Skip to content
Part 2 of 5 in the Series Sa'adatu by Usaina Salisu

Fatima tafito waje domin samowa Ahmed abunda zaici, tsohon nan sai tunani yake inda zaiga fatima hankalin shi yakasa kwaciya ya rasa abinda yakemai daɗi, ku dakatar da motar ya faɗa aƙausase buɗe murfin motar yayi ya fito ya fara suntiji a gurin yana tunani ga bodygaurd sunyimai rumfa ma’ana sun zagayeshi suna jiran umarnin shin juyowa yayi ya kallesu yace, “ƴanzu ina kuke ganin zanga Fatima”

“Sir nasan bazata wuce asibiti ba domin kuwa wannan bawan Allah damuka riƙe yafaɗi kuma nasan tatafi kai shi Asibiti mariya hospital shine kusa danan.” Wani ne daga cikin jami’in tsaron wani mai shegen surutu wai shi Sadiq murmushi tsohon nan yayi wato alhaji yace zancenka haka yake ku shiga mota muje mugani idan har tananan tabbas sainayimaka kyau mai tsoka, dariya yayi yace nagode sir da sauri suka shiga mota suka juya kan motar su ya zuwa asibitin mariya daret nan suka nufi, A daidai lokacin da fatima tafito daga ɗakin a daidai lokacin ‘ƴan gidan su ahmed ke shigowa  asibitin cike da tsantsar tashin hankali suka nufi ɗakin mazan saboda sunsan canne kawai zasu samesa

Sun kwayi sa’a suna isa  suka iske doctor sadiq ƙofar shiga ɗakin emergancy ɗin tambayarshi sukayi Nanne  ɗakin maza sbd goge kokwanto “Eh” ya cemasu tare da basu hanya suka shiga ciki

Alhaji sun shigo da motar su cikin asibitin tunkafin motar ta tsaya ya buɗe murfin ya fito cikin sauri ko sauraran jami’an tsoronshi baiyiba ya shiga ciki da wata uwat babban rigarshi sai buxum buxum yake yana sheƙa uban sauri kaikace yasan idan fatimar take

“Fatima” Tadawo daga amsoma Ahmed chips da jus ta ɗakko su a cikin plate tana tafiya  sadda kanta tayi domin gyara plate ɗin kawai taji tayi karo da mutum duka abinda tasiyo ya zube kuma ta ɓatamai babban rigar shaddar shi da ruwan lemon da taɗauko, Cikin tsananin ɓacin rai ya zanyota ya ɗaga hannu zaikifamata mari kwatsam!! sai yaga fatima cike da mamaki yake kallota yace ke mikeke a nan? kaikace ba ita yazo nemaba ya nuna tamkar zowane yayi kuma ya ganta, cike da jin haushin shi na abinda Ya mata ɗazu ta janye jikinta daga hannushi na riƙon dayatyimata cike da sanɗauka fansa tace bansaniba kai miyakawoka…..?

Dogon tsaki taja tare da juya tana jan Siraran kafafuwanta tana tafiya domin komawa ɗauko wani abinci tunda wancan ya zube.Alhaji ranshi idan yayi dubu tofa yaɓaci ganin yadda taimai tsaki a gaban  mutane gashi taɓatamai riga da ruwan lemon da taɗauko shuru yayi kawai domin idan ya mata magana tofa akwai matsala yadda yaganta afusace zata iyamai abinda yafi wannan

Komawa fatima tayi taƙara amso wani chips da lemo ta wuce ta gaban Alhajin  da ya saki baki yana kallonta mutane kuma dasuke ta kallonsu kowa ya yakama gabansa,  Jami’an tsoronsa kuwa ba abinda sukace kamar arufe masu baki saida kowa ya watse suka nufi gurin a
Alhajin

Tana zuwa daret ɗaki da aka kwantar da ahmed tanufa inda ta iske ƴan gidan su ahmed sunzo ko kallon ida suke batayi ba balle tayimasu magana mamaki suke gananin yadda zarah ta sauya

khadija tace zarah! cike da mamaki tace wato kina ganina zakiyi fuska bazakimin magana ba ko? khadija itama bazata wuce sa’ar fatimar ba juyowa tayi da wasu jajayen idanunta ta kalli khadija cike da halin ko inkula tace niba fatima sunana ba Zarah ba idan bazaki kirani da haka ba to just ki ƙyaleni infatan kin fahimta cike da tsantsan mamaki khadija take kallonta saidai takasa cemata ko uffan sai faman kama haɓar baki  datayi

