Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Sa'adatu by Usaina Salisu

TAKUN FARKO DA ƘARSHE

Godiya odiya ta musamman ga iyayena,da ‘ƴan’uwana da masoyana, Allah ya biya wa kowa buƙatarsa ta alkhairi, amin. Duk wanda suka mutu Allah ya yi masu rahama ya sa Aljannah ce makoma. Idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani, amin. Wadanda ba su da lafiya gida ko asibiti, Allah ya basu lafiya, amin. Wadanda suke neman haihuwa, Allah ya basu. Masu son aure, Allah ya tabbar da alkhairi, amin alfarmar farin jakada Annabi Muhammad S. A.W.

Jinjina da godiya ga Sadiq Abubakar da Haiman Raees.

Godiya ga aunty Surayya, Hasina, Fatima Muhammed, Fauziya Sani Jibiril, Ummul Kursum, Sadiya Ko’ajo, da sauran mambobin Lafazi Writers’ Association bisa gudummuwar da suke ba ni.

Ba zan manta da ke ba, Zainab Yahuza (Besty) da Rabiya Rabe da sauran masoya wannan littafin.

Bissimillahi rRahamanun Rahim 

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammed (S.A.W), Ameen. Na godewa Allah da ya bani ikon rubuta wani sabon littafin mai suna SA’ADATU. Ina mai roƙon Allah S.W.T., yadda ya bani ikon rubutashi lafiya, Allah ya sa na gama shi lafiya cikin aminci, Allah ya hane ni da rubuta abinda ba zai amfanar da al’ummar Musulmi ba, amin.

GARGAƊI

Ban yarda ba a canja min littafin nan koda da kalma ɗaya ce, ko a ɗora min shi, ta yanar gizo ma’ana a karanta shi a Youtube ba tare da izinina ba. Duk wanda yayi haka shi da Mai sama, Allah ya sa mu cika da imani, amin.

Wannan littafin mai suna, SA’ADATU ƙirƙirarrar labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba. Duk wanda ya yi daidai da halayyarsa ko ɗabi’arsa  akasi ne. Fatan za a yi min afuwa.

Sadaukarwa ne ga masoya wannan littafin.

Babi Na Daya

Why fatima? mi yasa! mi yasa!! za ki rabudani a lokacin danake tsanannin buƙatarki,kar kimantafa ina matuƙar sanki sama da rayuwata danmi zakaimin haka wlh inasanki ki,fatima!

Ki tausayamin fatima miyasa zaki hukuntani akan laifin daba nawaba? turƙusawa yayi a ƙasa ya kama hannuta  yana hawaye, fusge hannuta tayi  tace wannan kai tashafa tare da  jan dogon tsoki  cikin halin ko un kula tayi tafiyarta tabarshi yashe kamar batasan waye ba,

Gurin wani dattijo tanufa tana zuwa gurinshi batayi wata wata ba ta afka cikim motarshi,kallon ahmed tayi cike da rainin wayo da wulaƙanci ta ɗagamai gira ɗaya tare kashe mai ido ɗaya tana dariya

Juyowa tayi gurin tsohun nan shi kuma  ya matso  ya  rungumeta a cikin motar, a saitin da ahmed zai gani.

Magana ya mata a satin kunnanta tare da sunbatar ta, sai magana yake mata ba ƙaƙƙautawa a harabar titi ko kunya basaji,  ya yinda ahmed yake ganin kiss yakemata wata irin  zabura yayi mai kama da gigicewa, ya tafi da gudu gurinsu domin kaiwa tsohon nan duka  saidai kash! hakan batasamu ba,saboda bodygaurd ɗin dake gurin basu bashi damar isa inda boss ɗin nasu yakeba.

Da shi da babynshi fatima wacce takasance budurwar Ahmed ce,Ahmed gurin ya durƙushe yana ta kuka ya ɗora hannu  shi a samar kanshi abun duniya yadamai ya shiga damuwa matuƙa yarasa yadda zaiyi,”Fatima” tacuce shi ƙirjin shi ya dafe daidai satin zuciyarsa tare da kwantawa ƙasa idanunshi suka fara canza kala daga baƙi izuwa fari tashin hankali da ba’asamai date!

