’ar zuwa cikin gidan. Ya dubi gefen Haidar zai ba shi umarnin ya ja mota, caraf idanunsa suka kai gareshi. Ya mike daga kwanciyar da ya ɗan yi jikin kujera.
“What a coincidence, mutumin da ya taimakamin ne.”
Jin haka Haidar ya kai duba ga inda ya nuna. Yana tsakiyar yan uwansa da abokinsa Dr Ibrahim wanda ya zo mishi daurin aure sai fara’a yake. Ya haɗe cikin farar shadda ƙal mai aiki ash.
Haidar ya juyo fuska cike da tambaya, sai dai gani ya yi wayam babu kowa a seat din. Ya waigo ya hangi Fu’ad na nufar inda guy din yake. Mamaki ya hanashi motsawa, me ya sauya Fu’ad har haka? Yana mamaki yana kara mamakin hakan.
“Hi.” Suka ji an furta hakan ya yi sanadin katse hirarsu, gaba daya suka dubeshi. Mamaki ya cika Adam, me yake yi anan? Duk da cewar gidansu mijin Mummynsa ne, bai yi zaton a taurin kan yaron da tun yana karami bai ta6a takowa ba, zai zo a girmansa.
“Assalamu Alaikum.” Fadin wani Waleed yana miƙawa Fu’ad hannu. Da dan murmushi ya miƙamishi yana maimaita yanda ya faɗi.
Waleed bai damu ba ya bada amsa yanda ya kamata. Guntun tsaki Adam ya ja, ya tabbatar ba shi da wani ilimin a zo a gani na addininsa.
Hannu ya miƙomishi yana sallamar. Sanin girman hakan ne yasa ya miƙa mishi suka yi musabaha.
“I hope ka gane ni?”
Dr Ibrahim suka zama ƴan kallo ganin Fu’ad har da su ɗan kunne irin na mannawa a kunnensa. Tunaninsu ina ya samo wannan?
Adam takaici ya ishe shi. Ya ƙi bada amsa. A zaton Fu’ad bai ganeshi ba, don haka ya yi mishi nuni da kansa da ke ɗaure da Bandage.
“Wanda ka kai asibiti jiya.”
“Ok.” Adam ya furta a takaice.
Sai ya ji ba dadi kadan, yana son bayar da shi a gaban mutane. Dr Ibrahim ya yiwa Adam ido. Shi kuwa Fu’ad ya kasa hakuri.
“Ina son kiranka ai but ban sami chance ba sai kuma ga shi kun haɗu anan. Na fa gode sosai.”
“You are welcome.” Ganin ba fuska bai san sadda ya ce.
“Ai tare muke da Mum dina, ta shiga ciki.”
Adam ji ya yi kamar ya riko kan yaron ya nutsar a cikin ƙasa tsabar takaici.
“Ok, muje lokaci na ƙurewa.” Fadin Adam yana duban abokansa. Ya dubi Fu’ad da murmushin yaƙe ganin idanun abokan tafiyarsa na kansu.
“Na gode sosai fa.”
Fu’ad ya maida martanin murmushin jiki a sanyaye. Bai san me ke jansa gareshi ba, haka kurum yake jin kaunarsa da zuciya ɗaya. Da wani zai ta6a fadamasa zai jure koda tsayuwar mintuna biyu ne a gaban mutanen da bai gani da ƙima a baya ba abinda zai hanashi zazzaginsa. Yau gashinan shi ne abin wulaƙantawa.
“Ko kaima wurin daurin auren ka nufa?” Fadin Dr Ibrahim ganin yanda kunya ta kama Fu’ad a dalilin yanda Adam ya mishi. Lokacin Adam har ya kama handle din kofar motarsa zai bude sai ya dakata don jin amsar da zai bayar.
“Eh.” Ya tsinci kansa da faɗi ba tare da ya shirya ba.
“Ya Rabb.” Fadin Adam a zuciya. Takaici yake, ba ya kaunar yaron. Ya kausasa murya.
“Dr ina jiranku.” Dr Ibrahim ya dubi Fu’ad
“Muje, ko a mota kake?”
Ya gyaɗa kai.
“Yes, ina tare da friend ɗina ne. Venue please?”
“Ina zuwa.” Fadin Dr Ibrahim. Motar Adam ya nufa inda ya ga Iv card a barbaje cikinsu har da na dinner guda biyar da aka ba shi koda zai yi gayyata. Ya dauki kowanne bibbiyu ya ba Fu’ad. Godiya ya yi ya juya.
“Kana da matsala wallahi.” Fadin Adam a fusace yana duban Dr Ibrahim lokacin da suka shige mota. Sauran tawagar duk an soma tafiya.
