Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Sa'adatu by Usaina Salisu

Unguwar GRA manyan manyan gidaje je a unguwar masu matuƙar kyau da tsari wasu dogayen ginagine ne masu matuƙar ɗaukar hankali gwanin birgewa,  motar Ahmed tana shigowa layin daret gurin wani ƙofar gida ta nufa wanda duk unguwar ba kamar sa, ginin doran zabuwa ne jikin ginin blue ne ammah get ɗin block ne hon sukayi getman yazo ya wangale masu get ɗin shiga sukayi da motocin su har dasu Abbah suma gidan su Ahmed ɗin suka shiga duk cewar suma gidan su a unguwar yake, gurin parking space suka nufa suka tsaida motocin su kana suka fito daga motar domin shiga cikin gidan.Ma’aikata sai aikinsu suke kama daga masu ba flower ruwa sai masu gyara katafaran cikin  Babban gida wanda yasha kayan alatu daban daban masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali hatta flower sai ƙamshi suke idan kazo giftawa ta wajen Su Ahmed Suna sauka daga motocin suka nufi palour gidan.

Ahmed tafiya yake cike da ƙasaita  da izzar mutum ne shi da bayasan hayaniya baya da surutu Sannan yana da zafin rai saidai yana san ‘ƴan,uwa sa” Ƙyakkawa ne ajin farko matashin saurayi wanda zaiwuce shekara ashirin da bakwaba asalin mahaifiyar sa Shuwa Arab ce  shiyasa suke da kyau musamman shi,saidai kuma ƙanansa da ƙanwasa  mai suna Aryan da iman sufishi kyau.

Shigar su palour keda wuya naga abun mamaki  “Wow”  abunda na iya furtawa kenan tsaruwa abinda na iyacewa kenan gani irin wannan palour wanda kamar ba a ƙasar ba ya haɗu iya haɗuwa wannan shi akecewa aljannar duniya.

Aeesha da Ashraf da iman da kuma Aryan da masu aikin palour sune kawai a cikin palour Ashraf yana samar kujera  maicin mutum ɗaya daga gefe  yana danna Lapton ya yinda Aeesha take kusa dashi tana riƙe da waya smart 6 A hannuta tanayin  chat. Aryan kuwa da iman sai gojegoje suke a palour Aryan wai sai ya kamata iman ita kuma tana cewa bazai kamata ba suna ta faman ƙyalƙya dariya  suna nishaɗi. Har fillow suke yardawa a ƙasa.

Ahmed yana sanya ƙafar sa cikin palour dukkan su ma’ana iman da aryan banda sauran tsayawa sukayi suna kallonshi, shima ya zuba masu ƙyawawan idonsa masu alamar barci sai lumshe su ya keyi duk a cikin su ba wanda ya fara ganinsa sai iman da aryan.

Yaya ta faɗa da ƙarfi tatafi da gudu gurin sa sai kowa hankalin shi ya dawo jikin shi, dajin an ambaci yaya kowa yasan waye  daga masu aikin har Ashraf kowa tashi tsaye yayi yana gyara nutsuwar sa kowa yashiga taitayin su kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya sun zumasa idanu, ammah ba wanda ya iya cewa uffan.

Ware hannayen sa yayi yace bazaku zo ku rungume ni ba nadawo sai ku zubamin ido kamar yau kukafara ganina jikin su ne yayi sanyi dajin wannan magana tashi da sauri kuwa suka isa idan yake suka rungumeshi suna  tambayar shi yajikin fatan yayi sauƙi “Alhamsulillah” Da sauƙi in  sha Allah kama hannu iman yayi suka je kan kujera suka zauna suma sauran ƙannan nasa zama sukayi yayinda ‘yan aiki suka fara maida fillow da su Aryan suka yarda ƙasa suna gaishe da mai gidan nasu wato Ahmed Boss  sunan dayafi so duk a gidan a haka ake kiransa.

Su mommy ne suka shigo gidan suna magana daddy ne yace “mu zauna sai mu ƙarasa tattaunawa ko?”

Tare da khadija suka shigo ammah itace a gaba ɗakinta ta wuce daret domin watsa ruwa, su Ummi sun sami guri  sun zazzauna ya yinda yaran suke tayi masu sannu da zuwa, ummi ta kalli Aeesha tace Zarah batazo nan ba “Eh” ummi har ƙawayen ta na makaranta suka zo nemanta ta bada amsah daret! batanan kuma Kowa kallon Aeesha yake tana magana musamman Ahmed to ina tatafi a cewar su Daddy ni wlh abubuwan da zarah takeyi ‘yanzu tsoro suke bani cewar mommy niko nace mizaihana ayimata karatu ko Iska ya shafeta bamu saniba acewar Ahmed yace saboda abinda takeyi sai masu sune kawai zasu ringa irin abinda take nidai a ganina ammah yaya kuke ce ?Abba ne yace nimadai haka naga yafi dacewa muyimata  magani saboda abin nata gaba yake ƙarayi anemi mutum a rasa saikace wani aljani,Eh Ayimata hakanɗin.

