Aunty ta fito daga matattakalar bene inda dakin barcin ta yake zuwa daki na rike da 'yan mukullan motar ta "Siyama na fita, zani Wuse Market kayan cefanen mu sun kare, da dai-dai kike da na nemi rakiyar ki, to duk kin bi kin susuta kan ki akan da namiji, kin susuta min Abban ki babu gaira babu sabar na kasa gane kan sa. Ga nan Nadia ki kula da ita kafin na dawo."
Ta fada tana miko min ‘yar autar mu Nadia, babu kiwa ba komai yarinyar ta taho zuwa gare ni tana bangale baki, ta bani jakar. . .