Unguwar GRA manyan manyan gidaje je a unguwar masu matuƙar kyau da tsari wasu dogayen ginagine ne masu matuƙar ɗaukar hankali gwanin birgewa, motar Ahmed tana shigowa layin daret gurin wani ƙofar gida ta nufa wanda duk unguwar ba kamar sa, ginin doran zabuwa ne jikin ginin blue ne ammah get ɗin block ne hon sukayi getman yazo ya wangale masu get ɗin shiga sukayi da motocin su har dasu Abbah suma gidan su Ahmed ɗin suka shiga duk cewar suma gidan su a unguwar yake, gurin parking space suka nufa suka tsaida motocin su kana suka fito. . .