Lalle ne zarah kin’isa!!! kafin khadija ta rufe bakinta ta, fatima ta juyo afusace  idaninta sun kaɗa sunyi ja tsawa ta dakamata  wacce tarazata har saida taja dabaya tace banace kidaina  cemin zarah ba  matsowa kusa da ita tayi takaleta tace ke bakida kwakwalwa ne baki fahimta ba, mommy daddy kallonta suke da al-ajabi wai yau zarah ce take dakawa khadija tsawa ƙawarta tunsuna yara batta dawa ƙawa aduniya data wuce  bestie   khadija cike da mamaki suke kallonta Babban  abinda yafi ɗauremasu kai shine yadda khadija tayi shuru da fatima tayimata tsawa anya kuwa! duk a xuciyar su suke maganar

Fatima daret gurin ahmed tayi tare da jan guntun tsaki  na kallon dasuke binta dashi ita kuma ta tsani kallo sukuwa mamaki suke, zaunawa tayi kusa da Ahmed  ta ajje abinci tare da buɗemai  take away tace gashinan cokali tasanya A cikin abincin  ta ajjemai  gabansa tace kaci mamaki ne shima dai yarufeshi saboda Zarah bahaka takemaiba plate ɗin ya ɗauka ya fara cin abincin badan ransa yasoba yanaci yana ya mutsa fuska bawani ci yayi ba ya tattara ya ajje gefe   Dankartaji haushi ne yasanyashi ci dabazai ciba Saidai

“ALLAH YAJARABCESHI DA SAN FATIMA”

Y yinda iyayen ahmed,mommy da daddy da kuma khadija suke zaune gefe suna kallon kallon zarah  ganin duk yadda ta canja,kallon su tayi rai a haɗe  ta ɓata fuska tace wannan kallon fa ku wai makusan kallo baya da kyau ba kunsani gaba kamar zaku cinyeni haba dallah ta buga uban tsaki, Dukan su Zaro ido sukayi Ransu ya sosu Ai khadija batasan lokacin da tashaƙi Zarah  ba, cike dajin zafin maganarta tace iyayen nawane keke faɗawa haka To wlh yau saidai muɓata Bazaiyuwa ba ke wacece Banxama dake yar tsintuwa “kwatsam” Fatima ta ɗauke khadija da mari,jikake tassss tasss!” Khadija kuwa intaƙyale sai suka hau Dambe Danda nan akayiwa khadija mugun duka saboda ƙarfi ba ɗaya ba “MUTUM DA ALJAN” Tashin hankali da ba’asamai date

Su Mommy, Daddy, Ahmed, sun kasacewa ko uffan domin jisuke Arufe masu baki kuma anriƙe masu ƙafa  suna kallan abun Ammah sun kasa magana,Khadija taji wahala tafara ihu tana neman taimako  A daidai lokacin dasuke   tsaka da wannan saiga iyayen fatima wato zarah sunshigo cikin asibitin domin duba ahmed khadija takirasu a waya tafaɗamasu halin da akeci da yadda zarah ta chanja mata suna shiga suka  iske wannan dramer Ta faɗan su khadija,Ummi da saurinta tatafi gurin faɗan ta riƙe khadija ta raba faɗan nan take ta hauyiwa fatima faɗa ta inda take shiga batanan take fitaba,su mommy ma sun dawo daidai da duk sun fita daga hayyacin su Likita kowa  ba wanda yashigo cikin ɗakin  abun mamaki!

Daddy ne yace ya isa ƙyaleta zamuyi maganar daga baya,Su ummi Fara gaishe gaishe sukayi a tsakanin su da suka gama  sai ummah mariƙitayar zarah tatafi gurinta ganin zarah kamar bata gansuba,KO faɗan da suka matane  yasa taƙyake su matsawa gurinta tayi  tare dafa kafaɗa tace zarah baki gammubane bakiyimana magana ba ko faɗan danayi makine, infatan kina lpy hannuta tasanya ta janye hannuta ummi tace kidaina dafani kuma ni sunana fatima bawai zarah mamaki yaƙara kama ummi ashe yadda khadija tafaɗa hakane anya zarah kina lpy kuwa wai mike damunki ne?nima abinda nace kenan mike damunta cewar khadija wlh nihar tsoro take bani inji Ahmed kamar ba zarah taba.