“Matsala a ina? Kai ne mai matsala. Haba Adam, ko waye shi, ko wani abun ya ta6a yi maka da ba ka ji daɗi ba ai bai kyautu ka disgashi gaban mutane ba har hakanan. Yaron da bai fi sa’an Ammar ba (kanin Dr) ga dukkan alama jininshi ne ya haɗu da kai kawai. Irinsu ake so a dinga ja a jiki da nasiha da komai sai ka ga Allah Ya shiryar da su.”
Wato dai ya fahimci daga kallon yanayin Fu’ad da kuma ɗan kunnen da ke kunnensa, Dr Ibrahim ma ya gane ko waye Fu’ad.
“Ba ka ji ba?” Ya fadi da alamun fada.
Ya dubeshi da ƴar dariya
“Na ji Babana. Kada ka doke ni.”
Suka dara.
“Toh naji amman meye na daukar iv card har na dinner ka ba yaronnan? Ni nace maka bana kowa bane?”
Harararsa ya yi.
“Bansani ba, inace yanzu ka gama cemin na su Hamza ne ka ɗauka tare zamu taho? Yanzu kuma tunda bamu taho taren ba ai kuma ya zama rabon mai rabo.”
Adam ya tayar da mota tana murmushi bai ce komai ba.
“Kai ni wallahi kuma ɗan yimin yanayi. Kodayake wancan ya fi yanayi da dangin Abbanku.”
Ras! Ya ji gabansa ya faɗi. Abinda yake gani ne tun ba yanzu ba kuma yake yaƙar zuciyarsa yana kauce mishi da iyakar karfinsa. Yanzun ji ya yi kamar a cusa dusa a kwakwalwarsa sam ya kasa tunanin komai. Don haka ya yi azamar dakatar da Dr Ibrahim sa’ilin da ya harba motar titi.
“Ba kowanmu bane. Kawai dai Mum dinsa ke auren Abba.”
“Oh, sorry.” Fadin Dr Ibrahim yana mai bar wa cikinsa, hannu ya sa ya ware karatun Alkur’ani. Sai da ya ji Ibrahim ya dau wata hirar sannan ya kashe.
*****
“Idan ba ka bar kallona ba duk abinda nayi maka kai ka ja. Stupid kawai. Yi abinda ke gabanka.”
Haidar ya yi dariya har da dukan sitiyari.
“Wai mafarki nake? Kai ne yau da halartar daurin aure? Kuma zuwan da ba shiri? Meke faruwa haka?”
Fu’ad ya runtse ido.
“Kuma na gidan wannan maƙiyin nawa.”
Ya gane Hayat yake nufi.
“Kasan me? Kawai jin guy dinnan nake kamar wani dan uwana da muke the same Dad da shi. Dagaske kawai ina jin kaunarsa ne bansan dalili ba.”
Jinjina kai yake yana dariya. Shi kawai abin mamaki yake gani wanda bai zata ba. Su na isa gidan ya sauya kaya wanda Mum ta ajiye ya ƙi ɗauka. Ba karamin kyau kayan su ka mishi ba. Ya koma kamar wani buzu. Hular kansa ta ɗan rufe Bandage din da ke zagaye da kannasa. Turarukansa ya fesa sannan ya fito. Sakin baki ya yi yana kallonshi, ɓata baki ne ma wurin faɗin kyan da kayan suka mishi. Yana shiga suka bar gidan, a hanya da kwatance suka isa wurin. Cike taf ya hangi wurin. Ya rasa ta inda zai hangeshi. Ya ga dai motarsa da ya hau a wurin.
“Wai kai ina zamu je ne? Wa muka sani?”
Fadin Haidar, ya dubeshi yana harara sai dai bai tanka ba. Haka suka dinga ratsa jama’a, da yawa kan yi zaton shima Ango ne su shiga miƙa mishi hannu, makaɗa har binsa suke. Nan da nan ya soma gajiya da taron, ga babu ta inda ya hangesu. Dr Ibrahim ne ya hangosu ya yi saurin zuwa gareshi. Dakyar ya ganeshi domin ba don ɗan kunnensa ba zai iya rantsewa ba shi bane. Ya kuwa ja su zuwa inda suke tsaye.
Tun yana dan ba shi amsa sama-sama a taron har dai ganin idon jama’a ya sanya shi soma yi mishi yaƙe. Bayan an watse taro kowa ya yi nashi wuri. A mota Haidar ya dinga budewa Fu’ad wuta wai akan me zai dinga cusa kai inda ake wulakantashi. Kuma wurin namiji ba ma wata mace ba. Ganin zai dameshi ya duramasa zagi da harshen nasara a dole Haidar ya ja bakinsa ya yi shiru kowannensu kuma ya kauda kai ba wanda ya tankawa wani.