Ya shiga damuwa matuƙa yarasa  yadda zaiyi da zuciyarshi,  yasha ƙananan kaya sai ƙamshi yake sunsha guga fari tas dashi aji  farko, haɗaɗɗe  saurayin ɗan kimanin shekara ashirin da da bakwai dafen saitin zuciyarsa yayi tare da zubewa ƙasa warwas  fatima suna tsaka da soyayya taga ahmed warwas a ƙasa bashiri tature wannan alhajin gefe taɓalle murfin motar tafi da gudu zata gurin ahmed saidai kafin taƙarasa bodygaurd sun dakaratar da ita bisa umarnin boss ɗinsu

Fatima haƙanta  bai cimma ruwa ba domin kuwa tsohon yasa bodygaurd ɗinshi su tareta, Alhajin nan ƙarasawa yayi gurinta, tare da kama hannuta yafara janta izuwa mota ture hannushi tayi tafara ihu tana kira ahmed wayyo zai mutu kabarni naje gurinsa dan allah ya yinda yake ta jan hannuta ko sauraranta baiyiba, bodygaurd ɗinshi suna take masu baya. lumbashin ahmed sai go and come yake daga ƙarshe  ya tsaya cak!

Jikinshi Ahmed ya saki  ma’ana yayi warwas cike da tashin hankali ta warce hannuta tare da daka mai wata uwar tsawa! wacce ta zarazashi  tace kana ganin zai mutu dama haka mukayi dakai? Ta hankaɗa shi gefe yayi tagal tagal zaifaɗi, Cikin sauri ya riƙo hannuta  tare da ware hannushi tafkeke kai wannan daga ganima bana mutum bane yadage  ya zafgabata mari  tass tasss !!!!kakeji.

Wanda ya janyon hankalin bodygaurd ɗin,  “kallon kallon akafara” bamai iya cewa komi  domin hangazashi datayi abun ya matuƙar ɓatamai rai, dafe kunci tayi cike da mamaki tace nika mara? lalle ka kyauta indai nice zakagani…. Ta juwa cikin ɓacin  rai ta nufi gurin Ahmed da gudu ya yinda bodygaurd suka bata hanya

Jikin wannan tsohon ne yayi sanyi da ya tuna yadda akayi ta biyoshi, juyawa yayi ya shiga mota sukabar gurin suna masu tada ƙura da motar su,fatima da kallo tabi motar su tana maijin zafin marinta da yayi…Tayi alƙawarin ramawa dazaran Ahmed yasami lafiya, ɗago da ƙafaɗar shi tayi tana jijjigashi tana cewa ahmed katashi ba abunda zaisameka, gashi unguwar ba mutane sosai saidai ɗay ɗaya  addu’a tafara allah yakawo mota su tafi asibiti kartaje ya mutum!” ya zatayi? Tashiga damuwa sosai  hawaye take zubarwa.

Wata napep ce ta shigo kwana kamar anjefota fatima juyawa tayi takalli napep ɗin “Alhmdulilah” Tace domin addu’ar ta ta amsu shiga,tun kafin ta idasa gurinsu ta kwalamata kira tana  tsaida mai napep…… gurinta yayi  daidai inda suke yaja birgi fitowa yayi ya taimaka mata yayi ta kama  ahmed suka sashi a  napep ɗin, Shiga tayi ta  zauna  ta ɗora kanshi a kan cinyarta, airforce suka nufa asibitin sojoji cikin ɗan ƙanƙanan lokaci saigashi sunje asibiti shiga sukayi da gudu fatima tafita ta kirawo likita, Da gado suka taho suka fiddo ahmed suka ɗorashi a kan gadon marassa lafiya,danda nan aka shiga dashi emergancy aka fara bashi kulawa  cikin gaggawa

Akayi sa’a lunbashin shi yadawo ya kuma daidaita saidai bugun zuciyarsa yana ƙaruwa likitoci suna bakin ƙoƙarinsu ya yinda fatima take ta zarya a gurin tana kai da komowa takasa tsaye takasa zaune tana tuna idan fa ya mutum tashiga ukku ko ƙannansa kadai sai sunkusa sheƙeta dandaima tana da masifa bazasu ƙwareta ba sosai, Ahmed  bugun zuciyarsa ya daidaita ya yinda yake kiran sunan “Fatima” yana dan allah karkimin haka idanunsa a rufe likitocinne suka kalli juna sukace A wannan a maganar soyayaya ce,

Ko wacce ta kawoshi ce Fatima? bari na  kirawota cewar wani daga cikin su mai suna Aryan dama su biyu ne docter sadiq da docter ahmed, fita docter Aryan ya yi domin ya kirawa fatima  Alhajin nan suna tafiya a mota yaji yakasa nutsuwa da yabar fatima a wannan gurin gashi ya mareta shi kuma sbd kar bodygarud su ga rauninshi shiyasa ya yi hakan ammah bada sanranshi yamareta ba sbd  kar jami’in tsaronshi su rainashi shiyasa yamareta ta yadda ta tureshi a gabansu.

