Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Sa'adatu by Usaina Salisu

Sa’adatu a kwance takea inda ɓarayin nan suka yarda ta   ruwa sai bugunta yake a furgice ta tashi kamar wacce ka tattaɓa tashi tayi daƙar domin  duka gaɓoɓinta  ciwo suke mata tashi tayi tsaye da ƙyar  a hankali take tafiya gurin  titi  ta nufo domin kozata idan sani ko mafaka domin samun hanya tafiya gida  kallon hagu da dama tayi taga ba kowa a gurin tashin hankali daba’asamai rana sadiq tafara kwalawa kira tana tunanin tayaya tazonan? domin ba inda take bane idan bazata manta ba suna ghoan da sadiq.Tafiya ta cigaba dayi kan titi da roƙon Allah yakawo mata mafita, kan titin ta tahau ba zato zba tsammani wata mota ta feso da gudun gaske  sai hon takeyiwa sa’adatu ya yinda ita kuma ta tsunduma kogin tunanin inda zata sami mafaka.

Abinda Allah ya rubuta to ba shakkah saiya faru, haka kuwa yafaru da ita kwatsam! motar nan tayi ciki da ita batare datayi tsammani ba,wani gigitaccen ƙara tasaki Ta faɗi ƙasa sumammiya, wani uban birki wanda take jan motar tayi cike da ruɗewa tsayar da motar tayi tare da ɓalle murfin motar tafito cikin sauri ita da mijinta ma’ana dai macece kejan motar.

Gurin sa’adatu suka ƙaraso ganinta kwance kamar gawa yasa hankalin matar tashi Faɗawa jikin mijin nata tayi tafashe mai matsanan cin kuka duk da cewar ba musulma bace ammah tana da tausayi kuka  takeyi shi kuwa mijin ta mai suna cristoper ƙara rungume abar kaunasar yayi yana tambayar ta what happy? sorrry stop crying  “am so sorry dear” kama hannuta yayi yajata zuwa mota ya zaunar da ita kasancewar ruwan da akeyi bayaso ruwa ya taɓamai matarshi, gurin sa’adatu ya dawo yasa hannushi yaduba domin ganin idan ta mutum saisu barta nan  idan bata mutum ba kuma saisu kaita asibiti.

Duba sa’adatu  yayi sosai duk da a ana ruwa hakan baisa ya koma ba saida ya tabbatar da sa’adatu tana da rai saboda hannu yasa saitin zuciyar ta ya duba ganin tana bugawa ya sashi ɗaukata cikin sauri ya sanya ta a mota shima shiga yayi mazaunin driver kana yaja motar da gudun gaske yana barin gurin jeniper kuwa sai juyawa take bayan seat ɗin baya tana kallon sa’adatu domin ita bataso ace ta mutu, gudu yake ta shararawa cikin ‘ƴan Awowi dabazata wuce ukku ba suka iso garin abuja.

Wata unguwa ce yanufa duk da cewar ba GRA bace ammah unguwa ce tamasu hannu da shuni gidansa zai wuce da sa’adatu kasancewar shima likita ne Ammah dayaga hankalin matar sa ya tashi bazai dubata ba cikin kwanciyar hankali saboda zairaba hankalishi biyu ne.

Tuna wannan abu da yayi ya tilas tashi fasa shiga kwanar gidan shi ya juyawa kan motar shi izuwa asibitin “musa haro”  yana shiga da motar shi dama akwai likitoci a waje wanda suke amsar taimakon gaggawa musamman mashi dayakasan ce a gurin yake aiki  dandanan sai ga likitoci da sauri domin ya yi waya da suna hanya cewar yana tare da marar lafiya suzo su tare shi a ƙofar ɗakin shiga emargency, aikuwa haka sukayi ba ɓata lokaci sukazo da gadon mararsa lafiya suka zauna suna jiran  isowar motar sa cikin ikon Allah saigashi ya iso an kaɗauki sa’adatu akashiga da ita akafara bata taimakon gaggawa  “Alhamdulillah” Sunsamu sundawo da ita hanyacinta.

Farkawar ta ke da wuya tafara kiran sunan sadiq da ummo ƙokarin tashi take saidai ciwon jikin datake ji bazai bata damar tashi ba A dole ta koma ta kwanta badan ranta ayasoba, Allaura akazo mata inda tana ganin allura tarikice kasan mutum ƙauye da ƙin allura, tace itako sambata yarda da wannan zancen ba na allura idan suka fara kokuwa da doctor hafsat,hafsat kira take ki tsaya ayimaki allura samin lafiyar kice fa,   bawani abuba ammah sa’adatu fir taƙiya ayimata, idan garin kokuwa hafsat ta riƙeta da ƙarfin gaske wanda yasata yinwata Albaya tana faɗowa daga kan gadon nantake kuwa kanta ya bugu da gadon dayake kusa da wanda aka kwantar da ita nan fa ta sume.