A can haka Dr Ibrahim ya yi ta nemansu don zuwa reception amman bai gansu ba. Duk ya wani damu kansa har abin ya soma ba Adam haushi. Dakyar ya janye maganar ganin ba fuska.
*****
A bangaren Salma kuwa, ba wanda bai mamakin ganinta ba. Sai dai kasancewar ta iya takunta. Nan da nan ta kwatar da kai ta basu hakuri gami da yin ladabin karya. Kwalli kuwa ya yi aiki ƙalilan ne suka yi mata kallon bata isa ba, da yawa kam ciki har da matar baban Engineer Bello sun karɓeta da hannu bibbiyu. Umma ta je gidan Hashim hakan yasa ba su hadu ba sai Amira suka gaisa tana ɗari-ɗari. Koda za ta tafi haka ta cikasu da abin arziki. Ta shiga gidan su Umma ta gaida su Malam Kabiru. Jin matar Hayat ce bai sa sun mata kallon banza ba, anan ta ga uwar ango Baba Usamatu. Ta kuwa cikata da abin alheri, Baba Usamatu ba daga nan ba wurin son abin duniya. A gaban su Yaha ta yi ta rangaɗa kirari ga Salma kamar wata maroƙiya. Wannan abun ba karamin kunya ya basu ba sai dai ba wanda ya ce uffan. Haka Salma ta tafi da yawa a dangin su na haba-haba da ita. Da wannan farin cikin ta yiwa direban Hayat waya ya zo ya ɗauketa ta bar gidan tana ƙara gasƙata tasirin da kuɗi keda shi ga dan Adam. Yau kam ta ƙara ganin ranarsu.
*****
Misalin karfe takwas na dare aka soma tafiya wurin Dinnerparty. Su Humaira kamar yanda akai anko wancan karon na yara, haka akai a wannan ma. Wannan karon wani golden material akai musu dogon riga. Sai silver head. Bakinnan sai maiƙon jan baki yake. Hatta da kwalliyarsu iri daya ce. Sun saje sosai da yan Yobe ba za ka ta6a cewa daga kauye suka fito ba sai idan sun tafka wata shiriritar. Wurin ba karamin kyau ya yi ba, ya burgeshi sosai. Wannan karon ma wurin zaman iyaye daban, kawayen amarya ma haka, sai su flower girls da kuma wurin angwaye wanda ke kusa da su.
Da kadan-kadan aka soma cika. Ya shigo wurin tare da Dr Ibrahim. Anko sukai na wani arnen Voyel ruwan purple. Sai baƙar hula, ya zauna sosai a jikinsu ya haskasu sosai. Suka ƙarasa inda sauran abokan suke suka zauna. Ba jimawa da zamansu ya hangeta. Kwalliyarta ba karamin burgeshi ta yi ba. Ga dukkan alamu ba ta lura da shi ba sam don kacokan hankalinta yana ga wayar wata yar budurwa da ba ta wuce sa’ar su ba su na hotuna. A sace ya ɗaga wayarsa ya shiga ɗaukarta a hoto. Sai da ya yi mata kala kusan biyar ana goma ya haska hannu. Sauke wayar ya yi yana duban Dr Ibrahim. Da dariyar zolaya ya ce
“Are you in love?” Ya ji faduwar gaba sai dai ya daure fuska gami da kauda kansa.
“In love with who? Kar ka dauki abin da ka gani a baibai. Ba shi bane. Kallon kanwa nake mata.” Nan ya labarta mishi yanda sukai a ranar yini. Ya yi dariya sai dai bai ce uffan ba. Yasan ko me zai ce ba lallai ne Adam ya yarda ba don haka ya ja bakinsa ya yi shiru. Ba jimawa Amarya da Ango suka halarta. Wannan karon saboda idon Dr bai fita waje ba duk da yanda ya so ya yiwa Humaira magana a lokacin. Kawai ya ja ta da tsokana ma kadai burgeshi yake.
Ba jimawa da zaman su Nuriyyah aka shiga shagalin biki.
Daga inda take zaune ta ke hangen yanda diyarta take wani juyi da rawar kai, ba ta san sadda tayi murmushi ba. Kamar da wasa ta soma jin wata iska na wucewa ta kunnenta shuu, shuu. Ta ɗan dafe kunnen don a zatonta wani abin ne ke kokarin faɗawa ko y faɗa, kamar da wasa ta ji wurin ya yi duum bata jin komai sai wata kara a kunnen. Ta soma ambaton Innalillahi a zuciyarta. Ganin dagaske ne ga wuri ana ta kaɗe-kaɗe amman ba ta ji, sai ta dubi Inno dake gefenta. Za tayi magana ta ji kamar an shaƙe maƙogwaron. Ta tsinci kanta da motsa bakin kawai amman ba uhm ba uhm uhm.