“Ya isa” Tafaɗa cike da garsasi tace ya isa ranta a ɓace ta juya toyo hanyar waje domin fita daga ɗakin asibitin tana mai chanjan tsoki kallonta sukayi gaba ɗaya  Zarah ina zakije cewar ummi Ko kallon ummi batayi ba tasanya ƙafa tafita, bacin tafitane kowa ya sauke ajiyar zuciya ya yinda ummi tafara magana wlh ni sainake jin ajikina wannan kamar ba zarah ta bace duk dacewar bani na haifetaba nasan yadda zarah take macece mai haƙuri sannan bata da zafin rai sannan zarah idanunta baƙaƙene itakuma wannan nata bleu block ne sannan zarah tanaso acemata zarah miyasa zata chanja nikname ɗinda tafiso, inajin kamar ba itaba shima abbah haka yace gaskiya kamar ba itaba,yayin ahmed shima yakeji ba itabace ammah yakasa faɗa saboda soyayyar ta dake maƙale a cikin zuciyarsa.

Khadija da da mommy ma suma sunyar da, ba itabace to wacece wannan? mai kama da zarah Sai anyi bincike za’agane, sannan “ina asalin zarah take” ya yinda daddy yace kudaina cewa ba ita bace kuna ganin komi na yarinya dan ta ɗan chanja hali kuma saiku ce ba ita bace kawaidai ta sauyane kuyimata addu’ar allah yashirya takawai bawai maganganu mararsa amfaniba.

Sannan yajuya kan ahmed yace ahmed yakakejin jikin naka fatan kaji sauƙi? sannan inaso kafaɗamin minene abun yafaru dakai nasandai lafiyarka lau yace “eh” daddy dama saiyafara kame kame da sosa ƙeya haɗi da faɗin cikina ne yake ciwo dady shiyasa kallon rashin yadda yayimasa haɗi dacewa to allah yabada  lpy sannu kaji! yace yawwa daddy domin yasan yana da ciwon ki yana tashi kuma akowani lokaci shiyasa yake jeramai sannu  likitane ya shigo yaduba jikin nasa “Alhmdullh” da sauƙi dan haka ya rubutamasa sallama da magunguna sannan suka tattara kayensu suka nufo gida a motoci  su motar su daddy daban motar su ummi daban dukansu gidan daddy suka wuce domin dama kusa da kusane.

Fatima tana fita daga ɗakin daret bayan ɗaki tayi inda ba mutane ɓacewa tayi sai gata  a wani ɗaki wanda yakasance baƙikƙirin ba haske ba fitila, Kunna  ƙwan ɗakin tayi   tare da haske wata budurwa wacce naga kamarta sak da Sa’adatu  gurinta tanufa ta tare da jan kujera ta zauna tare da girgije jikinta tadawo suffar ta ta Aljan mummuna ce bata da ƙyan gani kokaɗan kuma ba yarinya bace ta tsufa da’alama zatakai shekara 30, “kwatsam! saiga wannan tsohon ya bayyana  shida ta wagar sheɗanin dasuka rakashi gurin su su Ahmed ɗazu, ya shigo da shiga ta ‘yayan sarakan Aljannu, abinda yaƙara bani mamaki kenan shima ba mutum bane  yariƙiɗa yakoma tsoho yakuma Suffar santa Aljannu shima ba yaro bane Aƙallah zaikai shekara 35 Asalin sunan sa Safwan Shima dai bashida kyau gwarama Ajanna fatima wacce asalin sunanta Zainab.

Hannuta tasanya A jikin Zarah  tare da zare mata ɗankwalin da tarufe mata baki tace zarahara’u yakike  zarah kuka tafashe dashi tana cewa dan allah kurabu dani kuƙaleni please minayimaku kumaidani inda kuka ɗauko Sai ta sake fashewa da kuka tana tuna lokacin data rabu da iyayenta gashi yanzuma ta rabu da masoyinta da ummi ta Nantake tatuna da Sa’adatu da sadiq,sai shashakar kuka take.

Dallah kiyimana shuru cewar Zainab  Safwan ne yace Zainab kidaina mata hakama Zaunawa yayi kusa da Zarah tare da sanya hannushi yarungumo Zarah jikinshi yana mai lallashinta Zahara’u taƙara Rikicewa saboda ganinta rungume a jikin Aljan ƙokarin kwatar kanta take saidai baibata damar hakaba saboda yamata riƙon bana wasaba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sa’adatu 1Sa’adatu 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×