Cristoper ne da matar sa janepar suka shigo domin duba jikin sa’adatu,So su ke su ganta kafin su tafi suna shigowa suka ganta  a yashe  a ƙasa gurin suka ƙarasa da sauri suna tambayar doctor ɗin tafiya suka ganta a ƙas haka, amsah tabashi da cewa faɗowa tayi ammah bata gayamai ainahim abunda yafaru ba kasancewar sa mutum mai zafin zuwaciya abu kaɗan yake ɓatamai rai,

Taimaka mata yayi suka kama sa’adatu akamaida ita kan gadon sannan ya umarci likinta da ta zauna da sa’adatu har safe shi yanzu zasu tafi gida ne dama daga katsina suke wajen wani taro da’aka gaiyacesa shine fa yatafi da matar sa jenipar, Amsah masa tayi da “to” cikin  girmamawa,   gurin sa’adau tatafi kujera ta janyo ta zauna  tare da gyarawa sa’adatu kwanciyar ta,jinepar fitowa sukayi daga ɗakin suka nufi motar su domin su koma gida danufi gobe da safe su dawo suga jikinta, su tambayeta inane gidan su sannan su maidata hannu iyayenta haka suka tafi gida da yaƙinin zata warke kafin safe.

Gidan Su Sa’adatu

Gidan su sa’adatu hankalin su gabaɗaya ya gama tashi domin jin sa’adatu ba’asam inda takeba gashi kuma ba’asan inda za’asameta! Baffa faɗa ya fara ta inda ya shiga batanan yake fita ba domin shi a ganinsa duk sakacin ummo ne taya zatace a fita da sa’adatu gona kiwon dabbobi bacin tasan ga abunda yafaru da yar’uwa ta Zahara’u miyasa zatayi haka sa’adatu yarinya ce.

Haƙuri ta dunga bashi da cewar itafa ko kaɗan batayi tunanin cewa sa’adatu zataɓace ba dahakan ya daina damuwa in sha Allah ba abinda zaisameta ƙilan tana wani guri a nan kusa da gonar taga ƙila anfara ruwane shiyasa ƙila ta laɓe a wani gurin.

Baffa gizgiza kai kawai yayi ya shiga ɗaki domin ajje abinda ya shigo dashi lema ya ɗokko daganan yace sufita suje su nemo sa’adatu dan Allah ya gani bazai iya bari ba har aƙara wasu mitinas bazai iyaduba sa’adatu ba duk da kuwa ƙasan zuciyar sa na cewa tabbas ɓacewa tayi kuma ba lalle a gantaba.

Itama kamar dai yayarta za’arasata siraran hawaye ya goge da suka zubo bisa bai saniba duk saboda tunanin dayake akan sa’adatu  gurin su ummo ya ƙaraso yace mutafi,ummo tace bari inzo muje  tare musamota sadiq muje ko kallon baffa yayi da idanuwanshi da suka kaɗa sukayi jawar saboda damuwa yana jin matuƙar ba daɗi yanaji a ranshi itama Sa’adatu sun rasata muje Baffa ummo nima zanbiku” Baffane ya kalleta yace idan kinbimu sa’adatun tadawo saitaje ina? shuru tayi mutafi ya cewa baffa yana miƙamasa lema a hannusa fita sukayi daga gidan duk da cewar ana ruwa bakowa kuma a gidan.

Ahmed tasowa yayi dagakan kujera dayake a zaune  fita yayi daga palour yaje yaɗauko wata zabgegiyar bulala  dorina alwallah yaje toilat yaɗauro wani ɗan table yaɗauko yazo kusa da fatimar ya zauna matso da kujerar yayi ya gyara zamansa sosai sannan ya kalli malamin yace ƙyaleta kallonta yayi ranshi nayimasa ƙuna yace “kince idan har nabari wani abu yasameki kamar yasami zarah ko” to bari muga ninayimaki lahani dakaina inyaso saiki kasheta bulalar yaɗa yafara zubamat yana tofamata addu’o’i dama ahmed ba dai iya addu’o iba zabgamata bulalar yake yana tofamata addu’ar ihu take tana kuka yace zakifaɗamin inda Zarah take kuwa, fatima taji wahala kira take zanfaɗa zanfaɗa! Dan Allah ka kyaleni pls.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sa’adatu 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×