Akan wannan shawar suka tsaya cewa zasu kirayo babban malami yayimata addu’a aji minene ke damunta.

Ahmed kakira zarah muji ko tana ina? cewar ummi tɓ”To” ummi ahmed hannu yasanya ya ciro waya daga aljihon wandan sa ya kirawo wayar  Zarah  tana hannu Safwan a lokacin suna zaune a gurin wata bishiya suna fira miƙamata wayar yayi yace masoyinki yakira nataho maki da wayar ne dakika bari a mota ɗatsu amsa tayi tana ganin Ahmed bata tsaya wani jinkiriba taɗau wayar.

“Assalamu Alaikum” daga can Ahmed ya amsah  “Walaikum salam”ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba yace  kina ina zarah? Nazo gida bakinan…naje wani gurine!” inane inda kikaje? nacemaka wani guri” ko dole saina faɗamaka.

“Zarah ya faɗa da ƙarfi kasancewar bata shakkar sa yasa tace na’am Ni kike faɗawa haka to nabaki miti biyar duk inda kike kimazamaza kidawo gida karkiyar da nanemoki dakai na kinji nafaɗa maki yana mai datse wayar daga kiran.

Fatima tsaki tayi duk da tanasan Ahmed Ammah bata ɗaukar raini, ita bataso a numamata iko ko gadara.

Safwan muje naga wannan yarinyar kafin natafi to muje yace tashi yayi suka nufo ɗakin dasuka ajje zarah suna zuwa suka kunna fitilar ɗakin ga mamakin  su babu ita babu labarin ta waigw waige suka fara ammah ko alamarta basu gamiba sunnemeta sun rasa tashin hankali daba’asamai date!dubata suka fara baji bagani Ammah ko ƙeyarta basu ganiba To tayaya tafita daganan jikin ta  ɗaure yake da kaca kuma ɗakin a rufe yake tayaya ta buɗe To tabbas wani yazo ya taimaketa kuma ba MUTUM ba  saidai ALJAN  domin mutum bazai iya shigowa nan yafita lafiya lau ba tofa hankalisu ya tashi nemanta suke hakku da gaskiya ammah basu ganta ba su tsoron su kar wani yazo daga fada yaganta ya kaita masarauta dasun shiga ukku Allah Allah suke batacan tajeba Sunje masarauta batanan “Alhamdulillh” sukace sukaciga da nemanta.

Bayan fitar su ne wata ƙawar fatima tazo nemanta nan mai suna Ruky itama aljanace abinda yasa kuma tazo nan neman fatima saboda mafiyan lokuta idan suna zaune saitace tatafi nan tahuta shiyasa  tazonan nemanta, “kwatsam! tayi arba da zarah kwace tana karkarwa sai neman taimako take  da mamaki ruky taƙarasa gurin ta tare da tambayar ta ko lafiya? taya tazo nan Zarah kuwa bataɓoyemata komi ba tafaɗamata yadda akayi tazo nan

Ita kuma Ruky mutum ce mai imani da Allah sannan tana da tausayi kuma ita ba shaiɗaniya ce ba kamar fatima, Zarah ta faɗamata duk abinda yafaru sannan ita kuma tataimake ta tafitar da ita daga wannan gurin duk da ba gida takaitaba Ammah tataimake ta Abinda yasa bata kaita gida ba saboda jiranta ake shiyasa ta fiddata daga duniyar su takawota wani gari daban, Safwan yace fatima yanzu dai kije gidan su Ahmed kinga karsuyi ta jiranki nizan nemo Zarah duk inda tashiga a faɗin duniya to shikenan  abinda ta iya cewa kenan ta ɓace sai gashi ta sauka tsakiyar gidan su Ahmed  tafiya tafara  da wani irin salo kamar majiciya sai wani abu take kaida kaganta kasan ba mutum bace  sai lauyewa take.