Hankalin shi ya kasa kwanciya yasa yace wa driver ya juya kan motar domin komawa gurin fatima motar suka juya suka dawo gurin da sukabar fatima saidai ga mamakinsu babu ita babu alamarta buɗe motar  ya yi ya fito suma bodygarud fitowa sukayi suka tsaya, waige- waige suka fara ko zai gangota saidai ko ɗuriyarta  bai ganiba hakan yana nufin tatafi  cike da ladama abinda yayi mata yakoma cikin mota sukabar gurin.

Wayar shi yajawo daga Aljihu ya kirawo Lambarta  sai yajita tana ƙara a kusa dashi alamar tabar wayar a motar juyawa yayi ya kalli wayar a bedseat ɗin dayake,  hannushi yasa yaɗau wayar ya kallah sai ya ajje tare da jan dogon tsaki,ya ajje wayar tunani ya fara ko ina zaiganta ‘yanzu tunanin shi idan yaɓace domin zuwa gurinta to su wannan bodygaurd yazaiyi dasu tunda sunkasance mutane ne shikuma da fatima ba mutane bane aljannu ne kawai bari yabarta sune mota daga baya sun haɗu a gurin da suka ajje zahara’au.

Docter sadiq fitowa yayi ya iske fatima sai sintiri take  magana ya mata kece kikawa wani saurayi cike da zullumi gabanta nafaɗuwa ta ce “Eh” nice docter miyafaru? ya tashi cike da damuwa take tambayarshi? kikwantar da hankalinki madam yasami sauƙi zaki iyashiga kiganshi “To” Tace cike da farin ciki, Da sauri ta nufi ɗaki da aka shiga dashi binta yayi da kallo yana murmushi yadda yaga ta ruɗe, bayanta yabi ya shiga shima ɗakin….. gadon ahmed tanufa daret har tana shirin yin tuntuɓe ta isa gurin shi tashi yayi zaune yana lunfashi a hankali kallonta yayi yace fatima kallonshi tayi cike da tausayawa tace ahmed yajikin naka “yace da sauƙi” tunda kinzo!

Hannuta yakama yace dan allah fatima kirabu da wannan mutummin please, kizo muyi soyayya muyi aure mu haifi ‘ƴaƴa please masoyiya yana magana hawaye nabin kuncinshi, jikin fatima yayi sanyi ammah tsabar ji dakanka bazaisa tace to ba, hannuta tazare daga hannushi ta tace yakake ji ƴanzu fatan bakajin zafi ƴanzu ko? hmmm kawai yace domin yasan da wahala ta canzu.

Wani lokacin kamar bata da tausayi ammah kuma yarinya ce mai tausayi dajin ƙai ammah baisan miyasa gabaɗaya ta burkuce hakaba,Aranshi yaji kamar ba Zarah ba, girgiza hannushi tayi tace yadai ina magana kana tunani yace a bakomi banajin komi tace to mizakaci nasa akawomaka? yace komi kikace naci! tashi tayi tafito waje ta nufi kichen ɗin dake asibitin domin samomar wani abu yaci!!!

KATSINA

Katsina cikin garin Daura wani ƙaramin ƙauye da ake cewa “Yar daji” rigace ta fulani  ƙyawawan gaske mafi yawan ‘yan garin  makiyaya ne, sun kasance suna kiwon shanu da dabbobi, Da sana’ar hannu, Gidaje ne ɗay ɗay  a garin  kowa yana harkar gabansa ba ruwan wani da wani saidai akwai zumunci a tsakanin su kusan fulani da zumunci kuma Sun kasance tawani ɓangaren yan,uwa ne, Can nahango wani   Gida anzagayeshi da iccen kara  ma’ana anyiwa gidan rufa da kara gidan sallau kenan bafulani Asali Dattijan Arziƙi mafiyan mutane nasanshi kuma sunabashi  girma a garin sosai mahaifi ga Sadiq Zahara’u da kuma Sa’adatu mutum mai haƙuri da sanin ya kamata