A cikin mintuna kadan ta fahimci abinda ya sameta, innalillahi ta ci gaba da maimaitawa a ƙasan ranta. A hankali wasu zafafan hawaye suka taho tayi azamar sharesu da hannunta. Ba za ta tashi hankulan mutanen wurin ba, ba za ta ruɗasu har su ji taron ya fice a ransu ba wannan ta sanya ta yi shiru gami da saurin share fuskarta ta hau murmushin yaƙe. Tana ci gaba da ambaton Allah a ƙasan ranta. Sai dai kafafunta har rawa suke tsabar tashin hankali.
*****
Kallon harabar wurin ya ke yi daga cikin mota yana zuƙar sigari. Ƴan matan da ke Safa da marwa yake ƙarewa kallo. Taɓoshi ya ji an yi.
“Guy, Idan ba za ka shiga ba ya kamata mu bar nan tunda Mum ta shiga ma dawo mu dauketa. Mu tafi kafin nayi ɓarna, ka san dai idona idon babies ba magana ko?”
Maganar Haidar ta katseshi. Bai ce komai ba har sai da ya zuƙe tas sannan ya yi amfani da mouthfreshner masu karfi ya fesa har kala biyar bakin. Orbit ya dauka ya jefa a bakin sannan ya bude motar ya fito. Ganin haka Haidar ya fito. Anko sukai na brown yadi irin na Morocco. Ciki suka nufa kai tsaye bayan sun ba da gate-pass. Wannan karon ganinsa bai musu wuya ba sosai, suka ƙarasa har wurin da suke. Gaisawa suka yi. Bai ta6a zaton ganinsa ba a wurin, wannan abu ya ɓata mishi rai. Ya kauda kai yana daure fuska, Fu’ad ya gane sarai, bai yi niyyar zama ba ya so ne su gaisa ya tambayi sunansa su wuce. Amman da gayya sai ya zauna gefensa, guntun tsaki ya ja.
“Adam, meyefaru ne?” Cewar Dr. Nan ya gane sunansa Adam. Murmushi ya yi ya fiddo gilashinsa ya manna a idon.
“Kana shan sigari ne?” Ya ji tambayar daga sama. Ya dubeshi. Ya akai ya gane? Ganin kallon rainin da yake mishi sai ya kauda kai.
“Yes.” Bai ce uffan ba ya maida hankali ga danna wayarsa.
“Dan Biyutiful!” Lokaci guda suka ɗago kai suka dubeta, ba wanda ya iya kauda idanunsa a cikinsu. Ita kuwa sai murmushi mai bayyana haƙora take zabgawa mai ƙara fiddo da tsantsar kyawunta da yarinta.
Lokaci guda suka tsinci kansu da sakin murmushin a tare. Idanunta na kan Adam, idanun Fu’ad a kanta. Ta shagwaɓe fuska.
“Ina ta nemanka, na sha ba ka zo ba.”
Ta ƙarashe tana yatsine fuska. Murmushin dai Adam ke yi.
“Afuwan Gorgeous, ai gani. Kina da magana ne?”
Ta kuwa gyada kai gami da yi mishi alamar ya zo da hannu. Ba musu ya mike, ita kuwa ta koma ta jawo Jamila suka bi bayansa zuwa waje. Ya tsinci kansa da miƙewa, so yake ya bi bayansu sai dai ya ce musu me? Ya rasa bakin magana.
*****
Kamar ance ta ɗaya idanunta, ta hangota zaune wurin dangin Ango. Kujerar da ke fuskantarsu. Damƙe hannun Hajjo ta yi ba da shiri ba, gaba ɗayanta sai ta hargitse. Ta sanya mayafi sosai ta rufe fuskarta wani irin gumi da rawar jiki na faruwa da ita lokaci guda. Hajjo a firgice ta dubeta.
“Maryam lafiyarki kuwa?” Shiru babu amsa. Me ta san ma tana faɗa.
Ta rasa yanda za ta nunamata so take ta bar wurin kawai sai ta soma kuka da rawar jiki. Salati Inno ta shiga yi, ba don muryar Dj da ya ware kiɗa ba, babu abinda zai hana saura su hankalta. Su Inno na gida ba su zo ba. Hajjo ta ruɗe sosai, ganin Maryam ta miƙe itama ta mike gami da jan hannunta su fito waje hankali a tashe.