Tana shiga cikin palour sallama kawai tayi  itama bakowa yaji taba tasami guri ta zauna tofa a daidai lokacine kuma wannan babban malamin da Ahmed ya kirawo yazo Yana shigowa gidan ya kirawo wayar Ahmed ɗin ɗaga waya yayi yace ƙaraso malam Muna ciki

Zarah ce ta kalleshi karaso malam kuma? ta tambaya tana kallon su   ba wanda ya bata amsah   kowa ya shereta   kamar yadda tayi datazo ba wanda ta gaishe sa ko tayi ma magana, duk da cewar a fili tayi tambayar basu bata amsah ba kuma yaran sun tashi sun bar gurin bisa umarnin Ahmed da su mommy suka shigo

Suna zaune wani mai aikin gidan ya shigo da malam ɗin tunda fatima ta ɗogo ido ta kalli malamin antar jikinta takaɗa ido ta zaro waje cike da tashin hankali domin tasan wannan malamin dazafin addu’a kallonshi take ya yinda shima ya sanya idonshi cikin nata yana mata murmushin wanda nakasa fasaara wani irine yake mata na mugunta ne ko najin daɗin sake haɗasu da Allah yayi a karo na biyu  dama tataɓayiwa wata haka kuma yayi maganin ta shine ta dawo wajen zarah  cikin sauri tatashi zatabar gurin cikin zafib nama ahmed yariƙo hannu ta yaƙi bata damar fecewa yayinda malamin yakaranta wata aya wacce ta tsayar da ita A inda take

Malam ga guri zauna cewar su Daddy guri ya samu ya zauna ya kalli su daddy da Abbah suka gaisa sukayi masabaha a tsakanin su kamar yadda allah yace ayi sannan Abbah yace dama muna so kaduba mana ɗiyar mu Zarah wacce ta canja kwanakin da suka wuce munkasa gane kanta shine muke ganin ko iska ya shafe ta cewar daddy

Malami kallon su yayi sai yayi murmushi yace kunga wannan ya nunata da tsaya kallon ta sukayi datayi tsaye ƙekam ko motsi takasa yi sai faman raba idanu datakeyi yace to bawani iska da yashafeta, “Ita dakanta” itace ALJANAR cike da furgici kowa yasake kai dubansa gareta Ahmed ya tashi tsaye cike da tashin hankali yace ya malam Zarahara’u ɗin  itace Aljana kasake buncikawa dai kodai bakaga daidai ba “Ahmed nasan minakayi bazance Aljana bace bacin mutum ce”

Sukuwa su ummi ko uffan basuce ba face mamaki gani suke kamar almara Itakuwa mommy da take da shegen tsoron aljannu tuni ta lafe jikin Daddy tana karkawa,fatima kuwa gabaɗaya ta furgice jitake kamar akan ƙaya take daza’ace ance kul to ba shakka  zabgawa zatayi da guntun gaske.

*****

Malamin yace bari kagani saika tabbatar karatu yafara na alƙur’ani mai girma” ihu fatima take bil haƙƙi tana cewa wayyo ka kyaleni domin jitake tamkar ana toyamata jikinta Ahmed kuwa yayi mutuwar tsaye ganin yadda fatima take kuka tana ihu Addu’a yafara karantawa a sirrance “La’ilaha’illah anta subahanaka inni kumtum minallal zalimin”! fatima taya zakimin haka?

Kallon Ahmed fatima tayi cike da yaudara da salo tace Ahmed nicefa zarah  kace ya daina ƙonani zanyimaka bayani dan Allah gabayaɗaya tacika gidan da Ihu ya yinda malam yadage yake ta watsamata ruwan addu’a.

Kabarta haka cewar Ahmed tayimana bayani,bakasan halin tabane shu’uma ce ta iya yaudara bazatayi bayani ba a haka dole saitaji jiki,ya cigaba da watsamata ruwan sai kuka ta ƙara fashewa dashi tace Ahmed kataimakamin wlh zayi maka bayani Ahmed yanafa cutar dani Zarah kace fa,Datagadai ahmed ya ƙyaleta baya cewa komi saitayi tunanin ɓollomai tawata hanya dakatawa tayi da ihun datake ta kalli Ahmed tace to kasani muddin suka cutar dani kasara Zarah kallonta kowa yayi.

*****

Sa’adatu sai tafiya ake da ita a cikin amalan ke gashi sai zabga ruwan sama ake, sunzo bakin titi suna tafiya sukazo kan kabarin mai ta tsine wanda keyin wani tudu a kan titi saboda motoci masu yin gudu kwatsam! wannan amalan ke tasake faɗuwa sakamakon hannuta a ƙarye yake lallaɓata sukeyi nan take dabbobin suka zube gefen titi cikin sauri sauri suke kwasu su suna zubawa a amalanken yayinda suka ruwa sai jiƙamasu jiki yake wani daga cikin su yace kawai kubar sauran  mutafi kawai to anan dai suka bar sa’adatu a yashe a gefen titi ita dawasu dabbobin daga cikin ɓarayin kuma sukaci gaba da tafiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sa’adatu 3Sa’adatu 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×