“SA’ADATU” ummo ta kwaɗamata kira tana daga gefen ɗaki ta hora wuta ta ɗora sanwa……, Duwatsune ta sanya guda ukku sune murhun sai kara datake sawa shine a matsayin iccen, Sa’adatu fitowa tayi daga ɗakin tana hamma da’alama daga barci tatashi gurin Ummo  ta nufa kai tsaye Domin Amsa kiran datayi mata ,Ummo gani  yawwa Sa’adatu kifita ƙofar gida kicewa sadiq yazo kufidda dabbobin nan kiwo domin naga duk yunwa sukeji gashi Baffan ku baikawo masu abincin dayasaba kawoma su ba, Ummo  mu fiddasu kiwo tananata Tambayar? Domin taji wannan shine karin farko zatafita kiwo tunda ƴar’uwarta ta ɓace Zahara’u Dama Zarah da Sadiq suke fitar da dabbobin Banda ita,Kuma Tunda Zarah ta ɓace basake fidda dabbobin kiwoba, sai yau tace suzo su fidda su, ko jiran Amsar Ummo batayi ba natabbatar mata dacewa za’afir daTimakin kiwo.

Cike da murna da ɗoki  tayi hanyar waje domin kiran sadiq “Allah sarki” UMMO  yau karan farko Taji wani irin ƙewar Zahara’u dabatataɓa jin irintaba Nan take siraran hawayen masu zafin gaske suka zubo daga ƙwayar idonta A daidai lokacin kuma su Sadiq suke shigowa cikin gidan shida Sa’adatu “Assalamu Alaikum” ɗago ido tayi tana kallonsu tare da Amsah sallamar su, Hannuta tasanya tafara   goge hawayen dasuke sauka daga  fuskarta, ammah damuwarta takasa ɓoyuwa Gurinta suka ƙarasa Sadiq ne ya kallah ta cike da alamar tambaya domin yaga lokacin datake goge hawayenta daga fuskarta, Ummo lafiya kuwa naga kina goge hawaye kasaɓoye damuwarta tayi tace natuna da Zahara’u ne, Sadiq.

Sadiq da Sa’adatu jikin su yayi sanyi Mussaman Sadiq wanda saida yaji wani abu a ranshi marar daɗi Ammah dayake shi Namijine kuma Jarumi sai ya danne damuwarsa YA zauna kusa da mahaifiyar tasa yace Ummo ki kwatar da hankalinki in sha Allah Zarah zata Bayyana Hannuta tasanya tashafa sumar kansa wacce take a kwance luf t tace Inanfatan haka ɗana Murmushi yasakar mata,Yawwa Ummo haka nake sanji cike da shagwaɓa yayi maganar hakan yaba Ummo dariya wacce har saida haƙoranta farare suka bayyana Sadiq shine mai share Ummo damuwarta Tunda ZArah taɓace Shine mai ƙwaikwayar halin Zarah.

Yawwa sadiq kutashi kuje kaida Sa’adatu ku fidda waɗancan dabbobin waje cikin gona domin suyi ƙiwo,Ummo Harda Sa’adatu zani? “Ae” mana minene ko bazaka da ita bane? kallonta yayi cike da tunanin karyatafi da ita abinda yafaru da ƴar’uwarsa shekarun da suka wuce yafaru da ita, Ummo tafahimci tunanin dayake yasa tace Sadiq kutafi Allah zaikiyaye ku kaji,Sannan kacire duk wani tunani dake marar kyau ga Sa’adatu ba abinda zaifaru In sha Allah.Mace mai tawakkali To Ummo bari na ɗakko sandata ke kuma Sa’adatu ɗakkomana fura a cikin ƙwayar koda zamuji yunwa To Hamma,Sa’adatu tashi tashiga ɗaki ta ɗakko ƙwayar wacce take cike da kindirmo da fura,Tana sanye da kayan Fulani farare ƙyakkawa ce ajin farko Asalin fulani gashinta har gadan bayanta ita ba gajera bace sannan ba doguwa bace batada jiki Matashiyar budurwa Yar kimanin shekara 14 mai kama  da yayarta Zahara’u sak!

A dai-dai lokacin  ne Sadiq kefitowa daga ɗakinshi hannushi riƙe da sanda Matashin saurayi mai tasowa mai neman nakansa,jikinshi sanye da kayan fulani blue, ɗan kimanin shekara Ashirin dai-dai Sa’adatu muje ko! a lokacin da yaƙarasu gurin su’To Hamma Ummo saimun dawo suka nufi hanyar ƙofar gida “to” Allah yakiyaye hanya Fita sukayi daga gidan sukaje suka kaɗa Shanayen da dabbobi..! Sai gona!

Comment, share, subscribe and like, please!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Sa’adatu 2 >>

1 thought on “Sa’adatu 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×